GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Daga nan suka zauna suna al’hinin abin.

Har azahar tayi nan suka watse kowa taje tayi salla.
Ita Umaymah a ɗakin Aysha tayi salla.

Bayan sunyi sallan ne Ummi ta kawo musu abinci suka ɗan ci.

A nan suka zauna Ummi da Umaymah a ɗakin Aysha.
Juwairiyya kuma taja Hibba suka tafi dan yin girkin dare.

Haka suka zauna har la’asar bata tashiba.

Sheykh kuwa sai ƙarfe biyar na yamma ya dawo gida daga asibitinshi.

Nasa falone ya wuce Side ɗinsa kai tsaye.

Biyar da miti bakwai dai-dai ta farka daga nannauyan baccin azabar.
Da sauri Umaymah tayi kanta.
Ganin tana ƙoƙarin tashine yasa Umaymah taimaka mata.
Cikin disashewar muryar tace.
“Lah Umaymah yaushe kikazo? Sannu da zuwa”.
Cikin tausaya mata tace.
“Sannu Aysha ai ke za’a cewa sannu. Ya jikin naki”.
Cikin sanyi tace Alhamdulillah”.

Sai kuma ta zuro ƙafafuwan ƙasa tare da cewa.
“Umaymah zanyi salla zanyi wonka”.
To tace da sauri kana ta juya zata shiga bathroom ɗin.
Da sauri Ummi tace bari in haɗa mata ruwan wonka.”

Umaymah kuwa kamota tayi ta tsayar da ita.
Dai-dai lokacin Ummi ta fito hannun ta zubawa ido cikin sanyi tace.
“Ya naga kamar hannun ya ƙara kumɓura ne?”.
Kallon hannun sukayi a tare.
Cikin sanyi tace.
“Eh kamar ya ƙara kumɓura”.
Umaymah ce ta ɗan kalli hannun kana tace.
“Je kiyi wonka ki fito kizo kiyi salla kici abinci, in baki mgnin da nazo miki dashi.”

To tace kana ta nufi Bathroom ɗin tana cewa.
“Bana iya gogo sosa a jikina sai sabulu kawai.
Shiyasa nakeji kamar ba wonka nakeyi ba”.
Cikin tausayawa Ummi tace.
“Allah sarki in kin samu lfy dai shike nan”.

A haka ta shiga bathroom ɗin yau ko sabulun bata iya gogashi da kyauba.

Ita kuma Ummi kaya ta fito mata dashi kamar kullum.

Ita kuwa Umaymah Dinning area taje.
Ta ɗauko Foodflaks ɗin da plate ta dawo nan.

A hankali ta fito bathroom ɗin.

Cikin ɗaga hannun sama ta kalli rigar da aka fito mata dashi a hankali tace.
“Ummi bazan iya sashi ba, matsastsene a bani mai faɗi”.

To Ummi tace ta sauya mata wani.
Mai faɗin ita kuwa dogon wondon dake kan gado ta ɗauka ta koma bathroom ta saka da kyar sannan ta fito.

Koda Ummi ta bata rigar sai ta gaza sata.
Ido cike da hawaye tace.
“Ummi samun hannun rigar a hannu mai ciwon a hankali kada ya taɓa shi, sai kin buɗashi da hannu biyu.
Cikin sanyi Umaymah tace.
“Bakisa bra ɗinba”.

Kanta ta sunkuyar tare da cewa.
“Bazan iyaba”.
Shiru Umaymah tayi tana tunanin dole jinyar hannu sai da mataimaki.
Ita da Ummi kuma surkaine Hibba ƙaramace.
Shiru dai tayi tana nazari.
Bayan Ummi ta taimaka mata tasa rigar ne.
Ta saka hijabi tayi sallan a daddafe da taimakon lafiyayyan hannun.
Tana idarwa Umaymah tasa mata abinci a plate kasan cewar tuwone da miyar ganye da ɗan tsami.
Sai ya zama gaba ɗaya a kaikaice take sa spoon ɗin da niyar gutsuro tuwon.
Kuma taji tana son cin miyar.
Da kyar ta gutsuro gaya ta ɗan ɗebi miya ta ɗaya zata kaishi bakinta kenan ya faɗi a jikinta.

A hankali ta kallesu cikin sanyi tace.
“Umaymah a bani tea kawai bazan iya cin wannan ba, zai tazubewa.”

Da sauri Ummi ta gyara zama tare da cewa.
“To matso in baki”.
Ɗan gajeren murmushi tayi cikin jin kunya tace.
“A a bari in sake gwadawa to”.

Dai-dai lokacin Sheykh da Umaymah ta kirashi a waya ya shigo yanata buɗe al’kyabbar jikinshi gudun kada a iya ganin tudun abinda yake ɓoyewa.

A bakin ƙofar ya tsaya tare da yin sallama.
Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace.
“Shigo”.

A hankali ya tura ƙofar ya shigo.
Tunda tazo gidan tsawon watanni biyu kenan yanzu bai taɓa tako ƙafarsa nan ba sai yanzu.

