GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Tana kokarin fitowa falo Rafi’a na ƙoƙarin shigowa da sauri Rafi’a ta zaro ido tare da cewa.
“Yaushe kika dawo?”.
Hararanta ta ɗanyi tare da cewa.
“Ba dai kin gudo kin dawo kin barni ni ɗaya ba”.
Cikin tausayawa Rafi’a tace.
“La wlh yanzu nake ƙoƙarin komawa, na dawone in ɗan dafa mana abinda zamuci in mun dawo, sabida naga rabonki da abinci tun jiya, shiyasa kina shiga Office ɗin Dr na dawo”.
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace.
“Na dawo a guje fa, wannan Sheykh ɗin hannunsa zafi kamar allurar mashi yakewa mutun”.
Zaro ido na mamaki Rafi’a tayi tare da cewa.
“Shida kanshi ya miki?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh”.
Cikin taɓe baki tace.
“Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke”.
Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Aysha tace.
“Ba doleba yadda yake tura ruwan alluranshi nan kamar mai tura mai a mota, kuma ina dawowa nasha mgni, sannan abin ya iso, kinsan dama wuyar kafin ya isone”.
Dariya Rafi’a tayi tare da cewa.
“Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai”.
Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira.

Cikin hirar tasu ne Rafi’a tace.
“Anjima da yammafa jirginmu zai tashi”.
Da sauri Aysha tace.
“Haba dai Rafi’a dan Allah ki bar zuwa hutunnan mana ki bari mu zauna, wallahi in kin tafi nima dole in tafi kuma ke kin san matsalar da nake da ita a gida ko Mamey ma da mukayi waya dazu cemin tayi kar in koma hutu Rugarmu, in zauna a makaranta”.
Cikin sanyi Rafi’a tace,
“Wallahi nayi kewar gidane Aysha, shekara guda kenan banje gidaba fa”.
Cikin sanyi Aysha tace.
“Haka ne kam ba, matsala, ai hutun sati ukune, kina tafiya yau nima gobe zan shirya zan koma Rugarmu”.
a haka sukaci gaba da hira suna cin abinci.

Ƙarfe huɗu dai-dai na yamma jirginsu Rafi’a ya tashi daga Ɓadamaya international airport, zuwa Farazan state.

Ita kuwa Aysha taci gaba da shirinta ba tare da ta gaya mutanen gida cewa zata dawo ba.
Kaya kaɗan ta ɗiba dan tanada kaya a gida, system ɗinta da wayarta da kuma kaya kala biyu kawai ta ɗauka, sai yan ƙananun abubuwan, ta da tayi nufin sai gobe zata koma.
Amman ina tafiyar Rafi’a yasa taji bazata iya zaman kaɗaicinba, dan haka huɗu da rabi, ɗaya daga cikin motocin dake maida ɗalibanda in gidajensu na kusane ya ɗauke ta.

Kai tsaye garin Shikan suka nufa.
Tafiyar ba wata mai nisa bace daga cikin birnin Joɗa zuwa Shikan, cikin mitina kaɗan suka isa,
Ƙarfe biyara da miti biyar suka isa.
Cikin Shikan a nan tasa drever ya tsaya ta sayi Junainah sweet.

Biyar da mintuna goma dai-dai suka isa kwanar mashigar Rukarsu Rugar Bani.

Cikin tsoron kada Ba’ana yaga wani yazo ya sauketa ya masa rashin mutunci, tace.
Ya sauketa a nan ba musu ya sauketa dan ai inda sabo ya saba.

Tana fita taja jakarta, ta rataya kana ta gyara tarhan da tayiwa kanta.
Shi kuma ya juya ya tafi.

A hankali ta zubawa yankin garin nasu ido, ko ina yayi kore shar, yabanya da ni’imar damina ta wadaci ko ina, wata iriyar sassanyar iska mai daɗin ke ratsa mata jiki da zuciya.

Ajiyan zuciya ta sauƙe a hankali tare da lumshe idanunta kana ta buɗe hannayenta cikin begen gida tace.
“Rayuwar ƙauye mu akwai daɗeeee”.
Ido ta buɗe tana kallon tako ina makiyayen rugarsune suketa dawowa daga kiwo,
Dabbobi saffan-saffan sunata dawowa,
garin yayi lum ga wani hadari mai ƙarfi daya keto, daga ƙasan dutsen da yayiwa Kyauyen ko ince Rugar Bani ƙawanya, a hankali take taku tana bin kan faffaɗan hanyan da makiyayan sukayishi bi ma’ana burtali kenan.

Taku take yayinda gefen hagunta wutsiyar kogin Shikan ne konce iya ganinta,
gefen dama kuwa Garden ɗinsune mai girma wanda yasa sanyin wurin yake yawaita, sauri ta ɗan farayi sabida akwai ƴar tazara kana kuma gashi magriba ta karato.

Tana cikin tafiya tana rataye da jakarta, kamar daga sama taga wulgawar inuwan mutun, cikin sauri ta zaro idonta ta kalli gefen hagu da damanta,
Ba kowa ganin hakane yasa taci gaba da tafiyarta cikin dakiya, taku uku tayi ana huɗu taji ansa hannu an amshi jakarta, da sauri ta juyo ta kalli gefen da aka amshi jakar.
Babu kowa a wurin kuma ga jakarta a rataye ita ɗaya tana binta suna tafiya a jere.
Cikin wani irin fargaba tsaro kaɗuwa da tsananin firgita ta….!

