GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ba jinshi takeyi ba bare ta gane abinda yake nufi.
Da sauri ta yunƙura zata sauƙa.
Juyowa yayi ya kamata ya ajiyeta kusa dashi kana ya juyo suna fuskantar juna.

Cikin kuka ta faɗa jikinshi tana cewa.
“Umaymah hannu zai tsinke.
Zafi zai kasheni”.
A hankali ya ruggumeta tare dasa hannunshi ya kamo hannun dake ciwon.
Da sauri tayi tsalle zata zille hakan ne yasa ya ƙara ruggumeta gama ya haɗa jikinsu wuri ɗaya.
cikin sanyi ya fara mata karatu a kunne yana hura mata iskar bakinshi kan hannun

Ajiyan zuciya mai ƙarfi da numfarfashi ta fara sauƙewa da ƙarfi-ƙarfi.

Umaymah kuwa jin shirune yasa, ta nufo Side ɗinsa.
Ganin baya falone.
Tace.
“To ina suke ina ya kaita?”.
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom.

Tana tura ƙofar sai kuma tayi sauri taja da baya sabida hangosu da tayi yana konce lib yayi rigingine ya ɗan jingina da allon kan gadon.
Kana ita kuma ya kontar da ita kan jikinshi, ya ɗaura kanta bisa ƙirjinshi hannunshi na kan…!

Jinyar Sheykh ta musamman ce. To ya zata kaya ne in ɗan gidan ba’ana yazo. Hege Sarkin baka wa yakewa aikin.

                       By

          *GARKUWAR FULANI*

Cikin tsuke fuskarsa da muryar dake nuna zafin abinda ke zuciyarshi yace.
“Ummi in ya fito kiyi mishi jagora zuwa wurin sarkin ƙofa ki nunashi kada a sake barin yazo ko kusa da katangar masarautar Joɗa ne, a korashi ya bar jihar Ɓadamaya.”

Da sauri Ummi tace. “Toh”.
Kana tayi gaba tare da cewa.
“Mu tafi”.
Da sauri Barun yabi bayanta.

A can falon Sheykh kuwa komawa yayi ya zauna gaban Bappa cikin sanyi yace.
“Bappa kayi haƙuri, ka gafarceni, bisa korarshi da nayi.
Wannan sunada manufar data kawoshi, ni zan ji da ciwon hannunta, in sha Allah zata samu lfy. Ka kwantar da hankalinka.”

Ido Aysha ta zuba mishi cike da mamakin ta ina ta yaya ya gane meke tafe da Barun har ya gane sunada wata manufa, ta yaya ya gano kuramen bakin da Barun ya karanta mata, ta yaya yayi musu wasali har ya basu cikekkiyar jimla ya karancesu da fassararsu, meya sani a kanta.

Hakama Bappan kallon Mamaki yakeyi mishi amman sai ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Ba komai Muhammad Allah ya bamu sa’a ya kuma bata lfy”.

Amin Amin yace shida Umaymah.

Al’amin ne ya ɗan gyara zama tare da cewa.
“To Allah yasa a dace. Amman ko za’a gwada asibiti ne?.”
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Kada ka damu, in sha Allah ba damuwa”.
Kai ya ɗan gyaɗa cikin gamsuwa.
A hankali Umaymah ta miƙe ta fita.

Shi kuwa Sheykh Aysha ya kalla tare da cewa.
“Tashi ki barsu suci abinci mana”.
Da sauri Bappa da Al’amin sukayi mgna kusan a tare sukace.
“Alhamdulillah mun ƙoshi”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Al’ameen da kyau kana a hankali yace.
“Ba’a zuwa masarautar Joɗa a fita ba’aci komaiba”.
Murmushi mai cike da gamsuwa Bappa yayi kana yace.
“Eh Alhamdulillah munci a wurin Lamiɗo ai”.
Kanshi ya gyaɗa cikin gamsuwa da hakan yace.
“Toh Bappa”.
Cikin sanyi ita kuma Aysha tace.
“Ya Al’amin bani zanci”.
Murmushi Al’amin yayi kana ya jawo Foodflaks ɗin,
a plate ya zuba mata Couscous da biyar hanta.
gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau itama gyara zamanta tayi.
Bappa kuwa Murmushi yayi yana kallonsu.

Shi kuwa Sheykh ido ya zuba musu zaiga dai iya gudun ruwansu duk da zuciyarshi ta gama gano mishi nasabarsu.

Shi kuwa Al’ameen. A hankali yasa spoon ya ɗan ɗibo, kana ya nufi bakinta da spoon ɗin tare da cewa.
“Ha, buɗe bakin”.

To tace kana ta buɗe bakin ya saka mata.
lumshe idonta tayi tare da tauna abincin dan ya mata daɗi.
Sake dibowa yayi ya bata, still ta buɗe baki yasa mata.

Cire kanshi yayi a kansu, ya maida dubanshi kan Bappa dake mishi mgna.
Umaymah da Ummi ne suka shigo a tare ita Ummi cewa.
Sheykh tayi an fidda Barun.

Ita kuwa Umaymah ƙwaryar fura da nono ta kawo musu.

