GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Kowa yasan Hibba na masifar son Ya Jalal ɗin.
Duk abinda yakeyi burgeta yakeyi.

Tun yana kaucewa har dai shima ya gane yana sonta ne.

Shi kuma Jamil sarkin latsi yaje can yace, i love You yaje can ya kuma cewa haka har yau bai tsaida matsaya ɗaya ba.
Kuma soyayya ta hanashi maida hankali kan aikinshi.

A hankali Aysha ta sunkuyar da kanta ganin hawayen Hibba na zuba.

Shi kuwa Sheykh Jabeer ido ya zuba mata.

Lokacin da taga Umaymah ta miƙe tace.
“To Ummin Jabeer Allah ya sadamu da al’khairi”.

Amin Amin Ummi tace cikin kewarta tun kafin ta tafi.

Hibba kuma ruggume Aysha tayi tare da cewa.
“Aunty Aysha zanyi kewarki sosai”.
Ta ƙarashe mgnar murya na rawa.
Tuni hawaye suka tsinkowa Aysha.
Aunty Juwairiyya ma sai ga hawaye.
cikin danne zuciya Umaymah tace.
“Ha Juwairiyya harda ke a kukan so kuke in tafi nima ina kukan ko”.

Kai Juwairiyya ta jujjuya.

Ya Jafar kuwa shiru yayi yana kallonsu.

Shi kuwa Sheykh idonshi ya maida kan tab ɗin shi dake hannunshi.

Aysha kuwa.
Cikin son danne kukanta tace.
“Nima haka Hibba zanyi rashinki sosai.
Sai yaushe zaki zo kuma”.

Cikin zubda hawaye tace.
“Aunty Aysha auren Ya Haroon ya kusa, ai zaki zo, bai cika wata biyu ya rage bama”.

Cikin sanyi tace.
“Allah ya kaimu”.

Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Suna fita Aysha ta koma ɗakinta.
Tana kuka.

Ummi da Aunty Juwairiyya da ya Jafar kuwa a falon suka zauna.

Sauran kuma duk yan rakiya ne sun fita.

Daga Side ɗinsa, sashin Hajia Mama taje ta sallameta kana ta wuce sashin Lamiɗo suma ta sallamesu sukayi mata fatan isa lfy kana ta tafi.

Ummi da Saratu suka shiga kitchen.
Ita kuwa Aunty Juwairiyya ta koma sashinta itama.

Koda suka dawo rakiyar bata fitoba.
Kasan cewar magriba tayi ne,
sukayi al-wala suka tafi masallacin.

Itama Ummi taje ɗakinta.

Ita kuwa Aysha yau tana hutun sallan.
Dan haka taci gaba da konciya.

Har akayi isha’i tana konce.

Koda suka dawo kai tsaye Side ɗinsa ya wuce.
Jim kaɗan ya fito yacewa Ummi.
“Bari inje Lamiɗo na nemana”.

“To sai ka dawo”.

To yace ya fita.

Ita kuwa Aysha, kiran da akayi mata a wayane yasa ta ɗanyi murmushi.
Muryar Junainah taji tana cewa.
“Adda na ya hannunki”.
Cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah ƙanwali ya worke yanzu kam ina Ummey na”.
Cikin jin daɗi tace.
“Gata nan”.
A hankali tace.
“Ummey na nayi kewarku, ina jina kamar bani da kowa nawa a duniya.
Gashi Hibba ma yau ta koma”.

Murmushi Ummey tayi tare da cewa.
“Ke kuwa kikeda kowa naki a duniya, gaki ga salihin mijinki da Al’amin ya dawo yana yaba mana kamalarsa kowa naki sun gamsu da zaɓin da Bappanki ya miƙi.
Gani ga Bappanki ga Abboi ga Ninnanki gasu ya Ahmad sannan ga dengin mijinki masu sonki
Gashi kuwa munji lbrin su Ya Gaini”.
Ta ƙareshe mgnar dan son kontar mata da hankali.
sabida basu wani ji lbrin su Gaini ba.
Cikin jin daɗi ta gyara konciyarta tare da share hawayenta.
“Alhamdulillah Ummey na godewa Allah. Ina suke?”.
Cikin sanyi tace.
“Suna wata rugar FULANI dake ƙasar Senegal, yanzu ana ƙoƙarin a tabbatar ki cire damuwa a ranki ki sasu a addu’a kinji ko”.
Cikin sanyi tace.
“To Ummey na ina sha Allah zan sasu.
Kuma zan roƙi Yan Sheykh ma ya samin su a addu’o’in shi”.

Cikin jin daɗi tace.
“Yauwa to yafi. Ga Bappanki”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Bappa na ina wuni”.

“Lfy lau Shatuna ya jikinki”.

“Alhamdulillah Bappa na worke”.

“Masha Allah, to Allah ya ƙara mana lfy”.

“Amin Amin tace.”

Kana sukayi saida safe.

Tana katse kiran Ummi dake zaune gefenta tace.
“Taso muje kici abinci kinji ko kije ki gayawa Sheykh damuwarki ya saki a addu’o’in shi.
Domin addu’ar miji ga matarsa bata da hijabi”.
Kanta ta gyaɗa cikin gamsuwa kana ta miƙe ta fito.

Kaɗan taci abincin. Sannan taje tayi wonka, tasa doguwar rigar bacci kana ta zurma hijabin ta.
Ta nufi falonshi.

