GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin kulawa tace.
“Gida lfy lau. Ya jikin iyalin naka?”.

A hankali yace.
“Alhamdulillah”.

Da sauri tace.
“Muhammad yaushe zaka kawo min itane?”.

“Nima ban sani ba”. Ya bata amsa a gyatsine.

Murmushi tayi kana tace.
“Shike nan zan zo ai”.

Da sauri yace.
“A a bance ba, ki bari in ta samu lfy zata zo”.
To tace tana murmushi tasan yasan in tazo tofa.
sa’idonta yafi na akowa.
Duk motsinshi zata gayawa Lamiɗo.
Nan dai suka ɗan yi hira kana suka ƙatse kiran.

Da daren ranar kuwa koda suka zo konciya Umaymah tace.
“Aysha tafi ɗakin mijinki kar hannun ya tashi dare-dare ya zama kina fita.”
A hankali tace.
“Umaymah yau hannun da sauƙi tunda nasha ruwan addu’o’in nan bana jin zogin sosai”.

Cikin jin daɗi tace.
“To Allah yasa mu kwana lfy ba tashi”.
Amin Amin tace kana suka kwanta.

Allah cikin ikonsa da buwayarsa da al’farmar Annabi da al’ƙur’ani a daren sau biyu kawai ta ɗan tashi.
Shima in Umaymah ta shafa mata ruwan dai sai ta koma bacci a take.

Washe gari da safe kuwa,
Cikin mamaki ta kalli Umaymah dake shafa mata ruwan tace.
“Umaymah bakiga kamar kumburin ya raguba”.

Siyayan ruwan tayi a tafin hannunta tare da cewa.
“Sosai ma kuwa Aysha hannufa Alhamdulillah da sauƙi sosai.
Ga mgni kusa dake a bakin mijinki muje anyi ta wahala”.
Uhumm tace tare da sunkuyar da kanta.

Ummi kuwa Murmushi tayi.

Koda aka gama breakfast.

Ranar a haka a kaikacen ta daure taci.
Kafin azahar sosai hannun ya lafa.

Yau kuma tunda safe ko inda hanyar Side ɗinsa yake bata kallaba, in taji zogin ta ɗauko ruwan tasha a shafa mata.

Shi kuwa Sheykh ranar tunda safe ya fita bai dawoba sai tara da rabi na dare.

Still yauma an kwana hannun da sauƙin.

Washe gari da safe.

Sheykh ya kuma ɗauko wani zam-zam ɗin da ganyen magarya guda bakwai,
Yazo yana mata tofin cikin ruwan.
Yana mgnar zuci.
“Uhum jiki yayi sauƙi zamu huta da koken masifa da shogoɓar tsiya”.

Koda ya gama yaje ya ajiye a Fridge kana yazo.
Ya shiga wonka kasan cewar yau Monday ne tushen aiki ko nasara na tsoronta.

Ya fara kimtsawa.

Ita kuwa a falon bayan sunyi breakfast,
suka dawo nan cikin falon, juyowa tayi ta ɗan kalli Umaymah dake shigowa falon tace.
“Uhum Umaymah ruwan fa ya ƙare”.

Shigowa tayi ta zauna gefenta kana ta kalli hannun ya saɓe sosai.
“To kije ki gaya mishi mana, ai bai fitaba, tashi kije da sauri kada ya fita baki gaya mishi ba”.

To tace kana ta miƙe ta nufi can.

Tana shiga yana fitowa.
A hankali ta koma gefe ta tsaya.
“Ina kwana”. Tace mishi ido a ƙasa

Ta gefen idonshi ya kalleta tare da cewa
“Lfy ya jikin?.”

“Da sauki”. Tace kana ta ɗan kalleshi tare da cewa.
“Yah Sheykh!”.
Ido ya ɗan zuba mata kana yace.
“Na’am!”.

hannunta ta ɗan sa ta shafi fuskarta kana tace.
“Uhum dama maganin nawa ya ƙarene shiyasa nace bari in gaya maka”.

Hannunshi ya miƙo tare da cewa.
“Inga hannun”.

Ɗago hannun tayi ta miƙa mishi.
Amsar hannun yayi kana ya juyo ya nufi tsakiyar falon.
Tana biye dashi abaya.
Bisa kujera ya zauna tare da nuna mata gefenshi.
Zama tayi, duk yana riƙe da hannun,
ɗan sunkuyowa yayi ya fara karanta Suratul Baqra yana tofa mata, yana sa yatsunshi biyu yana ɗan murza hannun a hankali-hankali, ido ta ɗan rumtse tare da motsoshi jin yana ɗan jan hannun.

Wash tace a hankali.
Ɗan ƙara murza hannun yakeyi yana tofa mata.
Hannun hagunta tasa ta damƙi damtsen hannunshi na dama.
bai kulata ba yaci gaba da jujjuya mata hannun dan ya lura tana barin hannun a ƙage wuri ɗaya ko yaushe tana naɗe dashi.
Murza hannun yakeyi da ɗan janshi yana miƙar dashi da ɗan ƙarfi.
Wani irin bubbuga sawunta tayi tare motsoshi da kyau.
Tsakanin sawunshi tasa cinyarta ta dama.
kana tasa hannun hagun nata ta maƙaleshi.

duk ta kanainayeshi tako ina.
zuface ta fara keto mata tako ina na jikinta,
Ajiyan zuciya ta fara sauƙewa jin ya sake mata hannun.

