GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Barun kuwa ana korashi ya nufi ƙasar Cameroon, Ba’ana bai iya jiranshi ba, tahowa yayi suka haɗu ya gaya mishi duk yadda sukayi da Sheykh.
Nan suka sake komawa cikin Rugar tasu can inda ya samu sabon uban gida.
Yanaji kamar ya mutu dan baƙin ciki.
Nan yaci gaba da shirya yaƙan Sheykh.

A nan kuwa ɗakin Aysha.
Ƙarfe ɗaya da rabi Aysha ta farka da salati a bakinta.
Cikin sauri ta buɗe idonta.
Tare da miƙewa a hankali ta nufi falon.
Domin taji zogin na dawowa.
Tazo falon kenan ta hango mutun da irin shigar ranan cikin tsoro tace.
“Waye ne kai me kakeyi mana a nan?”.
Juyowa yayi ya kalleta cikin isa ya fara takowa zuwa gabanta.
Da sauri ta fara jan baya-baya tana cewa.
“Me hakan? Me kake nema damu?”.
Cikin Tsuke fuskarsa yace.
“Me na samu dai. Ai Jahan tun kafin ya nemi abu yake samun abun a hannunshi”.
Da ƙarfi ta buɗe bakinta zata zurma ihu.
Taku biyu yayi ana uku ya isota.
Tafin hannunshi yasa ya rufe mata baki tare da cewa.
“Kada ki razana wancan mataccen mijin naki”.
Wani irin zazzaro ido tayi tare da jujjuyasu cikin alamun firgici da tsoro da kiɗima.
Kanshi ya jujjuya mata tare da cewa.
“Kada kisa zuciyarki ta buga a banza dan nace wancan mataccen mijin naki.
Ban kasheshi ba, amman dai ke a wurinki dashi da mace yar uwarki ba sauyi”.
Hannunta mai lfyar ta fara kiciniyar ɗagawa zata ture hannunshi da ya ɗaura kan bakinta, ya rufe, ya haɗa kanta kuma da jikin gini.

Juyota yayi da ƙarfi ya manna bayanta da ƙirjinshi still hannunshi na kan bakinta.
Ɗaya hannun kuma, bisa ƙirjinta ya ɗaura.

Taku ya farayi yana janta ya nufi hanyar fita woje.

Wani irin bugu zuciyarta keyi tamkar zai faso ƙirjinta ya faɗo woje.
Zuface ta tsananin firgita da tsoro ta karyo mata tako ina na jikinta.
Tuni tsoro yasa numfashin ta ya fara subce mata.
Kiciniyar kwace kanta takeyi ta samu damar yin ihun amman ta kasa.

Sabida ba ƙaramin riƙo yayi mataba.

Hannunshi dake kan ƙirjinta ya cusa cikin rigar ta saman wuyan rigar tata.

Wani irin azabebben cizo ta dartsawa tafin hannunshi,
amman duk da haka bai janye hannun nashi ba.
Sai ma lumshe idonshi yayi tare da jan dogon numfashi mai fitar da ɗimaucewar da yake ciki.
Wani irin shafa yayiwa breast ɗinta, wanda yasashi rawan jiki bnnarsa tayi wani irin azabebben zabura da miƙewa gal.
wani kiciniya ta fara da iya karfinta dai-dai lokacin kuma suka iso bakin ƙofar fitan

Hannunshi dake cikin rigarta ya zaro bayan ya burza nimple ɗin ta.

Murza key ɗin ƙofar yayi ya kana ya jawo ƙofar ya buɗe.
Wani irin karkarwa jikinta ya fara,
Garin son kwace kanta da neman taimakon kanta, ta buge hannunta mai ciwon jikin ƙofar.

Dai-dai lokacin kuma ya janye hannuunshi kan bakinta.
Wani irin razanenne kuma gigitaccen ihu tasa mai sauti.

Shi kuwa Jahan da gudu ya fice kamar walƙiya.

Ita kuwa cikin karkarwa da tsoro da gigita ta juya ta nufi cikin falon tare da zurma wani ihun mai cike da kiɗima da azaba gaba ɗaya jikinta karkarwa yake.

Cikin bacci Umaymah da Ummi suka jiyo ihunta da rabka musu kiran da takeyi.
A guje suka fito cikin ɗakunan suka nufo inda suke jin ihunta.

