GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Aysha bakin ta ɗan tura tare da cewa.
“Allah ko sai na gayawa Umaymah ka cinye min lips ɗin a”.

Juyowa yayi yana kallonta, tare da murmushi a fuskarshi.
Sai kuma ya juyo da sauri jin Umaymah da Aunty Hafsat su ruggumeshi ta baya.
Hannunshi ya miƙo mata tare da cewa.
“To fito ki faɗa kada in rigaki yin nawa sharhin”.
Ture hannunshi tayi ta fito.
Shi kuwa tana fitowa yasa hannunshi ya kamo nata tare da jawota bayanshi.
Da sauri Aunty Hafsat ta sakeshi tare da komawa bayanshi hannunta ta jawo tare da Ruggumeta tana cewa.
“Masha Allah diyar kirki”.
Da sauri tasa hannunta ta yaye niƙabin.

Umaymah kuwa murmushi tayi cikin tsananin jin daɗin ganinsu take kallonsu cike da so da kulawa tare da cewa.
“Jazlaan naji daɗin ganinku”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Muma haka”.
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Haroon da Ibrahim da suka fito can gaban motar bisa alamu duk Ibrahim ne yaja motar.
Haroon kuwa yana gefen mai zaman banza.
Cikin dariyar tsiya Haroon ya matsoshi tare da ruggumeshi ta gefe, dan su Umaymah duk sun sakeshi sun koma kan Aysha.
Cikin tsiya yace.
“Ur welcome Mr Jabeer Ustazu ƙalilan iya shege kasiran”.
wani irin tsare fuska da gira Sheykh yayi tare da watsa Haroon kallon. “Hegen munafurcin sa ido”.
Ya faɗa tare da Ruggume Haroon da ƙarfi yadda zaiji zafi.
Da sauri Haroon yasa ƴar ƙara tare da cewa.
“Wayyo Aunty Hafsat zai karyan baya in rasa na amarci”.
Dariya sukayi dukansu.

Shi kuwa Sheykh ture Haroon yayi yana mamakin subutar baki irin na Haroon, kwaffa yayi tare da Ruggume Ibrahim murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
“Barka da zuwa Garkuwan Masarautar Joɗa”.
Shima murmushi yayi tare da cewa.
“Barka da zuwa, magajin masarautar Leddi julɓe”.

Hibba kuwa baki ta tura tare da cewa.
“Aunty Aysha wato kinga su Umaymah ni Ko ki kulani ko?”.
Da sauri ta juyo ta ruggume Hibba tare da cewa.
“Oh sorry my Hibba ai ke ta dabance”.

Da sauri ta juyo ganin wata kekyawar budurwa kamar Hibba ta gane Azeema ce yar Aunty Hafsat.
cikin bagwariyar Hausa Azeema tace.
“Wato mu bana musamman bane ko Aunty”.
Da sauri ta jawo hannun Azeema ta haɗa su ta ruggume.

Da sauri Umaymah ta juyo ganin Ummi ta fito.
Ruggume juna sukayi cikin jin daɗin ganin junasu sun kasa mgn sai murmushi.
Jamil kuwa da sauri yaje ya Ruggume Abudul-azeez da Sadiq ta baya.
Juyowa sukayi suma suka ruggumeshi suna farin cikin ganin juna.

Sheykh kuwa sake Ibrahim yayi ya kalli Sadiq da Abdul-azeez ya shafa kan ƴan matasan.

Umaymah ce ta juya ta nufi cikin gidan tare da cewa.
“Ku shigo, maza ku taho ko”.
To sukace kana duk sukabi bayanta.

Wani babban falo mai zaman kanshi wanda yake ɗauke da lumtsuma-luntsuman kujeru set biyu da Dinning table a can babban Dinning area da ƙaton fili a tsakiyar falon.
Suka zauna.
Su Hibba da Azeema sun sa Aysha a gaba.

Haroon da Ibrahim dasu Sadiq kuwa suna ɗaya sashin.

Umaymah da Aunty Hafsat da kansu suka rinƙa kawo musu abubuwan ci da sha.

Bayan sun gaggaisa ne.

Suka ɗan zauna suna hirar Yaushe gamo.

Ummi ce ta ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
“Ina Rahma ne ban ganta ba ita”.
Aunty Hafsat ce ta amshi zancen da cewa.
“Tab uhum Rahma taji biki ta zauna.
Ɗazu da safe jirginsu ya wuce.
Leddi julɓe, kinsan gobene za’ayi kamu, to taje ita da su Isha dasu Farida, sun haɗu dasu Juwairiyya sunacan suna shiryawa hidindimun da za’ayi”.
Ɗan juyowa sukayi suka kalli Azeema da ke cewa Sheykh.
“Hamma Jabeer zamuje da Aunty Ayshan can ko gobe in Allah ya kaimu”.
Ba tare da ya ɗago kanshi bare ya kalletaba ya ɗan jujjuya kanshi alamun.
A a, da sauri Azeema tace.
“Ayyah dai”.
Umaymah ce ta ɗaga mata hannu alamun tayi shiru.
Ummi da Aunty Hafsat kuwa murmushi kawai sukayi.
Hibba kuwa ƙasa tayi da muryarta tare da cewa Aysha.
“Zamuje ai”.
Kai Aysha ta gyaɗa mata alamun eh.

