GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Sannan Allah maɗaukakin sarki a wata ayar ya sake cewa a Suratul yashin aya ta 36:-
(SUBHANALLAZII KHALAƘAL AZWAJA KULLAHA MIMMA TUMBITUL ARDU WA MIN AMFUSIHIM WA MIMMA LA YA ALAMUN)
“Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci ma’aurata namiji da mace, dukkansu daga abinda ƙasa ke sirarwa, kuma daga ko wannensu kuma da ma abin da basu sani ba!.”

Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli gefen maza, idonshi ya ɗan lumshe sabida gamsuwa da nitsuwarsu data tabbatar mishi, zantukanshi na ratsasu.
Idonshi ya ɗan tsaida kan fuskar Haroon ango mai jiran gado.
Sai kuma ya janye idonshi yaci gaba da cewa.
“Tabbas da wannan tsarin na auratayya ne. Allah ya zaɓa mana ya zama hanyar da zamuyi ta haife-haife muyi ta karuwa a bayan ƙasa.

Domin shi aure wata muhimmiyar igiyace wadda idan aka ƙullashi zai bawa ma’aurata daman saduwa tsakaninsu ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma’aurata zasu zama sutura ga junansu kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a Suratul Baƙara aya ta 187:-
“Su mata suturane gareku maza, sannan kuma maza sutura ne garesu-su matan.
Saboda haka zamu tabbatar lallai akwai al’ƙawari da amana mai ƙarfi a tsakanin ma’aurata, kuma Allah ya al’barkaci aure kuma yana son tabbatarsa , yana kuma ƙin ɓacinsa ba tare kwakkwaran larura ba.

Shi aure sunnace daga cikin sunnonin da ɗan Adam ya sami kansa a ciki, sannan kuma larurace daga cikin larurorin rayuwar ɗan Adam domin da aurene mutun zai kiyaye dangantakarsa, kuma ya ƙididdige ƴaƴansa wanda ya haifa kuma da shine zai kiyaye mutuncinsa, martabarsa dama dukkan dangantakarsa ga sauran ƴan uwansa da jama’a baki ɗaya kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a Suratul Furƙan aya ta 54:-
( WA HUWALLAZII KHALAƘA MINAL MAA’I BASHARAN FAJA ALUHU NASABAN WA SIRRAN WA KANA RABBUKA ƘADIIRA)
“Kusani Allah shine wanda ya halicci mutun daga ruwa kuma mai dangantaka surukuta kuma ka sani Allah mai iko ne akan haka”.

Sassanyan numfashi ya fesar a hankali, kana yaci gaba da cewa.
“Shi Aure sunna ne mai samar da nitsuwa tsakanin ma’aurata. Ɗan Adam bazai samu cikekkiyar nitsuwa ba a gidansa ba, sai in har yanada mata wacce ya aura.
Domin zata ɗebe masa kewa ta sashi ya samu nitsuwar hankalinsa.
Saboda zamansu tare a inuwar aure zatayi masa maganin kaɗaici kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗi a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN AMFUSIKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA’ALA BAINAKUM MA’WADDATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN)
ma’ana.
Yana daga cikin ayoyin Allah mai girma da ya halitta mana mataye daga kawunan mu, mataye da muke aure da su.
Domin su samu nitsuwa da junansu, sannan kuma ya sama musu soyayya a tsakanin su, tare rahama da tausayawa juna lallai a cikin wannan al’amari akwai ayoyi abin lura ga jama’an da suke masu tunani.
Saboda haka idan muka dubi wannan ayar ga ma’aurata zamu gane girman kudirar Allah da hikimarsa mai girma da ya halicci maza da mata kuma ya sanya ko wanne sashi mai karkata ga junansu kuma ya sanya igiya ya ɗaure tsakaninsu, wannan igiyar kuwa itace soyayya da tausayin juna da jinƙai.
Kuma Annabi (S.A.W) ya ce, cikin hadisin da Ibnu Majah ya ruwaito cewa.
(Babu wata fa’ida da mutun zai samu bayan ya. Takawar da Allah (tsoron Allah) wanda yafi masa al’khairi fiye da ya samu salihar mata ta kwarai wanda idan ya umarceta da tayi masa abu zata yi masa biyayya idan ya dubeta ta faranta masa ransa idan yayi rantsuwa game ita akan zatayi abu kaza ko bazata aikata abu kaza ba, zata kuɓutar dashi akan wannan rantsuwar da yayi, idan baya gida baya tare da ita, zata kiyaye mutuncinsa (Bazata yi fasiƙanci ba) kuma zata kula da dukiyarsa.
Ku duba cikin Fikihul Wadi littafin Dr Muhammad B Isma’il shafi na 9 zaku sami wannan hadisin.