Ta gefen ido ya kalleta ta sake ɗaukan loma a karo na uku kafin ta kaishi bakinta ya ɓare.
Ture plate ɗin tayi tare da cewa.
“Bana iya cin abu da hagu gwara tea zan iya kafa kofin insha wani wani ya ɗan zube”.
Ta ƙarishe mgnar tana shere hawayen da suka zuba mata.

A hankali Ummi taja flaks ta fara haɗa mata tea.
Umaymah kuwa.
Gefenta kan Bedside drower’n ta nuna mishi tare da cewa.
“Zauna”.
fuska ya ɗan kauda kana ya zauna.
A hankali tace.
“Me zamuyi kan hannun yarinyar nanne?”.
Cikin jin haushi yace.
“Sai abinda su Lamiɗo sukace ai.
Ni Ko nayi mgna sai sun musamin ya rigada sun maidani kamar sa’ansu, bani da ancin mgn kan komai nawa sai yadda suka tsara min in naƙi bin unarninsu keda Abba kuyi faɗa, to ya zanyi?”.
Murmushi Ummi tayi ganin yadda yayi mgnar a tsare kamar shine babba a kansu ba suba wai sun ɗauke shi sa’ansu.
Ita kuwa Umaymah cikin sanyi tace.
“Kaga bata iya ko cin abinci tana bukatar kulawa ta musamman.
Wonka ma wuya yake bata haka al’wala ko kaya sai an saka mata”.
A hankali yace.
“Toh lallai kam Allah ya baku ladan jinya”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Amin”. A ranta kuma tace.
“Zanyi mgninka”.

Ganin tayi shiru ne ya sashi miƙewa tare da cewa.
“Allah ya sauwaƙa kana ya fita.”
Yana mai jin zafin katsalandar dasu Lamiɗo ke mishi a kan lamuran rayuwarshi, komai nashi sai sun saka mishi baki. Yace kar asa mgnin amman dan rainin wayo sunce dole sai an saka.

Su Umaymah kuwa nan suka zauna har akayi sallan magriba.
Su Jalal Jamil Affan sukazo suka ci abinci aka ɗanyi hira dasu.

Har zuwa ƙarfe goma na dare hannun shiru ba ciwon sosai.

Haka kowa ya shiga yana cemata saida safe Allah ƙara sauƙin.
Umaymah tace Ummi ta tafi da Hibba ɗakinta ita zasu kwana tare.

Haka kuwa akayi, har sun fara bacci.

Habawa sha ɗaya dai-dai,
Ciwo yace salamu alaikum.
Tashin hankali iya tashin hankali Umaymah ta ganshi a ranan.
Domin har gabanin asuba basu rintsaba kamar dai yadda ta kwana jiya da Ummi abinma har yafi haka yau.
Sau biyar Umaymah na kiran layukanshi duka basa shiga.
Kuma Aysha guduwa kawai take nufa.
Haka yasa dole tai ta riƙe ta.

Asuba na ƙaratowa tayi bacci kamar na jiya.

Sai da akayi sallan Umaymah ta tada ita.
Tayi salla lfy tasha tea.
ta koma bacci rana na fitowa ciwo ya dawo.

Gaba ɗayansu sun gigice sun tsorita da lamarin Umaymah ta tura Ummi taje ta gayawa Lamiɗo yazo yaga yadda take.

Hibba kuwa da Saratu sun kasa yin aikin da aka sasu sai kuka.

Hannun kuma yau yayi biyun na jiya.
Idanunta sun kaɗa sunyi jazir.
tana zaune kan kujera Umaymah na tsaye gefenta gudun kadda ta arce.
Ta ɗaura hannun a kai tana kuka iya kuka, kukan azaba haɗe da salati.
A haka Sheykh ya shigo ya samesu.
Cikin takaici Umaymah ta juya ta nufi falon Ayshan tana kallonshi tana cewa.
“Gata ka barta kada ka kula da jinyarta da haƙƙinta ne Allah ya rataya a kan wuyanka ai ka fini sani.
Ka sani kana take sani”.
Ta ƙarishe mgnar tana zubda hawaye sabida duk wanda yaji kukan da Aysha keyi yasan na wahala ne.

Ita kuwa Aysha da sauri ta miƙe ta kife kanta jikin gini tana mai ci gaba da kuka.
Jamil, Jalal, Affan, sunata yi mata sannu.

A hankali yabi bayan Umaymah da kallo tabbas ranta yayi matuƙar ɓaci, ga tashin hankali ga rashin bacci.

A hankali ya isa inda take.
Hannunshi yasa ya kamo nata. Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi, cikin zubda zafafan hawaye tare da cewa.
“Yah Sheykh zafi, hannuna zai tsinke.”
Wani irin masifeffen rauni da tausayinta ne yaji sun rufeshi, kanshi ya juya cikin sanyi, yaja hannuntan.
Suka nufi ɗakishi.
Ita dai binshi a baya takeyi tana tafiya kamar a sama takejin kanta.
Kai tsaye har bedroom ya wuce da ita.
Kan gadonshi ya ajiyeta yanajin kukanta na hawa kanshi.

Bakin gadon ya zauna ya bata baya tare da cewa.
“Ki kwanta kiyi addu’a zakiji sauƙi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button