GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Miƙewa yayi tare da cewa.
“Meke miki ciwo?”.
A hankali itama ta miƙa tare da cewa.
“Ya bari”.
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“To muje kiyi min tausa bayana ciwo”.

Ya ƙarashe mgnar yana kamo hannunta suka nufi bedroom.

Da goran zam-zam a hannunshi.
Bedside drower’n ya buɗe.
wasu magunguna ya fitar, ya ɓalli guda biyu a ciki ya miƙa mata.
amsa tayi,
“Sha wannan sauran na wancan wotan ne”. Yace mata.
sashi a baki tayi shi kuma ya miƙo mata goran zam-zam ɗin ta sha ta haɗiye mgnin.

Gariyar jikinshi ya zare ya saƙala cikin durowa, kana ya cire rigarma ya saƙala.
Hakama dogon Wondon da hularshi.

Hannunta yaja suka hau kan gadon.
A nitse yace.
“Ɗan daddanna min bayan”.
Ya kwanta a kife.
Shiru tayi sabida rawan da jikinta keyi.

Juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Umarnine fa ba shawaraba”.

A hankali tace.
“Yah Sheykh cikina marata ciwofa”.
Jawota jikinshi ya kontar da ita, kana ya juyata rigingine.
Hannunshi yasa kan cikinta.
A hankali ya ture rigarta sama kaɗan.
kana yayi ƙasa da siket ɗin.

A hankali yake shafa mararta-ta yanayi yana ɗan lallatse wurin da danneshi.
Shiru tayi sabida tanajin daɗin yadda yake matan.
A hankali ya ɗan manna bakinshi kan goshinta.
Kiss ya manna mata tare da cewa.
“Na sani ai baki da lfy, ɓoye min kikeyi. Sannu”.
Kanta ta gyaɗa tare da lumshe ido.
Cikin sanyi tayi bacci tare dasa hannunta kan sajenshi lokacin data juyo ta konta a rigingine.

Gyara musu kwanciyar yayi.
Lokacin ɗaya sukayi baccinsu.

Ummi kuwa da Saratu cikin sauƙin suka gama aikin hajji.
Jannama sai gobe.
Bayan sun gama suyan ne, Ummi ta dama musu kunun shinkafa kyau.
tasa manyan flaks.

Sannan ta koma ɗakinta itama ta ɗan kwanta.

A can jihar Tsinako kuwa, sosai fa shirye-shirye bikin Haroon da Jannart ya kankama.
Tuni an haɗa kayan lefe a saura kaiwa kuma sai bikin yazo a kai.
Haroon ya shiga ribibi.
Yau tunda gari ya waye baiyi waya da Jabeer da Ibrahim ba, sai yakeji kamar shekara yayi baiyi mgna da suba.
Kiran Sheykh ya farayi sai kuma ya tuno, yanzu duk inda yake lokacin baccinsa ne, in kuma baiyi baccinba to yana babban uzurin da bazai barshi ya ɗaga wayar Bama.

Umaymah kuwa tunda safe tayi mgn da AYSHA data kirata tayi mata barka da salla.

Ibrahim ma ya kira Jabeer ba’a ɗagaba.
Wayar Aysha kuwa Rafi’a da sauran ƙawayensu duk sun kikkira.
Bappa ya kirata.
Hakama Junaidun da Binto budurwar ya Gaini.

Sannan ƴan uwanta ahlin Abboi duk sun kirata.
Wani Ummi ta amsa wani ta bari.

Kiran salla ne ya tadashi a bacci.
A hankali ya zare jikinshi daga nata.
Ya shiga bathroom yayi al’wala kana ya fita sukaje sukayi salla.

Ƙarfe huɗu dai-dai ya kuma dawowa.
Dasu Jalal a falon suka zauna wurin Ummi suna cin soyayyan naman.

Shi kuwa cikin ɗakin nashi ya wuce.
Har yanzu tana bacci.

Wayarshi ya ɗauka Haroon ya fara kira, sukayi hira kana ya kira Ibrahim.

Yana cikin mgna dasune yaga ta tashi da sauri.

Sauƙowa tayi tana kallon jikinta, dasa hannun ta shafa bayanta dai-dai mazaunanta.

juyowa tayi cikin tsarguwa irin ta macen da takejin alamun jikinta ya ɓaci.

Ta gefen ido ya kalleta ganin ta juya zata nufi hanyar fita.
Da yatsarshi ya nuna mata jikin sawunta, da jini ke ɗan gangarowa.
A hankali alamun yanzu ya samu tsinkowa yadda yakeso.
Dan tun lokacin data shiga yin wonkan idi taga zubowanshi kaɗan sai kuma yanzu.

Ganin ta tsaya ne ya sashi kwaɓe fuskarshi tare da nuna mata hanyar bathroom nashi yana cewa.
“Kiyi sauri ki shiga kada ki samin najasa a tsarkakken ɗakina”.
Hannu tasa ta tattare bakin siket ɗin kana ta nufi ban ɗakin.