Murmushi sukayi ganin yadda Aysha ta zage tana cin abinci.
Shi kuwa Al’amin ya dage yana bata.
“Ya Al’amin zan sha ruwa”.
Tace mishi tana taunar sokar naman da yasa mata a baki.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah tare da cewa.
“Allah rene a sammin ruwa in bata”.

To Umaymah tace ta miƙo mishi ruwa.
Tana kallon kamanninshi da Aysha ba sai an gaya maka cewar ɗan uwanta jininta bane.
Bata ruwan yayi har baki.
Tasha sosai.
Kana ya kalleta tare da cewa.
“In ƙara miki abincin ne?”.
Kai ta gyaɗa mishi.
murmushi yayi tare da cewa.
“Bubbuga rumbun Abboi”.
Murmushi tayi itama tana mai share hawayen da suka silalo mata.
Ƙara mata yayi tare da ci gaba da bata.
Sosai kuwa taci tayi haniƙan.
Sheykh kuwa da wutsiyar idonshi yake kallon dukkan motsinsu.
Bayan tayi gyatsa ne, Ummi ta matsar da kwanukan.
Babu yadda Sheykh da Umaymah basuyiba, amman Al’amin da Bappa sunƙi suci abinci.

Kiran sallan azahar ne,
Yasa duk suka miƙe.

Cikin sanyi Al’amin ya kalli ogogon hannunshi da yaketa sheƙi yace.
“Bappa muyi salla mu tafi kada lokacin ya ƙure mana”.
Cikin kula Umaymah tace.
“Ba kwana zamuyi ba”.
Murmushi Bappa yayi tare da cewa.
“A’a zamu koma tunda jiki da sauƙin gata taci ta ƙoshi tana hira.”
A hankali Ummi tace.
“Eh ai dama haka takeyi, anjima kuma in ciwon ya tashi zakace kamar zata shiɗe, sai an mata tofi take ɗan samun sauƙin”.
Murmushi Al’amin yayi tare da kallon Sheykh cikin nitsuwa da gogewar cikar wayewar dake nuni ba makiyayin daji bane yace.
“Sheykh ka samu sabuwar wayar hannu, kenan tunda sai kayi tofi akejin sauki.
Dan Allah duk inda kake ta kasance a nan a ƙara kulan mana da Boɗɗin Abbai”.
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
“In Sha Allah”.
Cikin karrama Sheykh ya nuna musu wata ƙofar dake gefen ɗakinshi yace.
“Ga wuri kuyi al’wala mu tafi masallacin”.
kai Al’amin ya gyaɗa kana yace.
“Bappa je kayi al’wala kazo mu tafi.
Cikin nitsuwa Bappa yace da al’wala ta”.
Shima Al’amin gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
“Nima inada al’wala”.

Cikin gamsuwa Sheykh yace.
“To bisimilla muje nima da al’wala”.
To sukace kana duk suka nufi babban falon.

Suna isa tsakiyar falon. Al’amin ya ɗan tsaya tare da cewa.
“Parvina zo”.
Da sauri ta ƙaraso gabanshi.
Shiru sukayi jin Al’amin ya juya harshe zuwa wani Yaren ba larabciba ba Turanciba ba hausaba ba fillanciba.

Mgna yakeyi riƙe da hannunta.
Ita kuwa Aysha kai taketa gyaɗa mishi ido cike da kwalla.
Hannunshi yasa ya share mata hawayen kana yasa hannunshi ya shafa kanta tare da juyawa ya fita.
Ita kuwa Aysha cikin sanyi tace.
“Bappa dan Allah a kawo min Junainah”.
Kanshi ya gyaɗa kana shima ya fita.
Binsu a baya Sheykh yayi.

Ita kuwa hannunta mai lfyar tasa ta share siraran hawayen da suka zubo mata.
Kana ta juya ta nufi ɗakinta.
Ummi da Umaymah kuwa kallon juna sukayi suma suka wuce ɗakin su.

Bayan an idar da sallan ne, Sheykh da kanshi ya ɗauki su Bappa ya kaisu tasha kamar yadda sukace.

Bayan ya kaisune. Yayi musu fatan isa lfy ne, yaja motarsa kamar ya tafi.
Ya koma can baya ya ajiye motar kana ya kira Ado drevernshi da yake cikin but ya fito.
Sannan yace.
“Bisu”.

Da sauri Ado yabi bayansu.

Shi kuma yayi gida.

A hankali Ado yake binsu.
Ga mamakinshi sai yaga sun tari taxi sun shiga.
Shima taxi ya tsaida ya shiga,
tare da cewa.
“Bisu duk inda suka nufa.”

To yace, kana yabi bayansu kai tsaye international airport Ɓadamaya suka shiga.
Suna shiga.

Kuwa suka fito. Suka biya mai taxi ɗin da kuɗin ma da bana ƙasar Nigeria bane kuɗin ƙasar Cameroon ne.
Cikin sanyi Al’amin yace.
“Yi haƙuri bamu da canji ne, kaje wurin yan canji za’a canza maka su zuwa Naira”.
Cikin jin daɗi mai taxi ɗin ya tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button