                           By
               *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

  ????️????????????????????????????

             *GARKUWA*

                     PAGE 6

                                   NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

   ????????????️????????????????????????????

             *FREE PAGE*

Kada dai ku manta har yanzu Free page kuke samu, wanda zamu datseshi cikin ko wanne lokacin, hamzarta ku biya darinki uku kacal ko 1k ga mai dama da niya, domin samun cikekken labarin daki-daki cikin salama. Turo kuɗin ta asusuna na Jaiz. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidan biyanki ta layina 09097853276. In ya zama larura ba halin turawa ta ac turo katin mtn na ɗari uku, ko na 1k ɗin domin ci gaban lbrin GARKUWA. Sayan na gari maida kuɗi gida. Ina mai yi muku fatan al’khairi masoyana makaranta, ina sonku domin Allah ina fatan kyautata alaƙa ta da kowa sabida nasan ko ina raye watarana zan zama tarihi a duniyar marubuta, sabida yauda gobe ta wuce watsa, in ba mutuwa akwai tsufa. Kana dole watan wata rana gwanayen zasu zama tsoffin hannu kana yan koyo na yanzu su zama gwanayen, domin da babu yan koyo tabbas da gwanayen sun ƙare, inada fata da burin ganin al’ƙaluman Adabi sun inƙanta baki ɗayansu ba nawa kaɗaiba, tsarkake rubutu ki/ka domin kece madubin wata marubuciya da zata iya tasowa nan gaba.Ina mai muku fatan al’khairi????????????????????????makaranta da marubuta

Cikin firgita da tsoron tace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani’imanwakil, lailaha’illalahu Muhammadurasulillahi sallahu’alaihi wasallam Auzubikalimatillahi ta’ammati min sharrin ma khalaƙa Allahum…”.
Da sauri ta koma da baya ba tare da karisa addu’ar ƙarshen data faro ɗinba. Ganin Ba’ana ne tsaye a gabanta cikin wata iriyar dariya yace.
“Ke ki nitsu masoyinki ne ke gadinki, gsky Mata dole in rage miki wannan tsoron, domin matar Ba’ana bazata kasance matsoraciya ba, dole in ƙara tsumaki in dafaki da kyau, ta yadda idanunki zasu buɗe da kyau”.
Cikin karkarwar da bai bar jikintaba tace.
“Bana so. Ni ka barnin da tsorona, nifa macece ba namiji irinka ba, kaine ke shiga daji da tsaunuka kake buƙatar wani abu ya kare ka”.
Da sauri Ba’ana farin kekyawan babarbare ya matso gareta cikin shigar fulanin da ya zame mushi sutura yace.
“Mata ke bakya buƙatar kariyar ne?.”
Da sauri ta gyaɗa mishi kai tare da cewa.
“Ni na yarda cewa addu’a’u saiful muminin ne, kuma shi na riƙe, so bana buƙatar waɗannan asirce asircen”.
Murmushi yayi tare da murza ƙafarshi ta hagu sai gashi ya zama kamar inuwa ba mutun ya ɓacewa ganinta ɓat.
Da sauri ta rufe idanunta tare da cewa.
“Bana so ina tsoro ka dena caccanza kamanni a gabana”.
Da sauri tayi baya ganinshi gab da ita,
Dariyar ƙeta yayi tare da cewa.
“Baga irinta nanba, idonki baya iya ganin komai, dole zan ƙara haɗaki irin haɗin da zaki ke banbance mai layar ɓata data zana da jingina bongo da dama duk mutun mai juyewa i zuwa wata halittar”.
Ya karishe mgnar yana nuna mata hanya alamun su tafi.
A hankali suka jera suna tafiya a tare.

Allah ya sani Ba’ana yana masifar son Shatu tun tana ƴar ƙaramar yarinya, yana sonto irin sonda ko ƙudane in ya sauƙa kanta in dai namiji ne to zai kasheshi, ganinta kusa dashi kawai yana sashi jin daɗi, duk muguntarsa baya yi mata, duk duniya babu wanda Ba’ana ya yarda da shi bare yasan sirrin makarin sihirurrukan dake jikinshi. Ba’ana mutunne da yake tamkar al’janu sabida yawan ta’ammali da sihiri kai harma da tsafi, Ba’ana riƙeƙƙen tantirin ɓarawone wanda ya buwayi Fulani al’ummar Afirka gaba ɗayanta, da sace-sacen dabbobinshi, muddin ya ƙella ido yaga garken shanunka yayi mishi, to tazarar kilo mita talatin da biyar yake tsayuwa da garken, yayi FITO ɗaya tak, wallahi duk sihirin kafiyar garkenka zai kunce kuma duk inda yayi shanayenka zasu bishi a baya da kuma wannan tazarar, da zaran kasa Hukuma cikin zancen kuma yana burza layar ɓatanshi dashi da dabbobin duk zasu ɓace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button