GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar lumshe idonshi yayi a ranshi yake haɗa kalaman da yaci karo dasu a safiyar yau.
Kakarshi tace mishi, aji mgnar Malam kada a duba aikinshi, ta jaddada mishi, wai yayi aure, kana wannan mayyar yarinyar da in tana kusa dashi zuciyarshi ke barazar fashewa, kuma tace mishi wai shine shugaban tuzuran ƙasar nan baki ɗaya.
Tabbas wannan shaidace na abinda ake faɗa a cikin gari a kansa kenan, yaji ya sani Sitti ma da take son suje saudia wai so take ya zaɓi matar aure a can, ga wannan kafurar da ya san turota akeyi ta tallata mishi kanta, don a samu cinikin jarida ya hauhawa ta hanyar buga kanun labarai cewa, Sheykh mazinacine ko kuma mata yakebi shine ya hanasa aure.
Jingina kanshi yayi da kujerar tare da mgn a zuciyarsa.
“Ya ilahi ya mujibadda’awati”.
Ta yayane ta inane wa zai gayawa cewa,
shifa yanada banbanci da sauran maza, ba kamar kowa yake ba, taya zai gaya musu ko zai samu a daina binshi da kalmar yayi aure, me zaiyi da mace ta yaya zai fahimtar dasu su barshi ya huta.

Wannan shine nazarin da yakeyi cikin zuciyarshi,

Ita kuwa Aysha ido ta tsurawa, ƙasan kujerar da yake zaune a kai tana kallon wani al’amari mai cike da ruɗarwa.
Ido ta rumtse sabida bazata iya jurar ganin wannan abun ba.

A hankali Nos ɗin nan ya matso gabanshi, magungunan da alluran daya amso ya miƙa mishi su.

Cikin sanyi yace.
“Sir ga magungunan”.
Kanshi ya ɗan tankwarar tare da cewa.
“Kira Dr Ruƙayya tazo ta mata alluran”.
A hankali yace.
“Sir na duba duk sun tashi, sabida babu kowa. A Reception ɗin, mune kadai muka rage”.
Kanshi ya jinjina, don shima yanzu zai tafi, sabida akwai gidajen likitocin a nan kusa koda shi ya tafi Dr Ruƙayya da Dr Ute suna nan cikin makarantar.
Ta gefen idonshi ya ɗan kalli Aysha daketa fama da ciwo,
Ganin Nos ɗin na haɗa allurar ne yasashi, fara tattara woyoyinsh dake bisa table ɗin.

Shi kuwa nos ɗin. Yana gama haɗa alluran ya nufi inda take, tare da cewa.
“Gyara in miki alluran”.
Cikin sanyi tace.
“To”. Yana isowa gabanta yace.
“Dole ai sai kin tashi tsaye, kinga doguwar rigace a jikinki kuma sai kin naɗeta”.
Ido ta ɗan zuba mishi ta cikin niƙabin tare da jujjuya kai a hankali tace.
“Um ummm”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Tashi mana sauri mukeyi lokacin sallah ya ƙara to”.
Shi dai Sheykh ido ya zubawa bayan Nos ɗin yayinda ita kuwa yake kallon gefenta, cikin bada umarni yace.
“Kuzo”.
Da sauri Nos ɗin ya juyo ya nufoshi,
hannu yasa ya amshi allurar,
kana ya ɗan kalleta a fakaice yace.
“Zo nan”.
A hankali ta taso cikin sanyi takeyin taku tana matsoshi.
A take kuma bugun zuciyarshin ya fara hauhawa yana komawa matakin sama.
Taku biyu tayi ana uku yaji ƙirjinshi ya bar tsinkewar da yaketa yi ɗin, sai kuma bugun da yakeyi da sauri-saurin ne yaketa tsananta.

