GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Safiyyah kuwa bacci nema ya saceta a motar.

A ƙalla tafiyar awa ɗaya sukayi, kana suka fita jiharsu Jadda suka fara tafiya cikin dajin jiharsu Haroon.

A hankali ya buɗe idonshi.
Jin Ibrahim na cewa.
“Tab lallai Abban Haroon da Sarki Ahmadu suna ji da wannan walimar da za’ayi.
Kajifa duk gidajen rediyon Tsinako, gaiyatar walimar akeyi ba ƙaƙƙautawa kaji ko zasu sakeyi.”

Meda kunnuwansu sukayi kan abinda ake faɗin.
“A madadin iyalan mai girma sarki Ahmadu suna farin cikin gaiyatar walimar auren. jikokinkin mai Martaba Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗo da matarsa Aysha Aliyu Garkuwa.
Da kuma Haroon Abubakar Ahmadu. Da amaryarsa.
Jannart Umar Jalaluddin
Za’ayi walimar ne a wurin babban filin taron al’ummar musulmi na Tsinako, ana gaiyatar ɗaukacin al’ummar musulmai wurin walimar wanda za’ayi yau misalin ƙarfe takwas na dare zuwa goma da izinin ubangiji, in da sanan malamin nan Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda shima angone kuma shi zaiyi nasiha ga mauratan.
Saƙon gayyata daga Mai martaba Sarkin Ahmadu. Allah ya bada ikon zuwa Amin…”.

Gajeren tsaki Sheykh ya ɗan ja tare da cewa.
“Kai tsoffin nan fa sunada matsala, ji wani dogon sharhi iya sunayemmu ya ishi a gunduri mai sauraro”.

Murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
“Kuma wlh tallatar tayi armashi.”
“Sosai ma kuwa”. Safiyyah tace, cikin jin daɗi.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
“Tsaya nan garin muyi salla la’asar tana gab da wucewa”.
To Ibrahim yace, kana sukaci ga da tafiya.
Tafiya kaɗan sukayi suka isa.
Wani masallaci mai kyau wanda dama dan matafiya akayishi.
Gefen mata da ban gefen maza da ban.

Bayan duk sunyi parking ne fadawan, suka fara fitowa.
Da sauri sukazo suka buɗe musu mota.
Ibrahim ne ya fara fita kana Safiyyah.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta ganin ta gyara zamanta ta kishin giɗa tare da lumshe idanunta.
fuska ya ɗan yamutsa kana yace.
“Fitowa zakiyi muje muyi salla. Ba gyara zama zakiyi ba.”
Shiru batayi mgna ba, haka yasashi haɗe fuska ya kuma maimaita mgnar.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
“Ni nayi”.
Idonshi ya zubawa fuskarta na daƙiƙu biyar.
Uhummm yace kana ya sa ƙafarshi ya fita.

Bayan sunyi sallan ne kana suka dawo sukaci gaba da tafiya.

Ƙarfe biyar dai-dai suna cikin masarautarsu Haroon.

Suna shiga fadawan suka wuce masauƙinsu dan sai gobe zasu koma.
Su kuwa Sheykh da Ibrahim Side ɗin Abban Haroon Suka nufa sabida kiransu da yayi a woya.

Aysha da Safiyyah kuwa Side ɗin Umaymah suka wuce.
Suna Shiga Hibba tace.
“O oyoyo My Aunty’s Umaymah gasu Aunty Aysha sun iso”.
Da sauri Umaymah da Aunty Hafsat da Rahma suka fito.
Cikin kula Umaymah tace.
“Allah sarki Ɗiyata sukayi muku wayo suka dawo a jirgi ku suka barku da gajiyar mota ko”.
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tace.
“Ina wuni Umaymah Aunty Hafsat barka da yamma”.
Murmushi sukayi suka amsa cike da kulawa.
Aunty Rahma ce tace.
“Yaseen kuwa Umaymah ba wayo mukayi musuba Ibrahim ne yace mu barsu zasu dawo tare tun randa mukaje hutasa bayi shirin dawowa dasu a jirgiba”.
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Juwairiyya da Jazrah da suka shigo yanzu.
“A Safiyyah sai yanzu kuka iso”.
Jazrah ta faɗa tana ƙin kallon inda Aysha take.

“Eh ba kun musu wayo ba”.
Aunty Hafsat ta faɗa.

Murmushi suka ɗan yi.
Cikin kula Umaymah tace.
“To Safiyyah yanzu dai kuje ku ɗan huta, kafin ku fara shirin zuwa walimar.”
To tace kana suka nufi ɗakin Hibba dan yau Side ɗin Umaymah cike yake maƙil da taron al’ummar Annabi.

Suna shiga Aysha ta wuce Bathroom da hand bang nata a hannunta.
Meda ƙofar tayi ta rufe tare da sauƙe ajiyan zuciya.
Dan tana son kimtsa jikinta sabida larurarmu ta mata da take tare da ita.
Allah yasa ma ita in tana fashin salla bata yawan fitsari.
A wuni bazai fi sau biyu zata zagaba, dan fitsari sai dan ko kimtsa jikinta, shima kuma baya mata wawan zuba, a bisa tsari yake zubo mata sai dai tana yawan bacci in bata salla.

