GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Manyan mutane dattawa maza masu karamci da mutunci yan kasuwa da yan siyasa da sarakuna duk sun cika maƙil a babban hall ɗin.

Katon hall ne wanda a ƙalla zai iya ɗaukar mutune dari takwas zuwa ɗari dubu ɗaya.

An gyara wurin an ƙawatashi.
Ansa wani labule mai zaman kanshi an raba wurin biyu, kasan cewar dama ƙofofin shigowan biyune, haka yasa aka tsara wurin yadda mata zasu zauna a gefe ɗaya maza a gefe ɗaya bazama su ga junaba.

Sai can sama akayi wani ɗan dandamali wanda sai ka taka steps huɗu ana biyar zaka hau.
Shine wuri na musamman wurin zaman malami.

Ƙasa kaɗan dashi kuma wani ƙawataccen table ne mai kujeru shida, inda nanne wurin zaman angwaye da amare.

Can gefen inda malamin zai zaunama akwai ƙofar da ta nan zai shigo.

Tako ina ka cilla idonta haskene ras tamkar rana, wurin yayi kyau gwanin ban sha’awa.
Gaba ɗaya wurin mata da mazan ya cika maƙil duk manya-manyan baƙin sun samu isowa.
Hatta Sarki Ahmadu da tawagarsa da Abbansu Haroon da tawagar abokanshi duk sun iso.
Hakama Umaymah da da mutanenta hakama Mamma ta iso da Hajia Mama da Ummi da Aunty Juwairiyya da Hibba da Azeema.

Isowar Sheykh Jabeer da Ango da amaren kawai ake dako.
Madadin zama shurun sai akasa, sautin karatun al’ƙur’ani mai girma.

A can gida kuwa, Ibrahim, Haroon Sheykh da ne tsaye a harabar farfajiyar Side Umaymah, suna cikin wata iriyar fitinenneyar shiga mai masifar kyau da ban sha’awa.
Shigar fararen jallabiyar ƙirar Pakistan irin mai riga da wonɗonan ne kalar Sky blue mai azabar kyau da taushi da sheƙi.
Sai wasu tattausan al’kyabbar farare ƙal tamkar madara, al’kyabbar sun irin mai shara-sharan nanne haka ya bawa kolliyar tasu damar zama kamar adon sararin samaniya.

Sai hiramin dake kansu ne ya banbanta na kan Haroon da Ibrahim farine tas.

Sheykh kuwa nashi farine sai ɗigo-ɗigon Sky blue, hakama takalminshi hafl cover suma fararene sai ɗigon Sky blue.
Sai kekyawan zoben Daimond mai ɗigon Royal blue mai masifar kyau sai wal-wal yakeyi.

Sai ƙamshi sukeyi da sheƙi.
Ibrahim ne ya kira Safiyyah a waya tare da cewa suyi maza su fito mana.

To tace kana ta kalli Aysha dake cikin shigar doguwar riga mai masifar kyau da tsada, rigar iri ɗaya ce da Tata data Jannart.
sai dai tafi kama jikin Aysha sabida ta fisu faɗin ƙasa da sama.
Sunyi kyau sosai sunyi rolling kawunansu da gyalullukan suka fito tamkar yammatan larabawa.

Cikin sauri ta fesa turare kana ta kalli Safiyyah tare da cewa.
“To na gama mu tafi ko”.
Murmushi Safiyyah tayi tare da cewa.
“Masha Allah kinyi kyau. Mu tafi”.
Da haka suka fito.

A falo suka samu hadiman Umaymah nata gyara gidan.

Suna fitowa Aunty Rahma da Jannart suma suka iso.

Da sauri Ibrahim ya buɗe motarsa ya shiga, Safiyyah ta shiga gefenshi.
Aunty Rahma da Ishma suka shiga baya.
Haroon kuwa kama hannun Jannart yayi suka shiga bayan motarsa direbanshi na gaba.
Sheykh kuwa a hankali ya buɗe motarshi dasu Sulaiman da Ya Hashim suka zo da ita, kuma su tuni an kaisu can wurin walimar.
Kasan cewar babu mai janshi ne yasa ya shiga ya zauna a mazaunin gireban.

A hankali tabi bayanshi ganin tuni Ibrahim yaja motarshi hakama motar Haroon.