Haroon kuwa juyowa yayi ya kalli Sheykh tare da cewa.
“Yaushe kace zamu tsaida lokacin walimar?”.

Kanshi na sunkuye yana kallon wayarshi yace.
“Na gama mgn da Abba, babu wani Dinner’n da za’ayi.
Madadin dinan shi zamuyi waliman”.
Da sauri Haroon yace.
“Wannan ai tatsuniya ce”.
Ibrahim ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
“Wlh sun gama mgn da Abba, yace tunima ya gaiyaci manyan mutane duk akan walima za’ayi.
An gama shirya komai ma, kuma babban wurine aka kama gefen, maza da matane, za’ayi walima mai kyau da ma’ana.
Yafi akan yin wannan bidi’ar nan da zamuje mu gwamutsu maza da mata a wuri ɗaya a rinƙa kiɗe-kiɗen da bushe-bushen da raye-rayen banza da wofi”.
Murmushi Umaymah tayi ganin yadda Haroon ya haɗe fuska kamar zaiyi kuka cikin takaici yace.
“To Ni yau ma zan tafi dan inje mu shiryawa kamun da kyau, duk sauran abokanmu zasu je”.
Ya faɗa yana kallon Sheykh, kafaɗarshi ya ɗaga tare da buɗawa kana yace.
“Ya rage naka, Ni nan Muhammad babu inda zanje walimace da ɗaurin aure ya kawoni. Dan dole in jamaka kunne kasan tsarin zaman aure a musulunci ba a yahudance ba”.
Dariya sukayi sosai.
Aunty Hafsat ce ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
“In anyi bikin a can, kana in mun dawo nan anyi walima, washe gari ayi fansan ido da daren ranar Lahadi da dare zamuyi mother’s day, dan ranar tamuce kuma biki biyune, tunda bamu samu zuwa na Jazlaan ba.
Anyishi babu bikin komai to in sha Allah mu dai iyaye zamuyi namu shagalin wannan umarnine ba shawara ba, bakuma neman iziniba”.
Ido Sheykh ya zuba mata cikin sanyi yace.
“Mom”.
Hannu ta ɗaga mishi, alamar yayi shiru.
Sai ta kuma juyo ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummin Jabeer kunzo da shiri ko?”.
Cikin murmushin Ummi tace.
“Sosai ma kuwa”.
Nan dai sukayi hirarsu da tsara yadda abin zai kasance.

Hibba ce taja hannun Aysha, ɗakin Umaymah Suka shiga.
Suna shiga tayi wani irin tsayuwa tana kallon tsarin ɗakin yayi masifar kyau.
Wasu ƴan mata da manyan mata suka samu a zaune.
Cikin murmushin Hibba tace.
“Aunty Rabi’atu ga matar Hamma Jabeer Aunty Aysha da nake faɗa miki”.
Da sauri duk suka juyo.
Masha Allah shine abinda suka faɗa kusan a tare.
Ɗan rusunar da kai tayi ta gaidasu.
Murmushi tayi ganin Aunty. Kubra ƙawar Umaymah dake Ɓadamaya.
Motsowa tayi kusa da ita ganin tana miƙo mata hannu cikin kunya tace.
“Aunty Kubra Ina wuni. yaushe kika zo”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah Aysha.
Ni tun jiya nazo, ina ɗan nawa yana lfy ko?”.
Murmushi tayi a kunyace tace.
“Alhamdulillah yana falo”.
Nuna mata sauran matan tayi tare da cewa.
“Kinga nan duk ƙawayen Umaymah ne yawanci daga wasu garuruwan sukazo.
Kin san Umaymah taku ta jama’ace”.
Sannu ta sake yi musu.

Ita kuwa Aunty Kubra miƙewa tayi tare da kamo, hannun Aysha.
“Zo nan”. Tace tare suka fita Hibba na biye dasu a baya.
Juyowa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
“Jeki kira min Hafsat kice ina ɗakin can”.
Da sauri Hibba tace to, kana ta juya taje falo.
Ta kira Aunty Hafsat kamar yadda Aunty Kubra ta umarceta.

Tare suka juya suka tafi.

Haroon da Ibrahim da Sheykh kuwa miƙewa sukayi suka nufi wanni babban part dake bayan na Umaymah wanda yake da yalwan ɗakuna babban falo sai 3 bedroom sai ƙaramin falo.
Nan suka nufa, wanda akwai wani a gefenshi kuma nanne Haroon zai tare da Amaryarshi Jannart.

Suna shiga suka samu abokansu.

Hunnu sukayi ta bawa juna suna gaisawa cike da fara’a sukeyiwa Sheykh tsiyar yayi auren sirri wato dan baya son suje susha rawa ko.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Mazarai sarakunan rawa yanzu ai kun samu wurin rawan ko?”.
Dariya sukayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button