A hankali Haroon ya ɗan juyo ya kalli fuskar amaryarshi Jannart, hannunshi yasa ta ƙasa table ɗin dake gabansu, tafin hannunta ya haɗe da nashi, tare da ɗan ronƙofowa kaɗan kana yace.
“Kina ji da kyau dai ko?”.
Cikin lumshe ido tace.
“Sosai ma kuwa”.
Aysha dake gefensu Haroon ya kalla tare da cewa.
“Al Sheƙiya matar Sheykh, ko zakije ki ja mishi baƙine?”.
Ido ta ɗan sunkuyar tare da fidda nannauyan numfashi kana a hankali tace.
“Ba dan gefen can da tarin maza manya iyaye da kakanni da sarakuna ba, tabbas da naje na zauna gefenshi na ja mishi baƙi”.
Safiyyah da Ibrahim dake bisa kujerun dake gefensu ne suka kalli juna tare da yin murmushi.

Abokan Haroon kuwa gaba ɗaya sun nitsu.
Abbansu Haroon da tawagarsa kuwa sai jinjina kai suke alamun gamsu ɗari bisa ɗari.

Ita kuwa Aysha a hankali ta ɗago kanta ta kalli inda yake, aikuwa karab idonsu ya haɗe cikin na juna,
taɓe laɓɓansa yayi tare dasa hannunshi ya shafi tattausan sajenshi kana a nitse yaci gaba da cewa.
“Aure kariya ce, kuma GARKUWA ce ga Musulmi saboda duk wanda yakeda mata, to ba zaka ganshi ya bar gida yana yawace-yawace ba ko ka ganshi yana leƙe-leƙe a woje ba, don yana da irinsa a gidansa, saboda haka mata ta zama GARKUWA a rayuwar ɗan Adam. Saboda haka ne ma Annabi (S.A.W). Ya kwaɗaitar da matasa samari da yin aure a cikin wani hadisin da muka samu a cikin Fiƙhul waɗi littafi na 2 na Dr Muhammad B Isma’il shafi na tara, Annabi (S.A.W) ya ce:-
Yaku samari wanda ya samu iko daga cikin ku to yayi aure.
Domin shi aure yana kare mutuncin farji da aukuwa cikin haram, (Yin zina) wanda bai sami iko ba to lallai ne ya juri yin azumi.
Domin assaumu junnatu, shi azumi GARKUWA ne.
Kuma shi aure cikon addini ne, saboda idan muka dubi aure sosai. Zamu fahimci aure yana taimakawa musulmi wajen tsare-tsaren addininsa kuma da wannan ne addininsa yake cika kamar yadda.
Dabarani da Hakim suka ruwaito daga Buhari da Muslim inda Manzon Allah (S.A.W) yake bamu labari a kan cewa aure tsari ne wanda yake taimakawa ga mutum ya cika addininsa a in da yake cewa:
Yana daga cikin arzikin Allah.
Allah ya azurtaka da mace salihan ko salihan mata, haƙiƙa zata taimaka ko wannan auren zai taimaka akan wani yanki na addini ka sai kuma kaji tsoron Allah akan sauran yankin.
Aure sunnace ta Annabawa da manzanni, saboda haka idan kayi aure ko yi ne da Annabawa da manzannin Allah. Allah maɗaukakin sarki ya faɗi:-
(WA LAKAD ARSALNA RUSULAN MIN ƘABLIKA WAJA’ALNA LAHUM AZWAJAN WA ZURRIYYAH)
Haƙiƙa mun aiko manzanni kafin kai, (Muhammad, S.A.W) kuma mun sanya matayen aure da zuriya a garesu.
Idan muka duba zamuga cewa yin aure koyi ne da aikin Annabinmu Muhammad (S.A.W) ne in da yace:-
(Kuyi aure ku yawaita domin ni zanyi alfahari da yawanku ranar lahira”.

Juyowa yayi ya fuskanci gefen taron maza, kana yaci gaba da cewa.
“Kamar yadda muka sani cewa.
Mace abokiyar zama ce kuma shimfiɗa ce ga mijinta kuma mai rainon gidansa ce kuma abokiyar rayuwarsa ce, sannan kuma uwar ƴaƴansa ce sannan mai kula da dukiyarsa ce da mutuncinsa cikin amana saboda haka idan mata-ta zamo salihan ta gari to sai ta zamo kyakkyawan abu na duniya kuma ni’ima daga cikin manya-manyan ni’imomin da Allah ya azurtaka da ita”.

Gyaran murya yayi tare da gyara zamanshi, kana ya fuskanci Haroon da Jannart da kyau, sannan ya ɗan kalli Aysha da wutsiyar idonshi.
Tura bakinta ta ɗanyi fahimtar ita yake kallo, kanshi ya jinjina kana ya buɗe muryarshi da ɗan ƙarfi dai-dai misali yadda amon mgnarsa zata ratsa kunnen kowa yace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button