
Dariya dai sukayi ita kam Aysha.
Ta shiga ruɗani kamannin.
Ƴarinyar da aka kira da Ishma da Junainah sun bata mamaki, sai kuma ga kamannin da yafi bata tsoro ma yanzu kam ko murya da dariyar Ummey nata irin na Aunty Rahma ne.
Ya ilahi ya mujibadda’awati”.
Ta faɗa cikin ranta.
Lokacin da Ishma ta taso zaune daga baccin da takeyi, har kamar zata faɗi.
Da sauri tasa hannu ta tare yar yarinyar da bazata gaza shekara biyar ba.
Da sauri ƴarinyar ta manna kanta a jikinta tare da cewa.
“Mommy zansha ruwa”.
Da sauri ta sunkuyo kan yarinyar hannunta tasa ta dafa goshinta, cikin sanyi tace.
“To ga ruwan buɗe baki”. Ta ƙareshe mgnar tare da ɗaukan bottle water mai ɗan sanyi dai-dai misali, tana buɗe marfinshi.
Juyowa Ishma tayi jin baƙuwar murya.
Cikin sauri ta kalli Azeema tare da cewa.
“Laa Aunty Azeema kalli Aunty Ayshan Hamma Jabeer tazo”.
Tayi mgnar da alamun tasan Aysha a hoto.
Murmushi tayi tare da sa mata bakin gorar ruwan a baki.
Cikin mussuke ido ta buɗe baki ta fara shan ruwan.
Aunty Rahma kuwa, kallon Aysha take cike da ƙauna.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Aysha cikin yanayin da bazaka gane manufarshi ba tace.
“Sannuku da zuwa yau kam gaki a masarautarmu tushenmu, gaki ga Sitti kakarmu data haifi babana ta kuma haifi Mamansu Sheykh da Ya Jafar dasu Jamil jininmu ɗaya”.
Ta ƙareshe mgnar cikin nuna kusanci da dangatakar dasu Sheykh na jinine.
Kai Aysha ta ɗan juyo ta kalleta,
murmushin gefen baki tayi,
dan ta gane manufar Aunty Juwairiyya tana nuna mata cewa su jini ɗaya ne, itace bare a tsakaninsu.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh yau kam gani ga Sitti ga Aunty Rahma”.
Ta ƙareshe mgnar tana wata mgnar a zuciyarta.
“Uhumm Aunty Juwairiyya kenan, ai dama saida ɗan gari akanci gari da yaƙi, kina matsayin yar uwarsu kuma kike cutar dasu, in da zasu sani da bazasu aminta da keba”.
Muryar Ishma ce ta katse mata mgnar zuci da takeyi.
“Aunty Aysha ina Hamma Jabeer”.
Kanta ta ɗan shafa tare da cewa.
“Yana Tsinako”.
Da sauri tace.
“To shi bazai zo bane?”.
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
“Zai zo”.
“Yaushe?”. Ta kuma tambayarta a gajarce.
murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
“In Sha Allah gobe zasu zo”.
Allah ya kaimu ta tafaɗa tana wasa da jelan gashin Aysha dake bisa kafaɗarta.
Aunty Rahma ce ta ɗan harareta tare da cewa.
“Maza tashi a jikinta ki barta ta huta”.
da sauri ta ɗan zame ta sauƙa ita kuwa.
Aysha kai ta ɗan karya tare da cewa.
“Aunty Rahma barta”.
Safiyya ce tace.
“Ahyya baki san Ishma bane da shegen surutu da son jiki”.
dariya sukayi ganin yadda Ishma ta zumbura baki.
Sitti ce ta miƙe tsaye tare da kallon jikokin nata da yar autar tata, tace.
“Toh maza ku tashi muyi sallan azahar, in mun idar ku isa wurin Jadda ku gaisa.”
Kusan a tare suka mimmiƙe, Aunty Rahma ce ta kamo hannun Ishma tare da cewa.
“Jadda ya fita, ai ɗazu ya kirani yace in masa abincin dare, wai ya ɗan fita zai kai dare kafin ya dawo”.
Dariya Sitti tayi tare da cewa.
“Uhumm kai Jadda wato ki masa abincin dare. In kun koma kuwa naga wa zai ce ta dafa mishi”.
Safiyya ce tace.
“Oh zai ci girgikin yar autarsa”.
Ita dai Ramatu murmushi tayi tare da cewa.
Aysha Juwairiyya Jazrah Safiyya mu tafi ɗakina”.
To sukace kana suka bita a baya.
Har zasu fitane Sitti tace.
“A a Aysha dawo nan, ke kam baƙuwa tace ga masauƙinki”.
Murmushi Aysha tayi kana ta juyo ta dawo sabida tafi gamsuwa da zama kusa da Sitti akan a tsakiyar Juwairiyya da Jazrah dake mata wani irin mayataccen kallo.
Haka dai sukayi sallan azahar,
kana suka fara shirin kamu.
Wanda tuni ango Haroon da tawagar abokanshi sun iso.
Anayin Sallan la’asar suka fara.
Sai gab da magriba suka tashi.
Ranar kusan kwanan zaunen sukayi anata hirar yan uwantaka.