Taku takwas tayi ta iso tsakiyar Office ɗin, ido ya fara jujjuyawa kan table nashi yana mai jin wani masifeffen bugun zuciyarshin dayasashi hatsala cikin ɗan ɗaga murya yace.
“Ke da Allah kiyi sauri”.
Jin hakane yasa ta kara saurinta, ai kuwa da sauri ya dafe ƙirjinshi lokacin da ta iso gab dashi, cikin ranshi ya kuma cewa.
“Hasbunallahiwani’imanwakil”.
A zahiri kuwa, da kai ya nuna mata ta kuma matsowa, ba musu ta matso,
yatsarshi ya jujjuya mata alamun ta juya mishi baya,
still babu musu ta juya, a hankali ya murza kujerar da yake kanta, ya juyo ya fuskanci bayanta, dai-dai saman mazaunanta ta sama ta ɗan gefe kaɗan, ya saita, tsinin bakin allurar, cikin iyawa da gwarewa dan salonshi ne baya taɓa yarda ya kalli fatar jikin wanda zaiyiwa alluran ta saman tufafinka yake zira allurar, shiru tayi tana jin yadda, allurar ya ratsa dogon rigar jikinta ya bada sautin tub alamun ya huda rugar, a hankali ta kuma jin ya huda, dogon wondon jikinta tub, sai kuma taji ya sauƙa kan pantien jikinta, daga nan taji ya ɗisa bakin allurar kan fatarta, rumtse idanunta tayi da azaban ƙarfi sabida, wani zafi da taji yana ratsata, bawai tana tsoron Allurar bane, sai dai hannunshi yanada masifar zafine,
kana shina ruwan alluran irin mai, mai-mai ɗinanne kuma duk cikin allurai yafi zafi.
Da ƙarfi tace.
“Wach Allah na zafi-zaffi.”
Wani irin azaba taji lokacin daya fara cusa mata ruwan allurar a jikinta, babu zato babu sammani yaji tasa hannu damanta ta cabki hannunshi dake mata alluran hannunta na hagu kuwa yarfashi take tare dasa kuka da sauti tace.
“Wayyo Allah na, ka bari bana so zare Allurar nan zafi nakeji”.
Ta ƙarishe magar da zurma sakalin ihu”.
Bugawa da zuciyarshi keyi yana bada sautin dib dab dib dab dib dan shine ya kusan hallakashi lokacin data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi.
Sannan ya miƙe tsaye, sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje.
Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Nos ɗin ya fice.

Itama da sauri tabi bayanshi bayan tasa hannu ta amshi ledan magungunan.

Shi kuwa da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi babu ƙaƙƙautawa.

Ita kuwa AYSHA da sauri ta nufi sashin makwancin ɗaliban Hostel dake cikin makarantar sabida ta fara jiyo alamun bakonta ya iso.

Baba Ado kuwa drevernshi yana hangoshi ya tashi ya buɗe mishi marfin motar, yana zuwa, ya shiga, maida kofar Baba Ado yayi ya rufe sannan ya shiga yaja motar suka fice daga harabar asibitin.

Ita kuwa Aysha tana shiga Side ɗinsu ita da Rafi’a, ta samu Rafi’a bata falo da alamun tana kitchen nasu, dan tajiyo ƙamshi alamun tana ɗan dafa musu abinda zasuci ne.
Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, dan haka ta nitsu ta gyara jikinta, bayan ta gama ne ta miƙe a hankali ta kwance niƙabin tare da fara zare dukkan kayan jikinta dan yin wonka,
Aysha farar ba fullatanace irin farare ƙal-ƙal ɗin nance, gashin kanta kuwa mai tarin yawa da tsawone baƙine sit mai sheƙi, yanada cika,
jikinta ɗan fiyau, sai dai tanada welcome and bey bey masu girma da cika, cikinta kamar babu hanji a ciki ɗan fiyau dashi, breast ɗinta tirtsa-tirtsane masu cika tab-tab kuma irin mai gindin tasa ɗinnan wanda da alamun ba masu zubewa bane, domin suna nan cas dasu, kamar zasu tsone idon mai gani, tanada tsukekken ƙugu da kyawawan mazaunai, sawonta dai-dai musali baza’ace mata doguwa ba sam, kuma baza’a ce mata gajera sosaiba in tana kusa da dogo dai za’a iya kiranta da gajera.

Fuskarta kekyawa ce irin kyan da babu namijin da zai gani ya cire ido, hancinta dogo har kan ɗan ƙaramin bakinta mai jajayen tausasan laɓɓa idonta manyane sai dai ba ƙattiba, zirin idonta wurinda akesa kolli jane mai kyau, shiyasa yake ƙara baiyana farin idonta bakin ciki kuwa bakine sitik sai dai ɗan ƙaramin ɗigon cikin bakin shi kuma ruwan ƙasane wanda yakeda sirri namu samman.
Gashin idonta zara-zarane, gashin girarta kuwa irin mai W ɗin nanne kamar na Kajol, bi ma’ana yana haɗe bisa karan hancinta,
Tanada fararen haƙora masu kyau suna jere reras dasu tanada dimple ɗinta mai ɗan karen kyau. Idanunta kuma ko yaushe kamar maijin bacci suke.

Wonka tayi kana tayi al’wala dan ko bata salla bata zama babu al’wala.

Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button