Shi kuwa Sheykh lokacin ya dawo daga wurin a
Lamiɗo
Inda yake gaya mishi, akwai zagayen rangadin da zaiyi rugagen Fulanin ƙasar gaba ɗaya.

A cikin wata mai kamawa.

Koda ya dawo wonka ya shiga,
Ya fito ɗaure da towel a ƙirjinshi zuwa saman guiwarshi.

Mai ya shafa tare da fesa turare.
Kana yasa wani tattausan gajeren wonɗo mai ɗan faɗi amman ƙasamshi robar a tsuke take.
Yana riƙe da rigar bai saba.
Yaga kiran Umaymah ya shigo.

Wayar ya ɗaga bayan sun gaisa ne take ce mishi sun isa lfy.

A hankali ita kuma Aysha ta turo ƙafar bedroom ɗin ta shigo.

Ido ta zuba mishi sama da ƙasa a karo na forko kenan da ta ganshi babu riga a jikinsa.
Damatsan hannunshi ta zubawa ido zuwa kan ƙirjinshi da tattausan gargasa tsilli-tsilli ya mishi ƙawanya a farar fatarshi.

Shi kuwa ido ya zuba mata dan rabonta da shigowa ɗakinshi yafi kwana goma.

Umaymah kuwa cikin murmushi mai sauti tace.
“Ina ɗiyata, tanata kuka ko?”.

A hankali yace.
“Gata”.
Wani irin farin cikine ya rufe zuciyar Umaymah tasan burinsu bazai tabbataba muddin babu shaƙuwa da kusanci tsakanin Sheykh da matarsa.

Cikin jin daɗi tace.
“Bata wayar”.

Uhum yace kana ya miƙo mata wayar.
A hankali ta iso gabanshi kusa dashi gab-gab ta tsaya.
wayar ya miƙa mata yana kallon yadda take matsoshi.
Amsar wayar tayi ta kara a kunne tare da yin sallama.
Kana idonta kuma yana kan zanen macijiyar dake konce har kan cikinsa zuwa saman haƙar-ƙarinshi.

Da Ido yabi wurin da take kallon.
Fuskarshi ya haɗe tare da ɗaga ƙafarshi zai ja da baya.

Sai kuma ya tsaya cike da mamaki ya kalli hannunta da tasaka ta kamo bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Hannunshi yasa ya bugi hannunta,
Amman sai ta ƙara matsoshi.
Cikin sanyi ta….!

Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta number nan da nake whatsapp da ita, 09097853276 ba hoton katin zaki turoba, ba kuma TRANSFER ɗin katin zakiyi minba, ba kuma BTU ba, numbers ɗin katin zaki rubuto ki turomin. In kuwa special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min screenshort na shaidar biyanki ta wannan number tawa ta whatsapp 09097853276.
Kada kiyi min TRANSFER ko BTU na kati wlh in kinyi ba ruwana.

                      By
           *GARKUWAR FULANI*

Ta ƙara matsowa gabanshi.
A hankali tasa ƴar yatsarta ma nuniya dai-dai inda taga kan macijin.
Wurinda shi kuma yake masifar yimishi ƙaiƙayi.

Hannunta ɗayan kuma ta maidashi ta riƙe bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Ido ya zuba mata, cike da mamaki da kaɗuwa, da al’ajabi to me hakan me zatayi.

A hankali ta fara bin zanen kan macijiyar tana danna yatsarta, tanayi ƙasa da yatsar.
Wani irin yam-yam haka tsikar jikinshi ke tashi tana zubawa wani irin abu yakeji yana zir-zir-zirrrrr cikin jikinshi gaba ɗaya, abune da bai taɓa jin makamancinsa ba a rayuwarsa.

Cikin wani irin masifeffen da kasala daya diro mishi ya buɗi bakinshi a hankali yace.
“M.. me h hakan.”.

Manna kanta tayi da ƙirjinshi ta kife kunnenta dai-dai kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa da sauri-sauri dib-dib dib-dib.

Cikin wata muryar data ganar dashi,
ba ita bace, bata haiyacinta mutanenta ne a kusa tace.
“Kayi shiru da Allah”.

Kanshi ya sunkuyar a hankali.
Idonta a lumshe hawaye na zuba.
Cikin raunin muryar tace.
“Wurin yanayi maka ƙaiƙayi wasu lokutan ne?”.

“Uhummmmmm”. shine abinda kawai ya iya furtawa.

Ita kuwa ƙara shigewa jikinshi tayi.
tare da cewa.
“To kayi wa kanka jinyar wurin mana.
wannan zanen yana daga kan babbar yatsarka har zuwa nan.
Yana bin jikinka, kayi ma kanka aikin irin wanda kayi wa Aysha a ciwon hannunta.
Kana sha kana shafawa a wurin.
Zai bar jikinka zai ɓace duka.
Yanzu dai baya ci gaba da tafiya,
tunda Aysha ta tone aikin”.
A hankali yace.
“Yau kuma zuwa kika sakeyi kenan? Bazaki bar jikinta ba kenan kike nufi? Sai ki biyota har ɗakina dan baki da tsoron Allah”.
A hankali tace.
“Inada tsoron Allah wlh nima musulmace Kamarku.
Kafurun iska ko mugu bazai taɓa iya ratso cikin sashin kaba.
Sabida ka wadata wurin da ambaton Allah.
Ko yaushe madadin kallace- kallacen tv na banza da wofi karatun al’ƙur’ani kake sawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button