Yayinda Aysha bata gajiya da jin muryar Aunty Ramatu da kallon fuskarta da fuskar Ishma.
Basu samu sun isa wurin Jadda ba.
Sun bari a akan sai gobe da safe in Allah ya kai rai.
A can Tsinako kuwa, gaba ɗaya al’ummar masarautar Tsinako da baƙi abokan Abbansu Haroon dana kakansu Sarki.
Da kuma baƙi na nesa dana kusa duk an kwana cikin shirin, tafiya ɗaurin auren.
Masu tafiya a jirgi ƙarfe tara jirginsu zai tashi.
Masu tafiya a motoci kuma sammako zasuyi.
Sabida sha ɗaya na safe za’a ɗaura auren.
Haka kuwa akayi washe gari da safe masarautar Jalaluddin, ta fara amsar baƙi tako wani saƙo na ƙasar Nigeria.
Fadar masarautar dama farfajiyar ta cika tayi tab da baƙi da ƴan gari, tako ina halarta mutane keyi.
Karfe sha ɗaya dai-dai na safe taron al’ummar musulmi suka shaida ɗaurin auren Haroon da Jannart.
Bayan an ɗan wawwatse mutane duk sun kama hanyar komawa inda suka fito.
Sai Abokan ango da zasu ɗauki ƙawayen Amarya da wasu yan uwa.
Dan amarya dasu Aunty Juwairiyya da Jazrah da Aunty Rahma Ishma da ƙannen mamansu Jannart duk sun tafi a jirgi, da ango.
Safiyyah da Aysha da Azeema da Hibba ne kaɗai suka rage.
Dan Safiyyah ce ta hana Aysha tafiya dasu Auntyr Rahma tace, ita tare zasu tafi.
Haka kuma Sitti ma tace haka yasa koda suke ribibin tafiya ita tana bacci a ɗakin Sitti bisa gadon mulkinta, dan kwanan da sukayi ba bacci yasa duk suna cike da bacci.
Ibrahim da Sheykh kuwa sune suka tsaya da wasu abokan Haroon biyu, sai sunga duk mai buƙatar zuwa ta tafi.
Ƙarfe sha biyu dai-dai Sheykh Jabeer da Ibrahim da Munnir da Mansur abokan Haroon Suka shigo babban falon Sitti.
A nan suka samu Jalal da ya Jafar da Ammar ƙanin Aunty Juwairiyya da Ibrahim wanda shine yayan Jannart.
Sai kuma Goggo Mairo ƙanwar Jadda da kuma sauran yaran Jadda wanda kishiyoyin Sitti suka haifa.
Safiyyah na ganin shigowarsu ta miƙe ta nufi Dinning area fridge ta buɗe ta haɗo musu ya’yan itatuwa masu sanyi, ta gyara kana ta kawo musu.
Bayan sun gaggaisa ne,
Ibrahim ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Kun gama shiryawa ko?”.
Kai ta gyaɗa mishi al’amar eh.
Sai ta kuma kalli Sheykh dake miƙawa Ya Jafar nonon inabi yana kuma ce mata.
“Sitti fa?”.
jujjuya kai tayi cikin falon ta kalli gabas da yamma kudu da arewa.
Gane wai neman inda Sitti takene yasa Goggo Mairo cewa.
“Bata nan ai ta fita”.
ɗan miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
“Ikon Allah kuma fa da muna nan tare da ita. To ina tayi”.
Aunty Salima wacce take itace Babba a yaran Jadda ne tace.
“Nima fa ita nake jira”.
Jalal ne ya ɗan kurɓi ruwan sanyi tare da cewa.
“To ko tayi ciki ne”.
“Ba mamaki”. Goggo Mairo tace.
Cikin nitsuwa Sheykh ya miƙe tsaye, kekyawar al’kyabbar jikinshi ya ɗan buɗa tare da gyara zamanta jikinshi.
Corridor’n da zai sadashi da special Side ɗin Sitti ya nufa, a nitse.
A can bedroom ɗin Sitti kuwa.
Aysha ce tsaye gaban dreesing mirror bayan ta gama ado da kolliyar ta.
Wani dandatsetsen Shadda lace ne mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi ne a jikinta, ɗinkin Doguwar rigace.
Ta zauna ɗas a jikinta gwanin burgewa da ban sha’awa.
Kalan kayan sun taimaka kwarai wurin burgewa, dark red wine mai masifar kyau, sai ratsin zare Royal blue mai azabar kyau da sheƙi da aka zubashi suffar zanen ɗawisu.
Turare ta feshe jikinta dashi,
kana ta maida kolbar sannan ta dawo gaban dreesing mirror kujerar ta jawo ta zauna.
Kasan cewar dreesing mirror babbane mai tudu hakama kujerar.
hannu tasa ta fara tsaɓule ribon ɗin da ta tubke himilin gashinta dashi.
A nitse ya iso bakin ƙofar Bedroom ɗin Sitti.
hannunshi yasa ya tura ƙofar,
ɗan wani guntun tsaki yaja tare da sa guiwar yatsunshi biyu ya ɗan ƙonƙosa kofar sau uku.
Kana ya ɗan tsaya gefe.