Kanta ta manna a damtsen hannunshi tana maida numfashi.

Shi kuwa shiru yayi yana jin yadda take maida numfashi.
Kusa 6 minute kana a hankali yace.
“To ɗan sakeni in kin gama hutawa ko”.
A kunyace ta ɗan zame jikinta ta janye cinyarta.

Miƙewa tsaye yayi yana gyara al’kyabbar jikinshi.
goran ya ɗauko a Fridge ɗinsa kana ya miƙa mata.
Amsa tayi kana suka fito a tare.

Affan suka samu da matarsa Mami.

Suna fitowa Affan ya miƙa tare da miƙa wa Hamman nashi hannu bayan sun gaisane yace.
“Ya mai jikin dai?”.

“Alhamdulillah jiki da sauƙi”.
ya bashi amsa

Mami kuwa a hankali ta zame ta ɗan rusuna cikin girmamawa tace.
“Barka da safiya Hamma ya mai jiki”.

Hannunshi ya kai ya ɗan shafi kan ɗansu Karami Aliyu tare da cewa.
“Lfy lau Alhamdulillah jiki da sauƙi. ya yaran?”.

Suna lfy tace tare da kallon Aysha dake murmushi jin Affan na cewa.
“Aunty Aysha ya jikin dai yanzu kam hannun bazai faɗi bako”.

Murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah da sauƙi”.

Sallaman su Umaymah Sheykh yayi ya tafi.

Murmushi Mami tayi cikin son matar Hamman nasu tace.
“Ina kwana Aunty Aysha”.

“Lfy lau”.

“Ya jikin naki”. Tace tana kallon hannunta.

“Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai ma”.
Ta bata amsa.
Tana zama kusa da ita, tasa hannun hagun ta amshi Aliyu wanda Dr Aliyu sukayiwa mai suna.

Affan ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
“My Aunty ga iyalin nawa.
Ƙanwar Yusuf aboki nane yayar matarshi Zahra ce kuma.”

Cikin fara’a da son Mami tace.
“Ayyah yayi kyau Allah ya ƙara zaman lfy da zuriya mai Al’barka”.

Murmushi yayi tare da cewa.
“Amin tare daku, mu yanzu wannan na uku fa, ai munyi ƙoƙari ko Umaymah”.
Cikin dariya Hibba tace.
“Kai Ya Affan abinma ƙoƙari ne kenan”.
Dariya sukayi duka kana sukaci gaba da hira.
Aysha tana jin gamsuwa da gskyar Mami fiye data Aunty Juwairiyya.
Ranan dai anan Mami ta wuni.

Haka dai taci gaba da amfanin da ayatul shifa da zam-zam da ganyen magarya.

Cikin ikon Allah da izininshi.
Cikin kwanaki goma sha biyar hannun nan ya warke ya koma garau.
Har tana shiga kitchen ayi aiki da ita.

Hakane yasa Umaymah ta fara shirye-shiryen komawa tana mai jin sanyi kaɗan a ranta.

Yau kwananta ashirin da zuwa, kuma yaune zata koma.
To fa batun ƙomar da zatayi da Hibba ne yasa.
Aysha taji babu daɗi.

Allah yasani ta saba da Hibba sosai.
Ganin yadda ta koma ne yasa Umaymah ta ɗan zauna kusa da ita cikin lallami tace.
“Kiyi haƙuri Aysha kinga badon makarantar Hibba ba dana bar miki ita.
Yanzuma duk an gama mata komai na karatun zata tafi SS1 harma yan uwanta sun fara zuwa.

Kuma kema an kusa janye yajin aikin da University’s Suka tafi, nayiwa Jazlaan mgna ana komawa kena zaki koma kici gaba da karatunki kewan zai ragun miki.
Rafi’anki zata dawo itama”.
Cikin sanyi tace.
“To Umaymah ki bar mana ita mana, sai in gayawa Yah Sheykh ya sama mata wata makarantar a nan”.
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Abbansu bazai yarda ba Aysha”.
Cikin sanyi tace.
“Uhumm Allah sarki to shikenan Umaymah.
Amman wlh gidan zai mana babu daɗi ko Ummi”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Gsky kam Aysha zamuji kewar Hibba”.

Ita kuwa Hibba tana tsaye gefen Jalal ne.
Da alamu wani abun yake nuna mata a wayarshi.

Jamil kuwa murmushi yayi tare da cewa.
“Uhum in tayi tsami dai maji”.
Hararanshi Jalal yayi tare da cewa.
“Namu ƙamshi zaiyi ba tsamiba, ko Hibba”.
Murmushi ta ɗanyi tana share hawayenta, duk da rarrashinta da yakeyi kan kada tayi kuka.
Har yake nuna mata text message ɗin daya turawa Hamma Jabeer ɗin su cewa.
“Yana son Hibba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button