GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ɗan ɗagowa tayi ta kalleshi jin ya ruggumeta tsam a jikinshi tare da cewa.
“Ashe Allah ya rufa min asiri yamin gata”.
A hankali tace.
“Kamar yaya?”.
Cikin taɓe baki yace.
“Da basu cinye min hadiman Gimbiya Aminatu na data haɗomu dasu dan yi miki hidima ba”.

Uhum tace tare da yin mgnar zuci.
“Lallai ma Yah Sheykh watoma shi Hadiman gidansu ya jiwa tsoro ni Ko oho ko?”.

Sassauta riƙon da yayi mata yayi tare da cewa.
“Ina jinki Yah Aish sauran fa?”.

Kanta ta manna a damtsen hannunshi tare da cewa.
“Sai ƴan BBOKOLOJI sune zakaga shanayensu basu da ƙaho, ɗaɗɗaya zaka samu cikin shanayensu masu ƙaho, shima sai ka samu ƙahon ɗan ƙanƙanine kuma, in ka ɗan taɓashi sai kaji yana girgiza.
Kuma a haka sunfi shanaye masu ƙaho masifa da zafi.
Kuma duk cikin shanaye babu shanun daya kaisu ƙiba in an kiwatasu, makiyayan BOKOLOJI asalin fulanine kuma na ƙasar nan.
Su in suje gari, to sarakunan garin suke zuwa su samu, su biyasu kuɗi su saida musu dajukan manoma su.
Daga nan Duk gonar wanda suka samu sai su shiga su kiwata abunsu su fita.
In mai gona yayi mgna sai suce.
“Mufa sayan gonakinku mukayi sarkinku shiua saida mana”.
Cike da mamaki ya kalleta tare da cewa.
“Kenan ɓarnan da wasu ma kiyaye sukeyi dasa hannun sarakunan?”.
Kai ta jinjina tare dace mishi.
“Tabbas kuwa”.
Idonta ta ɗan zubawa hannunshi daya cusa ta tsakanin bayanta da kujerar motar.
Ya ruggume ƙugunta, hannun ya dawo har cikinta,
a hankali ta lumshi idonta jin yana cusa hannunshin cikin rigarta kasancewar yau riga da zanine a jikinta.

Sajenshi ya ɗan goga mata tare da cewa.
“Kalli nan baki gamaba ai su waye JOTTAN MA’EN?”.

Ɗan matsowa jikinshi tayi jin yadda ya cusa hannunshi ya zira yatsarshi cikin hudar cibiyar ta.
A hankali tace.
“Hhhhh washhh”.
Idonshi ya ɗan zuba mata kana yasa bakinshi saitin kunnenta a hankali yace.
“Yah dai Aish. Ci gaba mana”.
Wani irin masifeffen abu taji yana yawo a dukkanin jikinta, cikin sanyi kamar raɗa taci gaba da cewa.
“JOTTAN MA’EN sune, Fulani mazauna wuri ɗaya, a ƙalla su shekara ashirin ko talatin zuwa sama kuma su basa ƙaura to sune JOTTAN MA’EN kamar dai fulanin Rugar Bani”.

Shiru tayi jin yadda ya liƙa lips ɗinshi a kunnenta a hankali yace.
“Shhhhhhyyyy Yah Aishhhhhhhh. To kuma su waye TEMA’EN?”.

Murmushi tayi tare da cewa.
“Ku mana!”.

Da sauri yayi sama da hannunshi, Caɓɓullenta ya ɗan cafke tare da cewa.
“Mu kuma?”.

Hannunta dake cikin hannunshi ta fara ƙoƙarin ja,
dan janye hannunshi dake cikin rigarta.
Ƙara rumtse hannuntan yayi cikin nashi yanajin yadda Shey ɗinsa ke amsa amo da tsallen neman agaji.
Dan ma ya samu System ɗinshi ta danneshi ta hanashi harbawa yadda take son tona mishi asiri.

A hankali tace.
“Eh mana fulanin cikin birni.
Sune TEMA’EN dan in kunyi mgna kune kuke cewa Tema.
Ma’anar tema (wata ƙil) shine Tema.”

Kanshi ya sunkuyar Sosai

Yana sunsuna wuyanta, kallonshi tayi, shi kuwa a hankali yayi mata wani irin kallon dake nunida yana gab da fita haiyacinsa yace.
“To ke kuma wanne babin kike?”.

A hankali tace.
“Ni dai Aysha Aliyu Garkuwa Fulata marace. Da kuma JOTTAN MA’EN.”.

Cikin sanyi yace.
“Menene fulata mare”.

“Fulata mare shuwa Arab kenan, Babana su fulata marane, asalin fulanin tsatson Shuwa’arab ne.
Mamata kuwa JOTTAN MA’EN ne, Wuitin’en.”

Kanta ya manna kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa.
Shiru tayi tanajin yadda sautin bugawar keyi.

A hankali yace.
“Ngd da wannan bayani Shatu Bororiyar daji mai tallan nono da kiwo”.

Cikin jin daɗi tace.
“Asalina kenan tushena bana ɓoyeshi.
Ina al’faharin kasancewata bafulatanar daji makiyayiya yar Fulani makiyaya kuma manoma”.

Idonshi ɗaya ya lumshe tare da buɗe mata ɗayan.

