GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ya ƙarishe mgnar da juyawa ya nufi falo.

Ita kuwa Aysha wani irin bacci ne yayi awon gaba da ita,
tana mai jin zafin hannun ya ɗan lafa sai kuma raɗaɗin marin.

A can falon kuwa, wayar Aysha ne dake hannun Hibba yayi ringi.
Bappa am.
Shine sunan da ta gani a rubuce.
Da sauri ta nunawa Ummi shi tare da cewa.
“Ummi ana kiranta”.
A hankali tace ki ɗaga.
Kai ta gyaɗa tare da amsa kiran ta kara wayar a kunnenta.

Cikin nitsuwa tace.
“Wa alaikassalam”. Sai kuma tace.
“A a Bappa ba Aysha bace.
Hibba ce, Aunty Ayshan tana ɗakin Hamma Jabeer”.
Cikin dattaku Bappa yace.
“To Hibba ya jikin nata?”.
A hankali tace.
“Bappa hannunta kam yana ciwo sosai, ya kumbura yayi ja, in an taɓashi zafi kamar wuta, bata iya bacci”.
Da sauri tayi shiru ganin Ummi na girgiza mata kai alamu.
Ta daina faɗa mishi hankalinsa zai tashi.
Ila kuwa hakane, cikin tashin hankali da kiɗima yace.
“Yanzu kai mata wayar maza, kai mata inji muryarta”.
A hankali ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi wai in Kai mata wayar”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Jekiyi sallama ki kai wayar”.

To tace kana ta juya ta nufi falonshi.
Tana jin Bappa na cewa.
Yi sauri”.
A falo ta samu Hamma Jabeer ɗin cikin sanyi tace.
“Hamma Jabeer gashi Bappa am, na son yin mgna da Aunty Aysha”.
Hannunshi ya miƙa ya amshi wayar ba tare da yace komaiba.
Ganin kiran bai yanke bane.
Yasa ya zubawa number ido cike da mamaki ganin code number ɗin bana ƙasar Nigeria bane, na ƙasar Cameroon ne.
a hankali ya kai wayar kunnenshi tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.

“Wa alaikassalam Jabeer ne?”.
A hankali cikin nitsuwa yace.
“Eh Bappa nine, ina kwana ya gida”.
Cikin jin sanyi yace.
“Lafiya lau Alhamdulillah. Ya jikin Shatu?”.
A hankali yace.
“Alhamdulillah Bappa jiki da sauƙi sosai ma yanzu hakama tana bacci ne”.

Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah to Allah ya ƙara lfy, amman me yake faruwa da hannun ne?”.

Cikin sanyi ya miƙe ya nufi bedroom.
A gaban gadon ya tsaya tare da cewa.
“Hannun ya ɗan kumbura amman ba sosai ba, sai kuma yayi ja, sannan jikin hannun yayi zafi sosai”.
Cikin tausayawa ɗiyar tasa yace.
“Amman kada ayi mata allura, sannan a nunawa masu maganin gargajiya hannun, ko dajine”.
A hankali yace.
“Bappa ba daji bane an gwadata babu wani ciwo a jikinta.
Kuma inma dajin ne yanzu akwai alluran shi.
Matsalar hannun yana ɗan lafawa ya kuma tashi ne.
In ya tashi kuma ihu take son yi.
Kuma sai tayi ta kuka.
To kukan ne ke sa mata zazzaɓi da ciwon kai”.
Cikin sanyi yace.
“Allah sarki Shatu, haka take in bata da lfy.
Zan zo jibi in sha Allah.”
Cikin hikimar nuna mishi ya fahimci inda yake tace.
“To Bappa Allah ya kawoka lfy, daga gobe zaka taso ko?”.
Cikin nitsuwa yace.
“In sha Allah”.
Kontar mishi hankali yayi kana suka katse kiran.

Ba’ana kuwa duk abinda ke faruwa da Aysha yana gani a ƙwaryar tsafinshi.
Amman muddin Sheykh yana wurin sai yaga wani haske ya rufe ƙwaryar gaba ɗaya sai ya kasa ganin komai a kanta.

Yanzuma zaune yake yasa yaranshi a gaba.
Da kuma sabon uban gida daya samu.

Cikin fargaba da tausayawa Mata abinda ke damunta ya kalli ɗaya daga cikin yaransa wanda ɗan ƙabilar ɓachama ne, cikin waɗanda suka koro shanayen Bappa ne da Alhaji Haro.
Cikin Ɓacamancin yace.
“Barun zaka tafi ƙasar Nigeria ka wuce jihar Ɓadamaya kai tsaye har cikin masarautar Joɗa”.
Cikin tsoro Barun yace.
“Masarautar Joɗa kuma, ta yaya to?.”
Numfashi ya fesar tare da cewa.
“Duk magungunan da Sarkin bakan masarautar Joɗa yake saka mata da wanda zai sa mata nan gaba, duk na ruruta ciwon ne, sabida shi magautan Jabeer yakewa aiki, to kasan cewar bawai sihiri bane shiyasa Mata bazata ganeba, kawai maganin ingiza ciwon yake shafa mata.
Sannan makarin ciwon Ni kaɗai nake dashi.
To zan kira Bappa da layinka.
In mishi jawabin ciwon da mgnin sannan zance mishi kai yau zaka kama hanya,
dan taimaka mata, amman fa sai in zasu biya kuɗin jinyar da shanu hamsin”.
Cikin mamaki Barun yace.
“Shanu hamsin mutumin da muka kwashewa komai ko ɗan tinkiya bamu bar mishiba, ina zai bada shanu hamsin”.
Murmushi Ba’ana yayi tare da cewa.
“Uhumm baka san waye Malam Liman ba kenan Bappa baka san da waye yake tareba, baka san komai game da shiba. Kai dai bani inkirashi yanzu kaji.”