Wonka tayi kana ta kimtsa jikinta da kyau, kana ta fito ba kowa a ɗakin sai ɗan Safiyyah dake bacci.
Akwatinta ta buɗe ta zaro wata doguwar riga mara nauyi ta zura.

Tana rufe akwatin Hibba da Aunty Rahma Suka shigo da Foodflaks a hannunsu.
Ishma biye dasu da plate and spoons.

A tsakiyar ɗakin suka ajiyesu bisa carpet.

“My surka ina Safiyyah”.
juyawa sukayi jin muryar Safiyyah a bakin ƙofar shigowa tana cewa.
“Gani Aunty Rahma naje nayi wonka a wancan ɗakin ne”.

“Ok to ga abinci zo kuci”.

Cewar Rahma to tace kana ta shigo.
Aunty Rahma da Hibba kuma suka juya zasu fita Ishma na biye dasu.
Cikin yanayin gajiya Aysha tace.
“Ishma na zo mu zauna mana”.
Cikin sanyi tace.
“Mommy tace in barki ki huta”.
Fuskar Rahma ta kalla tare da cewa.
“Aunty bar min ita”.
Sake hannun Ishma tayi tare da cewa.
“Ai shike nan gata in ta buwayeku da surutu Safiyyah ta korata”.

Da sauri ta dawo ta zauna bisa cinyar Aysha kana su kuma suka fita.

Safiyyah ce ta zuba musu abincin.
Bayan sunci sun shane.
Aysha ta koma kan gado sabida har yanzu tana ɗan jin ciwon cikin kaɗan-kaɗan duk da tasha mgnin ta.
Kwanciya tayi tare dasa Ishma a gaba.
Ganin kamar bacci zatayi ne yasa Safiyyah fita, ta koma can cikin ƴan uwa nan sukaci gaba da hirarsu.

Saida aka kira sallan magriba ne duk suka tashi duk sukayi al’wala sukayi sallan magriba da yawa basu tashi bisa abin sallaba saida sukayi sallan isha kafin suka tashi.
Nan suka fara shirin tafiya walimar.

Aunty Hafsat Maman Safiyyar kenan wacce suke kiranta da Mamma ce ta nufi ɗakin Hibba tana cewa Safiyyah dake bayanta.
Yauwa zo ki kaiwa Jannart nata kayan da zatasa a walimar, gana Aysha kuma.”
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom ɗin Hibba.

A hankali ta ƙarasa cikin ɗakin.
Kana a hankali ta juyo ta kalli Safiyyah cikin yin ƙasa da murya tace.
“Har tayi bacci ne ma?.”

“Ai tun dazu ma tayi baccin, bari in tasheta”.
Safiyyah ta faɗa tana nufar gadon.
Da sauri Mamma tace.
“A a kada ki tasheta da ƙarfi ba’a son tada mai ciki daga bacci ta sigar da zata firgita”.

Aunty Rahma dake shigowane tayi saurin ƙarasowa tare da cewa.
“Kai Aunty Hafsat haba dama ni na lura kamar ciki take dashi naga tana yawan bacci”.
Juyowa sukayi suna kallon Safiyyah daketa dariya ƙasa-ƙasa cikin dariyar tace.
“Au ku dama kallon mai ciki kukeyi mata ashe.
To wannan kam yanzuma bata salla, kuma dama wasu in suna al’ada suna yawan bacci inaga ita hakane”.

“Kai Safiyyah wannan tsarabe-tsaraben naku na Nurses baya gaya muku gaskiya wasu lokutan”.
Mamma ta faɗa da iya kar gskyar ta.
Ita dai Safiyyah dariya tayi kana ta fara kiran Aysha.

Ita kuwa Aysha tun mgnar Mamma na forko ta farka daga baccin ta dai ci gaba da rufe idonta ne kawai sabida karta katse musu hirarsu.

A hankali ta buɗe idonta tare da yin salati kana ta miƙe zaune.
Cikin kula Mamma tace.
“Sannu ko tashi kiyi salla ki shirya dan har an fara kai mutane wurin walimar”.
Cikin sanyin bacci tace.
“To Mamma”.
Daga nan ta miƙa ta nufi Bathroom.
Ita kuwa Mamma miƙawa Safiyyah ledar kayan Jannart tayi kana ta ajiyewa Aysha nata a bakin gado tare da cewa.
“In kin fito ga kayan da zakisa a cikin jakar nan a bakin gado”.
“To ngd Mamma”.
Tace tana rufe ƙofar Aunty Rahma kuwa hannu tasa ta ɗauki Ishma dan zataje ta kimtsata.

Safiyyah kuwa da sauri ta kaiwa Jannart nata kayan ta dawo.

Tuni ƙawayen Umaymah manyan mata da matan abokan Abbansu Haroon matan sarakuna Da ƴaƴan sarakuna duk anata kaisu wurin da aka tanada dan yin walimar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button