Tana shiga ta ɗan leƙo tare da cewa.
“Ayyah Yah Sheykh dan Allah a kawo min zani mana”.
Shiru yayi itama shiru tayi tana leƙenshi.
da alamu abu yake rubutawa a wayarshi.
Saida ya gama har ta buɗe baki zatayi mgna.
Sai taga ya miƙe ya fita.

Bai kula su Jamil da Affan ba ya wuce.

Yana buɗe durowar, ya shaƙi ƙamshin sabbin kayayyakin dake jere.
Wata doguwar rigar material Sky blue ya ɗauko da ɗan kwalinta, ganin akwai rasin fari a jikine yasashi ɗaukar mata farin gyale.
Har ya rufe zai juya sai kuma ya dawo.
sunkuyowa ya ɗanyi. Inda yaga jerin bra and panties ɗauka mata yayi fara.
Sai kuma yaga audugar mata a gefe.
Kwaya ɗaya ya zaro kana ya juya ya fita.

A kan gado ya ajiyesu.
Kana ya juya ya fita ya koma falo bai ce mata komaiba.

Sake leƙowan da tayine bayan tayi wonka, taga ya ajiye mata kaya kuma ya juya ya tafi.

Da sauri ta fito da towel ɗin shi a jikinta.

Sauri-sauri ta kimtsa jikinta,
ta shirya tsab, sabida taji sauƙin marar tata sosai.

Bathroom ɗin ta koma ta wonke wanda ta ciren ta shanyasu a cikin, kana ta fito.
Gaban dreesing mirror ta tsaya, turaren shi ta fesa, kana ta juya ta fito.

Hanyar fita ta nufa, shi kuwa yana tsaye ta sameshi da alamun wani wurin ya nufa, har taje bakin ƙofa yace.
“Zo”.
Ɗan juyowa tayi ta kalleshi ganin kamar bashine yayi mgnarba, yasa ta juya ta nufi hanyar fita.
“Zo”. Ya kuma cewa.
A hankali ta juyo, ta nufi inda yake gabanshi ta ɗan tsaya.

Kanta a sunkuye.
“Waya baki izinin samin turarena?”.
Da sauri ta ɗan kalleshi tare da girgiza kai alalum a a.
Fuskar shi ya tsuke tare da cewa.
“Ƙarya nayi miki kenan”.
Still kanta ta jujjuya, shi kuwa kallonta yayi sama da ƙasa ya kalli iya tsawonta da ɗan jikinta da wuraren da sukafi abki a jikinta welcome and bay-bay ɗinta.
“Baki da turaren ne?”.

“Inada shi”.

“To meyasa kika samin nawa”.

Baki ta ɗan zumbura tare da cewa.
“Nifa bansa maka tutarenka ba”.
Tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar fita.

Da ido ya rakata, tana fita shi kuma ya buɗe ƙofar da zata sadashi da Garden ɗin da ke bayan sashin nasa.

Washe gari kuma ranar suyan jan nama, sosai Aysha ta tsaya kan aikin, dan cikinta yabar ciwon nanda nan sukayi aikinsu suka gama.

Haka dai akayi shagulgula bikin ƙaramar salla lafiya.

Yau kwana huɗu da yin salla a wuni na biyar ne.

Affan da Aunty Juwairiyya kusan a tare suka shigo.

Wani roba mai kyau Affan ya miƙa Aysha tare da cewa.
“Aunty ƙarama gashi inji, Mami a kawo miki”.
Murmushi tayi tare da amsar robar.
Soyayyan namane yayi kyau ya samu kekyawan aiki sai nason mai yakeyu.
“Kai a lallai nako gode sosai”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Wai tasan naku duk muke haɗuwa muna cinyewa, wai kowa ya bar na gidansa yazo ya cinye naku”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Tayi gsky ai haka kuke gaku bakwa gajiya da cin nama kamar ba Fulani ba.
Gwara ma Jalal shi bai fiye damuwa da namaba amman Kai Affan Jamil Imran da Sulaiman ko kuraye sai haka”.
Murmushi sukayi.
Kana Aunty Juwairiyya ma ta miƙo mata robar da tazo dashi tare da cewa.
“Gashi wannan a bawa Sheykh”.
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
“A a barshi kawai”.

Shiru Ummi tayi dan tasan za’ayi hakan.
Ta rasa dalilin da yasa Aysha batason kyautar komin na wurin Juwairiyya da Hajia Mama.
Su kuma basa gajiya da ba amsa takeyin ba sai sun bata.
Cikin tsareta da ido Juwairiyya tace.
“To aini ba ke na bawaba Sheykh nace a bawa”.
Fuska a daƙile tace.
“Bazan bashi ba, bazai ciba.
Kije kici abunki. Baya buƙatar nakin”.
Da mamaki Affan yace.
“To Aunty ƙarama meyasa”.
Juyowa tayi ta ɗan kalli Affan tare da cewa.
“Ita ai tasan dalili”.
Daga nan ta juya ta nufi ɗakinta.
Sosai Affan yayi mamaki.
Ita Juwairiyya kuwa, ciki takaici tace.
“Uhumm lallai ma yarinyar nan, bansan me take nufi da niba, ban san me nayi mata ba, shiyasa yanzu ni bana ko son shigowa nan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button