Da sauri ya miƙa masa wayar.
Shi kuma ya dannawa Bappa kira.

Yana katse kiranshi da Sheykh yaji wani kiran ya shiga wayarshi.
Amsa kiran yayi tare da kara wayar a kunne.
Sauya murya ba’ana yayi tare da cewa.
“Ina mgn da Malam Liman ko baban Aysha mai ciwon hannu”.
Da mamaki Bappa yace.
“Waye ne?”.
Ciki kaurara muryarshi yace.
“Sarkin bakan nufe ne, bincike nane ya nuna min ciwon hannun yarka tana can masarautar Joɗa.
An kawo wani sarkin baka yana mata mgni sai dai mugune magautansu yakewa aiki.
In har zaku biyani ni Shanu hamsin zan je kuma zan mata aiki a take zataji sauƙin”.
Cikin sanyi Bappa yace.
“To yanzu kai ina kake”.
A nitse yace.
“Ni yanzu haka ina bakin iyakar ƙasar Nufe da Nigeria ne.
Yau zuwa gobe zan shiga ƙasar”.
A hankali cikin sanyi Bappa yace.
“To ba matsala, nima jibi zan shigo.
Mu haɗu a can in dai kayi mata mgnin ta warke a take zan biyaka da abunda kace”.
Cikin jin daɗi yace.
“To sai mun haɗu.”

Katse wayar yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah Shatuna zata samu lfy. Zan kuma samu shanu hamsin. Sannan zanji lbrinta, zaka kuma isarmin da manufata.
Kunga na jefi tsuntsu biyar da dutse ɗaya.”

Jinjina mishi sukayi kana ya shiryawa Burun komai nagnin ya nuna mishi yadda zaiyi da yadda zai isar mishi da saƙonshi wurin Aysha.

Bappa kuwa Murmushi yayi dan ya gane Muryar Ba’ana.
Dama ya sani bazai rabu dasu haka a sauƙaƙeba yasani yanzu duk motsin Aysha yana tafin hannunshi.
Abinda yasa ya yarda su haɗu kuma yasan ba shi da kanshi zai jeba.
Sai dai ya wakilta wani.
Ya kuma sani tabbas yanada makarin ciwon taɓen sihiri wato ƙetare.
Yakuma san bazai cutar da Aysha ba yasan tabbas taimaka mata zaiyi dan baya son abinda zai cutar da ita.

A haka shima ya kira Arɗo Bani suka tattauna kana ya fara shirin tahowa.
Ko Ummey bai gaya mata abinda ke faruwa ba.

A can jihar Tsinako kuwa sha ɗaya dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi ya nufi jihar Ɓadamaya.

A cikin Rugar Bani kuwa. Tun shekaran jiya su Junaidu suka dawo gida.
Alhamdulillah duk sun worke kuma har gida aka dawo dasu.

Sosai Arɗo Bani da sauran dattawan sukayi mamakin jin Sheykh ne ya kaisu sibitinshi ya kuma kula dasu har suka samu lfy.
Kana yayi musu komai ya dawo dasu lfy.
Alhamdulillah kuma yanzu Rugar Bani basu da matsalar komai.
dan ya rigada Allah yasa tsoron fulanin a zuƙatan Ɓacamawan.
Yanzu kowa harkar shi yake ba kare bin damo.

Suyi kiwonsu lfyta shanayensu nata habaƙa.
Yanzu kuma sun maida hankali kan shuke-shuke amfanin gonakin su.
Sabida shigowar damuna.

A cikin masarautar Joɗa kuwa.
Sheykh yana gama mgna da Bappa ya shiga bathroom.

Cike da mamaki ya ɗan sunkuyo ya kalli boxes dake jikinsa,
wanda dashi zaiyi wonka.
hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi da tun jiya da safe data harba ta miƙe ta tsaya ta rinƙa kumbura da cika da miƙewa tayi tsawo.
Har yau har yanzu harbawa takeyi babu ƙaƙƙautawa yadda zuciyarshi ke harbawa haka itama.
Kuma tana tsaye gam tamkar zata faso boxes ɗin ta fito woje.
Shiyasa yake jin tsikar jikinshi yana zubawa.
A hankali ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, wanka yayi kana, ya fito ya kimtsa ya shirya jikinsa cikin manyan kayan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button