GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Duk sashin gidanka majigine na ƙura’an.
Ni ba muguwar iska bace.
Bana sata faɗuwa, ko kuka bare ihu.
Bana samata koda ciwon kai.
Ina kuma kareta ne ga wasu ababen cutarwa
wasu lokutan idonta kan iya ganin abinda ba kowa ke ganiba. Wanda wannan baiwar tace tun tana ƴar ƙaramarta”

Cikin dakekkiyar murya yace.
“Ki bar jikinta bana so.
Kina sata yin abinda in tana haiyacinta ba yinshi zatayi ba.”

Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Shike nan na tafi, amman in buƙatar zuwana yayi zaka gane nazo.
abinda ma babu wanda ya taɓa gane ina jikinta sai kai daga nayi mgn sai ka gane.
Zan tafi, amman tanada buƙatar daya kawota wurinka.
Zata roƙekasa yayunta a addu’o’in kane.
sabida sun ɓata tsawon lokaci har yau babu lbrinsu.”
Cikin haɗe fuskarshi yace.
“Na sani ai, ba sai kin gaya minba, Ni nan nasan komai a kan matata, nasan abinda ya faru da yayunta jeki kawai”.

Atishawa tayi a hankali.
Sai gashi ta narke a jikinshi tayi lib ido a lumshe alamun tayi bacci.

A hankali ya gyara tsayuwarshi.
Tallabeta yayi da kyau.
Hannunshi yasa ya cire hijabin jikinta.

A ranshi yake mgna.
“Na fahimta kenan iyayenta ma, basuma san tanada wata iska a jikinta ba.
Shiyasa basu sanarba kafin a ɗaura auren”.
Ido ya lumshe yana goge wannan ayar tambayar da ya bugawa Bappa cikin ƙoƙolwarshi na ya aurar da yarshi ba tare daya sanar musu tanada al’matsutsaiba kamar yadda shariya tace.

A hankali ya zauna bakin gadon da ita.

Yana nazartan abubuwa da dama.

Ya fara fahimtar wasu ababen a kanta musamman da yake Junaidu ya labarta mishi komai abinda ya sani a kan Shatu da Ba’ana lokacin da suke asibitinshi Valli.
konciya yayi a gefen daya kwantar da ita.

Kana yasa hannunshi ya kashe wutan ɗakin.

Ido ya lumshe ba tare da yayi baccinba.

Ita kuwa Aysha a hankali ta farka daga baccin, ido ta ɗan buɗe.
tabbas kam tasan tazo ɗakin shi kuma tasan ta ganshi babu riga daga nan kuma bata kuma sanin meke wakana ba.
cikin sanyi take juya kwayar idonta.
A hankali ta kalleshi yana konce yayi rigingine, cikin sanyin murya alamun baccin tace.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh!”.
A hankali ya ɗan juya kwayar idonshi ya kalleta.
cikin sanyi yasa hannunshi ya jawota jikinshi.
Kan ƙirjinshi ya kwantar da ita.
Yana mai jin wani irin baƙon yanayi yana game dukkanin sasan jikinsa gaba ɗaya.

Shiru tayi jikinta na wani irin sassanyan tsuma can ciki-ciki.

Cikin sanyi tace.
“Zan kwanta”.

Cikin sanyi murya can ƙasa yace.
“Yanzu a tsaye kike ai”.

Ya bata amsa a daƙile, shirun ta kumayi.
Shi kuwa gyara kwanciyar tasu yayi.
Tare da jawo blanket ya rufesu.
kana ya fara Addu’o’in yanayi yana tofawa a tafin hannunshi yana shafawa a fuskarta da sassan jikinta.
Idanunta ta lumshe yanaji sanyin tattausar fatar hannunshi.
A haka sukayi bacci, ɗaki ɗaya gado ɗaya borgo ɗaya pillow ɗaya a liƙe a jikin juna.
Karo na forko kenan da wannan kusancin ya samu tsakaninsu.

Washe gari kuwa.
Lamiɗo ya ƙara neman Sheykh akan batun tafiyar da dole zaiyita.
Shi kam yace zai tura wasu.
Dan yana son zuwa aikin haji,
Amman fir tsohon nan yaƙi.
Ya haɗashi da Abbanshi dole ya haƙura.

Washe gari da safe.
Mami matar Affan tazo, ita da Zahra’n Hamma Yusuf.
Bayan sun gaisane tace.
“Ga ƙanwata Zahra matar Yusuf”.
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
“Ayyah ai kuna kama fa”.
Da sauri Mami tace.
“A a na fita kyau duk gidanmu itace mummunar mu fa”.

Dariya Zahra tayi tare da cewa.
“A daba”.

Nan Aunty Juwairiyya ta shigo sukaci gaba da hira,
Ummi da Saratu suna kitchen.

To haka dai mafi akasarin lokuta Mami kanzo susha hira.

Tofa nan kewar ke ɗan raguwar mata, wani lokacin kuma ta kira Bappa susha hira ko ta kira Rafi’a ko Junaidu taji lbrin Rugar Bani.