A bakin ƙofar suka haɗu cikin karkarwa ta faɗa jikin Umaymah tare da Ruggume ta da hannu ɗaya.
Cikin kuka da fitan haiyaci take cewa.
“Umaymah wani, Ummi yau ma ya sake shigowa, zai saceni ya jani har bakin ƙofa, kunga can ƙofar a buɗe ko.
Wayyo Allah na, wayyo hannuna”.
Da sauri Umaymah ta ruggumeta gab zamewa tayi suka zauna a nan.
Ummi kuwa hannunta mai ciwon da taga yana rawa tamkar mazari ne ta rinƙa hurawa iska tana cewa.
“Sannu Aysha innalillahi sannu”.
Sai ta kuma fara kiran Sheykh.
“Sheykh! Sheykh!! Sheykh!!!”.
A gigice ya buɗe ƙofarshi ya fito,
ya nufi inda suke yana cewa.
“Na’am! Na’am Ummi meya faru ne”.
Cikin gigita tace kalli fa.
Dai-dai lokacin kuma numfashin ta ya tafi cak ta sume tana cewa.
“Jahan wai zai saceni”.
Cikin gigita Umaymah tace.
“Jazlaan ta suma, ta sumafa.
Waye ne Jahan kagafa can ƙofar a buɗe”.
Hannunshi yasa ya amsheta jikin Umaymah dan yaga itama jikinta karkarwa yakeyi.
Ruwan sanyin da Ummi ta miƙo mishi ya amsa, kana ya kurba a bakinshi ya fesa mata ruwan a fuska.
Cikin wani irin jan dogon numfashi ta sa hannunta mai lfyar ta saƙalo wuyanshi, tare da ɓoye fuskarta cikin jikinshi tana cewa.
“Zai saceni, ɗan iska ne shi”.
Ummi ce ta miƙe taje ta rufe ƙofar.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya kalli Umaymah dake gigice yace.
“Umaymah ki kontar da hankalinki, babu abinda zai samemu da izinin ubangiji.
Kije ku kwanta. Ummi kuje,
kwana kima tayi haka cikin Ramadan inaga al’janunta ne ke rikitata.
Dan ranar da tace ta ganshi ya shiga Side na ba inda bamu dubaba ba kowa”.
Cikin kiɗima Umaymah tace.
“Yau dai kam tabbas akwai abinda ta gani tunda harda suma kuma ga ƙofar a buɗe, Jazlaan na gaji wlh zaku bar Masarautar Joɗa ko zamu samu kwanciyar hankali a rayuwar mu”.
Cikin son kontar mata da hankali ya ɗan dafe kanshi kana yace.
“To Umaymah zamu barta jeki kiyi al’wala kiyi addu’a Allah ya kare mu”.
Ya ƙareshe mgnar yana miƙewa tsaye da ita a jikinshi.
Dan tayi mishi riƙon ɗaurin goro da hannunta mai lafiya.

A hankali Umaymah da Ummi suka juya suka tafi.

Shi kuwa Side ɗinsa ya nufa, kai tsaye.
Har cikin Bedroom, maida ƙofar yayi ya rufe.
Kana yazo kan gado ya sunkuyo ya kwantar da ita.
Jin yadda ta riƙe mishi wuya ƙam-ƙam ne ya sashi cewa.
“Zafa ki kasheni da shaƙa”.
Shiru tayi tana ƙanƙame da wuyanshi, hannunta sai karkarwa yake amman bata kuka alamun zafin yayi zafi tsananin yayi tsanani domin wani zafin ya wuce inda hawaye suke.

Dole a hankali ya zame wuyanshi kana ya zauna gefenta.
Idonta suna buɗe amman sunyi masifar ja, goshinta sai zufa yake tsastsafowa.
Numfashin ta wani na korar wani.

A hankali ya gyara zamanshi ya fara yi mata tofi yana karanta duk surar da tazo bakinshi.

A hankali hannun ya fara rage karkarwan.
Tsawon miti talatin yana mata tofi yana jin tausayinta har cikin ransa ya dade yana mata tofin.
Sannan ta iya juyowa ta kalleshi cikin rauni da zubda hawaye tace.
“Yah Sheykh ka yanke min hannunan mana ko zan huta da azabar da nakeji in ya tashi”.
Ido ya ɗan zuba mata tare da cewa.
“Kiyi bacci kinji ko?”.
A hankali tace.
“Ina tsoronshi kar ya dawo”.
Cikin sunkuyowa yana kallon hannun yace.
“Bazai shigo ɗakina ba. Ki dena tsoronshi babu abinda ya isa ya miki! Ki dena tsoronshi ko yaushe yana tare dake bai cutar da keba ki yarda dani”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Ɗan iska ne mugu ne”.
Cike da mamaki ya yamutsa fuska tare da cewa.
“Ɗan iska kuma to me yayi miki na iskanci?”.
yunƙura tayi ta konta kan gefenta na hagu ya zama fuskarta na kusa da cinyarshi a hankali tace.
“Tattaɓani yayi, yasa hannunshi har cikin”.
Sai kuma tayi shiru, cikin rumtse idonshi yace.
“Cikin me?”.
A hankali murya na rawa tace.
“Cikin rigata yana taɓa min”.
Fuskarshi a murtuƙe kamar zaiyi ruwan jini yace.
“Meyasa kika tsaya har ya taɓa ki, kema iskancin kikeso ayi da keɗin inba iskanciba, ai hannunki ne ke ciwo ba ƙafarki ba, ki gudu mana”.
Juyowa yayi ya fuskanceta tare da ciwa.
“Tukunma wanne iskancin ne ke fito dake da dare, in ba bikinku ba ɗaya ba, zakizo kina mana ihu da suman ƙarya ai so kike ayi ta taɓe-taɓe ko?.
In tattaɓakin kikeso anayi ki gaya min mana ba sai in tattaɓakin ba hankalinki ya kwanta in miki abin da kikeso duka har sai kince ya isheki”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Ina gudu ya kamoni kuma na fitone zanzo kamin tofi a hannuna na haɗu dashi.
Wlh ni dai ba yar iska bace.
Inata ihu har na fame hannuna Ina kafin kukaji kuka fito”.
Wani irin kallo ya watsa mata ƙasa-ƙasa kana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button