Su kuwa dogaran suka fara bin motar a hankali, har ta gama juya kanta, ta dai-dai-ta.
Sannan suka fara sauri yadda tafiyarsu zaiyi dai-dai dana motar dake tafiya a hankali.
A haka suka fito asalin farfajiyar kowa da kowa.
Nan Ummi da Jamil suke cikin motar da aka ware musu.
Kana Baba Wambai Wanda yake Aminin Abban su Jabeer ne ƙut da ƙut, shida Malam Liman suka shiga motarsu.
Suma dogaran suka shiga tasu motar,
haka suka jera motoci biyar tasu Sheykh ce a tsakiya, ta fadawa a gaba sai tasu Jamil sannan tasu, sai ta malam Liman sai kuma ta dogarai can baya.
A haka suka nufi masarautar Tsinako. Cikin mota da Sheykh da Aysha suke kuwa, waya Aysha keyi bisa alama da wata ƴar uwarta ce.
sabida yaga tarin farin ciki a fuskarta.
A hankali ta ɗan juyo ta kalleshi lokacin da Junainah tace.
“Adda Shatu ina mijin naki baki taɓa bashi waya mun gaisa ba, ko bakice mishi kinada ƙanwaba?”.
Da sauri ta ɗan janye idonta tare da cewa.
“Gashi nan, na gaya mishi mana”.
Da sauri Junainah tace.
“Ayyah Addana dan Allah bashi wayar.”
Juyowa ta kumayi ta kalleshi cikin raɗa dayin ƙasa da murya tace.
“Junainah shi miskiline, yayi fuskar bosawa, baya dariya baya son mutane, kada ki damu dashi badai gani kina gaisawa da yar uwarki ba, mai ruwanki da wani can bare”.
Da sauri ta juyo ta kalleshi, jin yasa hannunshi ya zare wayar a kunnenta.
Ido ta zuba mishi ganin ya manna wayar a kunnenshi.
Ita kuwa Junainah baki ta tura tare da cewa.
“A a Adda Shatu, shina ɗan uwanane, tunda yana tare dake yar uwata. Kuma ma Bappa yacemin da baki da lfy shi yake miki mgnin har kika samu lfy, Ni dai ko yayi fuskar bosawa bashi mu gaisa ina dai ba dukana zaiyiba”.
Wani irin bugawa da ƙarfi zuciyarshi tayi jin sautin amon Muryar yarinyar tamkar sautin amon da bazai taɓa mancewa a duniya ba.
hakane yasa yayi shiru yana jin muryarta na dukan dodon kunnenshi da zuciyarshi, jin tayi shirune ya sashi yin sassauƙan numfashin tare da cewa.
“Ƙarya takeyi miki Baby sherri take min.
Ni Bana fuskar bosawa, kuma ina son mutane sabida Allah da kanshi yace.
“Walaƙat karram’na bani Adam.
Toni waye da zanƙi mutane, bazan dakekiba kinji ko”.
Ya ƙarishe mgnar yana kallonta tare da tsuke fuskarsa ya ƙanƙance idanunsa ya tsura mata su cikin nata, yana mai son ganin iya tsaurin idonta.
Ita kuwa Aysha da sauri ta janye ƙwayar idanunta Allah ya sani batayi zato ko tsammanin zaiji abinda ta faɗa cikin raɗaba.
Towai shi wanne irin kunnene dashi a rayuwarsa.
Junainah kuwa cikin jin daɗi tace.
“Yauwa Ina kwana Hamma”.
Ido ya lumshe tare da cewa.
“Lfy Baby me sunanki”.
Da sauri tace.
“Junainah, wani lokacin Adda Shatu na cemin Junnu ko tace min ƙanwaliya ko tace min Baby Ummey’nmu kuma tace min Mamana ko tace min auta”.
baisan sanda wani murmushi ya subce mushiba.
Lokacin ɗaya yaji son yarinyar a ranshi.
cikin nitsuwa yace.
“Toni kuma da wanne sunan zan kiraki?”.
Da sauri ta kuma cewa.
“Junainah dan Bappa na yace in dena bari ana ɓata min sunan.
Hamma kai me sunanka, yaushe zaka kawo mana Addana”.
Juyowa yayi ya kalli gefenshi ganin sun isa cikin masarautarsu Haroon.
A nitse Suka nufi Side ɗin Umaymah.
dasu a cikin motar.
Shi kuwa Sheykh Jabeer gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“To Junainah, Sunana Muhammad Jabeer, yanzu munyi tafiya sai mun dawo zan roƙi Bappa a kawo mana ke mu zauna ko”.
Cikin jin daɗi tace.
“To Hamma Jabeer Allah ya dawo daku lfy, bari in meyarwa Bappa na wayarshi kar ya dawo ya sameni.”
Kafinma yace wani abun ta katse kiran.
Dai-dai lokacin kuma motar su ta isa bakin farfajiyar shiga Big Part ɗin Umaymah, parking akayi.
hakama motar Ummi da Jamil.
bin wayar yayi da ido yanajin wani abu na musamman a zuciyarshi.
Ita kuwa Aysha da sauri tasa hannun ta, zata buɗe marfin motar ganin Umaymah, Hibba, Aunty Hafsat da wasu ƴan mata da samari ƴan saffan-saffa kyawawa masu suffar larabawa sun fito daga wata babbar ƙofar suna tako wani babban steps masu faɗi dake jikin barandar wurin.
Zura wayar yayi cikin al’jihunsa.