Yau sallan layya saura sati biyu.
Kuma gobene Sheykh zai fita.
dole kuma tafiyar da motace bazai yiwu ta jirgiba.
Tunda rugogin manyan Arɗaɓe zai ziyarta wanda cikin dazuka suke.

Yana zaune a falon Lamiɗo shida Abbanshi da Galadima.
“Ka gama shiryawa ko Muhammad?”.
Abba ya tambayeshi cikin kula.
Kanshi ya ɗan gyaɗa tare da cewa.
“Eh”.
Lamiɗo ne ya ɗan shafi kan shi tare da cewa.
“Itama iyalin taka ta gama kimtsawa ko?”.
Da sauri ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
“Ta kimtsa taje ina ɗin?”.
Abba ne ya bashi amsa cikin bada umarni yace.
“Ta kimtsa ku tafi tare, dole tare zakuje”.
A hankali yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
“Dan Allah Abba tafiyar da nima ba sonta nakeyi ba, a kuma sake haɗani da wani jidalin”.
Fuska a haɗe Abba yace.
“A bayanka akace ka goyeta ku tafi ne?”.
A hankali ya jujjuya kai.
Cikin yanke hukunci yace.
“To ku tafi tare Muhammad bana son musu a kan yarinyar nan duk abinda akace kayi dan Allah kayi tunda ba wanda ya saɓawa shariyar musulunci za’ace kayi ba.
Baka san abinda muke zaton samu ta sanadinta ba.
Muna ganin nasarori kan matsalarmu. Kaje da matarka kaji ko Muhammad na”.
A hankali yace.
“To Abba ba komai in dai zakayi farin cikin hakan zanje da itan”.

Kanshi ya shafa tare da cewa.
“Allah yayi maka al’barka”.
Amin Amin yace cikin jin daɗi.

Kana ya sallamesu ya fita.
A falo ya samu Ummi ita ɗaya tana kallon wata tashar da aka saka wa’azin shi.
Cikin sanyi yace.
“Ummi gani gaki sai kin kalleni a tv”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Ina ƙaruwa ne ai”.
Kanshi ya jinjina tare da ɗan kallon gefe da gefe kana yace.
“Ummi ina take?”.

Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
“Tana ɗakinta”.
Kanshi ya gyaɗa kana yace.
“To Ummi Lamiɗo yace wai dole da ita zamuyi tafiyar zaga rugar Arɗabe.
A gaya mata ta shirya gobe sammako zamuyi inga ko zamu gama cikin kwana huɗun”.
Cikin murmushin Ummi tace.
“To bari in gaya mata”.

To yace shi ya nufi sashinsa.
Ita kuma ta nufi ɗakinta.

A gaban mirror ta sameta tanayiwa kanta kitson kalba manya-manya.
“Kitso kikeyi ne?”.

Juyowa tayi tare da cewa.
“Har na gama ma!”.

“Kuma yayi kyau sosai fa”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Allah ko Ummi”.
Kai ta gyaɗa alamun eh.
Kana tace.
“Sheykh yace in gaya miki ki shirya gobe zaku tafi tare yawon ziyartan Arɗaɓen inda dama na gaya miki zaiyi tafi, duk an turawa Arɗaɓen saƙon zuwanshi ma”.
Cikin jin daɗi tace.
“Kai naji daɗi na, zan fita in zagaya inga makiyayan in huta da zaman wuri ɗaya”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Wato zakije kiga fulani yan uwanki ko”.

“Sosai ma kuwa Ummi yanzu tayani shiryawa”.
Ta faɗa tana buɗe drower’n.

Nan kuwa Ummi ta tayata ta kimtsa ababen buƙatar ta.

Sannan suka fito falon inda suka samu Jamil ya dawo aiki Jalal kuma dama yana sashin Hajia Mama ne.
Sai yanzu ya dawo nan ɗin nan suka zauna sukaci gaba da hira.

Washe gari da safe suka fito cikin shirin tafiyar.

Motoci guda bakwai ne uku a gaban ta Sheykh uku a bayan tashi.

Biyu na gaba fadawa sai ta ukun Jalal ne da wasu mutane su biyu.

Sai motar Sheykh shida Aysha suna baya Ado na jan motar.

Sai wacce take binsu Affan ne da Ya Hashim sai Sulaiman kana Laminu ɗan jaridar, da zai ɗauki komai.
Sai biyu kuma na baya kuma Galadima ne.
Sai fadawa da godarai sai hadimai mata biyu da zasuyiwa Aysha hidima.

Tafiya mai ɗan nisa sukayi.
Kana suka ratsa wata babbar hanyar birji, suka fara tafiya suna kutsawa cikin daji.

A ƙalla awa ɗaya suna tafiya.
Sunata wuce ƙananan rugagen Fulani makiyaya, da dabbobinsu.

Kasan cewar manyan motocine masu inganci yasa.
Basu jin wannan gargada ta buwayesu.

Jalal da abokanshi sunata hira, sosai Jamil yayi mamakin sakin fuskar Jalal cikin abokanshi.
Sannan sukanyi mgna da wani salo na musamman.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button