Ita kuwa a hankali.
Bacci ya fara surarta sabida jin yana hura mata sassanyar iskar bakinshi.

Da sauri yace.
“Kada kiyi bacci Tashi muyi salla, sai mu wuce.”

Buɗe idonta tayi a hankali, kana suka fito.
Su suka shiga wani gida dake kan hanya sukayi salla.
Su kuma maza suka shiga Masallacin.

Bayan sun idar sun fitone.
Sukaci gaba da tafiya.

Baifi awa ukuba su isaba aka kira sallan magriba.
A wani ɗan kekyawan ƙauye suka tsaya sukayi sallan magriba da isha’i.
Kana suka shiga Mota sukaci gaba da tafiya.

Kasan cewar dare yayi kuma ga garin hadari ya ɗauro
Haka yasa cikin motocin yin duhu.

A hankali ya jawota jikinshi da kyau.

Ruggume ta yayi gam a jikinshi.

Lafewar tayi a jikinshi dan ba abinda takeson yi sama da bacci.
Dan taci gaseshen naman da Affan ya saya mata.
Tayi haniƙan tasha Dudunta mai sanyi.

Tayi salla ga gajiya ga kuma.
Bacci.

Numfashin gajiya taja a hankali tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi.

A haka tayi baccinta kana sukaci gaba da tafiya.

Ƙarfe goma da rabi tayi musu cikin masarautar Joɗa.

A hankali aka nufi bakin part ɗin kowa.

Har bakin mashigar hawa barandar falonshi motar ta ajiyesu.
Ya sani Ummi bata nan tana sashin Gimbiya Aminatu shi yasa.

Yace.
“Alhamdulillah Ado fita jeka kawai, saida safe kazo ka ɗauke motar a nan”.
Cikin girmamawa Ado yace.
“To”.
Daga nan ya fita ya juya ya tafi.

Shi kuwa a hankali ya ɗan ɗagota tare da cewa.
“Aish tashi mun isa gida”.
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
“Yah Sheykh Na gaji”.
Buɗe marfin motar yayi kana ya fito.
Tallabe da ita.
a bakin ƙofar falon ya direta, kana ya kalli inda Ummi ke ajiye mishi key ya ɗauka.
Buɗe wa yayi ya shiga, riƙe da hannunta.

Binshi kawai takeyi idonta, a lumshe alamun tana baccinta.

Shiru Side ɗin. Sai dai komai yana share yana goge ko ina fes-fes sai ƙamshi yakeyi.

Side ɗinsa ya wuce da ita.
Tana dai biye dashi kamar yar yaye.

Har cikin Bedroom ya wuce da ita.
Tana ƙoƙarin konciya kan gado, ya jawota suka nufi Bathroom.

Har cikin wurin wonkan ya shiga da ita.

Kamar daga sama kamar mafarki taji sauƙan ruwan sanyi a jikinta.
Wani irin zaro ido tayi tare da firgici tace.
“Innalillahi”.
Sai kuma ta kalleshi ya karkata kai ya tsura mata kyawawan idonshi.

Cikin tsiwa tace.
“Nifa bazanyi wonkaba”.

Juyawa yayi ya fita tare da cewa.
“Ashe kuwa yau a ciki zaki kwana”.
Yana fita ya maids marfin ya rufe.

Da sauri tasa hannu ta rufe ruwan sanyin.
Kana ta buɗe na ɗamin.

Dole ta cire wannan kayan ta saƙalasu gefe.
Kana tayi wonka fes.
Sannan ta fito a zatonta yabar cikin bathroom ɗin bata san yana cikiba.
Ta fito ɗaure da ɗankalinta daga gugunta zuwa guiwarta ta fito da niyar ta ɗauka towel.
Tana fitowa ta ganshi tsaye a gefen wurin da al’kyabbar jikinshi yana brush.

Da sauri ta juya.
Shi kuwa bayanta yabi.
Ya kamota buɗa al’kyabbar shi yayi gaba ɗaya kana ya haɗa da ita ya rufe kirif tare da cewa.
“Ina zaki je?”.

“Zan ɗauko zaninane in ɓoye jikina”.

Ɗan taɓe baki yayi tare da cewa.
“Meme za’a gani a nan?.”

Ya ƙareshe mgnar da ware al’kyabbar, da sauri tasa tafin hannunta ta tare ƙirjinta.
Juyawa bayanta yayi ya cire al’kyabbar tashi.
Kana ya zura mata a jikinta tare da rufeta kirib yace.
“To jeki kwanta”.

Da sauri ta ware hannayenta ta sasu cikin hannun al’kyabbar kana ta haɗa bakinshi ta riƙe ta juyo ta fito.
Kan gadonshi ta hau ta shiga borgon ba tare da ta cire al’kyabbar ba.

Shi kuma wonka yayi kana ya shirya cikin kayan baccinsa.
Sannan ya fito.
Yanata zuba ƙamshi.

Ita kuwa cikin ɗan baccin data farajin yana fizgarta ta ɗan buɗe idonta a hankali ta kalleshi sai kuma ta maidasu ta lumshe.

Wutan ɗakin ya kashe kana yazo ya zauna gefen gadon.
Hannunshi yasa ya lalubo wata yar mitsitsiyar waya dake kan Bedside drower’n dake gefenshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button