Cikin takun nitsuwa ta iso gab da motar, hannu tasa zata buɗe baya ta shiga.
Jin marfin a rufe yake yasa ta ɗan matso kusa da inda yake tare da cewa.
“A rufe yake”.
Ƙwayar idanunshi ya juya mata tare da mata alamun ta zagaya ta shigo can gefenshi.
Kasan cewar yana latsa wayarshi haskenta ya haska fuskarshi yasa ta gane manufarshi.
Zagayawa tayi ta buɗe ta shiga kana ta maida marfin.

A hankali ta juyo ta ɗan kalleshi jin yace.
“Bismillah”. Kana ya tada motar yaja suka bar harabar wurin.

Kasan cewar wurin babu nisa sosai da masarautar.
Tuni su Haroon sun isa har sun shiga sun zauna yanzu isowar Sheykh kawai ake jira.

Suna isa harabar wurin. Bayan yayi parking, suka fito.
Suna isa suka samu tarin fadawa a bakin ƙofar.
gaba yayi ya nufi ƙofar da zai shiga ta wurin.
Ita ma binshi a baya tayi.

Suna shiga, tayi maza ta kange fuskantar da bayanshi sabida. Tarin mutanen da ta gani sun firgitata, sam batayi zaton yawan mutanen ya kai haka ba.
Fahimtar hakane, yasashi yin gaba ita kuma tana biye dashi.
Har inda su Haroon suke. Kujerar dake gefen Jannart ya nuna mata.
Ai da sauri ta zauna.
Shi kuwa sunkuyowa ya ɗanyi kan Haroon kana yace.
“Ka nitsu da kyau ka saurari abinda Allah da Manzonsa suka ce a tsakanin ma’aurata”.
Cikin murmushin dake bayyana zallar jin daɗi da zumuɗin amarci Haroon yace.
“To Sheykh”.
Daga nan ya juya ya koma inda aka tanada domin shi.

Yana zama wani ɗan agaji ya dawo bayanshi ya tsaya.
kana ya miƙo mishi abin mgn.
Amsa yayi kana ya saƙalashi a bakin al’kyabbar jikinshi.

Gyara zamanshi yayi da kyau kana ya fuskanci taron al’ummar baki ɗaya.
Ɗaya daga cikin ƴan agajin ne yasa hannunshi ya katse sautin karatun Alqur’ani dake tashin.

Cikin nitsuwa kamala haiba da ilimi ya ɗanyi gyaran murya tare da fara bude taro da bimilla da addu’a da sallama.
“Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai’yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillalah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu’alla’ila’ha’illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhuwarasulu.
Ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa’ah wattaƙullah lazitasa’aluna bihi, wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiba, ya aiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna’asdaƙal hadisi kitabullah wa’ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi’a wa kulla bidi’atin balala wa kulla balaltun finnar.”
Dogon nufamshi ya sauƙe mai ɗan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli Side ɗin dasu Abbansu Haroon suke yace.
“Alhamdulillah kamar yadda muka sani, walimace ta farin cikin auren ƴan uwanmu, kana kamar yadda kowa ya sani walima shine aci asha kana a watse.
To a madadin muyi zaman da ci da sha kawai ya dace mu haɗa da ambaton sunan Allah, dayiwa ango da amrya taƙaitacciyar nasiha akan tsarin aure a musulunce da haƙƙoƙin ma’aurata ga junansu da addu’an zaman lafiya.”
A hankali yayi gyaran murya.
Kana ya muskuta ya gyara zamanshi da kyau ya fuskanci taro al’ummar Annabi dake gabashin.
Manya da yara maza da mata.
Especially matasa, yatsarshi manuniya yasa gyara zaman siririn farin gilashin dake manne a fuskarshi.

Ɗan sunkuyar da kanshi yayi.
Dai-dai inda abin sautin mgnar ke saƙale a wuyan al’kyabbar jikinshi.

Gaba ɗaya hall ɗin yayi tsit bakajin motsin kowa sai sautin numfashin mutane dana A/C.

Cikin tattausan lafazi muryarshi ta ratsa kunnuwan duk wanda yake wurin inda yace.

                      *AURE*

Ma’anar aure a musulunce shine. Sunnan Allah a wojen halittar Allah daya halitta ya haliccemu ne a jinsi guda biyu macce da namiji.
Kamar yadda Allah (S.W.A) ya ce, a Suratul Zariyya aya ta 49:-

(WA MIN KULLI SHA’I’IN KHALAƘNA ZAUJAINI LA ALLAKUM TAZAKKARUM)
“Kan ko wa wane abu Allah ya halice shi namiji da mace don ku yi tunani a kansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button