A hankali yasa hannunshin ya kamo nata, jawota yayi kusa dashi tare da ɗan juyawa ya fuskanceta da kyau fuskarshi ya haɗe tare da cewa.
“Nine mai fuskar bosawa ko? Ina zaune a gabana kikemin sherri da ƙazafi. Nine bana son mutane ko wato bana dariya”.
Bakinta ta turo ta cinnnashi sama.
Idonshi ya tsurawa tattausan red lips ɗinta masu masifar taushi sai sheƙi sukeyi.
mui-mui tayi da bakin alamun zatayi tsiwar Tata.
Cikin murza bakin tace.
“To kanayin dariyar ne? Ban taɓa ganin k..!”
wani irin zaro ido tayi da ƙarfi cike da bugawar zuciya.
Lokacin data buɗa lips ɗin ta tare da rabasu biyu zata furta kalmar K.
Da sauri ya lumshe idonshi tare da kusanto da fuskarshi kan tata manne gishinsu wuri ɗaya,
tattausan lip ɗinshi na na sama yasa cikin bakin ta, tare da kamo lip ɗinta na ƙasa, yasa cikin bakinshi ya zama nashi na sama yana cikin bakinta.
Da sauri yasa tafin hannunshi ya tallabo ƙeyarta da kyau.
Wani irin gigitaccen rugguma yayi mata.
cikin rawan jiki ya c…!
Littafina GARKUWA na kuɗine
By
*GARKUWAR FULANI*
Idonshi ya lumshe jin fatar idanun sun mishi nauyi.
Wani irin abu yakeji yana yawo a dukka cikin jininshi yana zaga jikinshi, manne lips ɗinshi da nata yayi, suka haɗe tamkar mayen ƙarfe.
Hanunshi yasa ya ƙara tallabe kanta da kyau.
Ita kuwa Aysha wani irin tsuma jikinta keyi tare da miƙewar tsikar jikinta, a lokaci ɗaya taji wani irin masifeffen mamaki, tsoro, kaɗuwa, domin abun yazo mata a baka-ta-tam ba zato ba tsammanin hakan daga gareshi domin bai taɓa gwada yin hakanba koda a kamace ne.
Jin yadda yayiwa lip ɗin ta wani irin lasa da kuma tsotseshi tamkar ya samu tom-tom ne yasata.
Yin yunƙuri da kiciniyar ƙwace kanta.
Ronƙofawa yayi kanta da kyau jin zata kawo mishi wargi.
Nauyin ƙirjinshi ya sakar mata ya danne nata ƙirjin da ƙirjinshi, kana ya buɗa al’kyabbar shi, ya rufesu ruf, wani irin numfarfashi yake fesarwa da sauƙewa a jere-a-jere.
Cib tayi jin yadda ya mata ƙawanya da jikinshi kana ya sakar mata nauyinshi da yimata garkuwa da al’kyabbar jikinshi.
Buɗe idonta tayi ta zubasu kan kyakkyawan fuskarshi, da take yalwace da.
Hasken addini, ta ƙawatu da kyawun sura da hali da nagartacen haiba da imani.
Gashin girarsa ta zubawa ido,
tana kallo tare da sajenshi.
a hankali ta shaƙi ƙamshin turaren OudKareem dake tashi a jikinsa.
meda idonta tayi ta lumshe da sauri ganin Umaymah ta iso har gaban motar kusa da ƙofarsu.
Mutsu-mutsu ta farayi.
Sam ta kasa zillewa.
Hakane yasa ta ɗago hannayenta, tasa bisa fuskarshi ta tallabe gefen hagu da damanshi ya zama tafin hannunta na kan sajenshi duka biyu.
A hankali ya buɗe kyawawan idanunshi ya zubasu cikin nata.
Da sauri ta janye nata, kanshi ya fara janyewa still dai yana liƙe da lip ɗinta kan harshensa.
da sauri ta turo kanta jin kamar zai tsinke mata shi.
Ɗouhh haka ya saki mata wani sauti mai kashe jiki da zuciya cikin kunnenta lokacin daya saki laɓɓan nata.
Da sauri tasa tafin hannunta tana fifita lips ɗin tare dayin rau-rau da ido tace.
“Zafi! zafi!! Zafeeeh!!!.” Hannunshi yasa ya kama tsinin hancinta da yatsu biyu kana ya ƙanƙance idanunsa, cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.
“In kika sake murguɗa min bakin, haka zan miki. In kuma kika sake yimin sherri ko ƙazafi tsinke bakin zanyi”.
cikin kwaɓe fuska tana fifita laɓɓan tace.
“Ka tsinke min baki kamar maye”.
Kafaɗunshi ya buɗa tare da ɗagasu sama ya taɓe baki kana yace.
“Mayen ne ai ni. In na tsinkasu haɗiyesu zanyi sai kije in sa miki na Aku kinji daɗin yin surutu da kyau”.
Ya ƙareshe mgnar yana janye al’kyabbarshi daga jikinta yana gyara shi.
Hannunshi yasa ya jawo niƙabinta daya ɗage ya rufe fuskarta tare da cewa.
“Ki rufe fuskarki kar Hibba tayi miki dariya tace kin zama mai dogon baki dengin jaɓa”.
Yana faɗin haka yasa hannunshi ya buɗe marfin motar tare da saƙo ƙafarshi ta dama waje.
Wani irin murmushi mai cike da tarin.
So, ƙauna, shaƙuwa, tausayi, da kulawa. Umaymah tayi mishi.
Hakama Aunty Hafsat.