Umaymah kuwa sai murmushi takeyi tana ƙara godewa Allah da samun Sheykh a ahlinsu.
Mamma ma sai murmushi takeyi.
Jamil Jalal Azeez da Sadiq da Imran ne suka ɗan haɗe kansu suna ƴar hira ƙasa-ƙasa.
Da sauri suka ɗago kansu jin muryar Sheykh yana cewa.
“Jamil ku fita waje kuna toshewa jama’a kunne”.
Cike da mamaki suka miƙe suna kallonshi suna al’ajabin ya akayi ya gane su kuma har yaji muryarsu.
“Ku fita”. Suka sake jin muryarsa, cikin tuttura baki suka fita.
Aysha kuwa tafin hannunta tasa ta tallabe haɓarta, tare da zuba mishi ido cikin wani abinda bata san sahihancinsa ba, take kallon tattausan lips ɗinshi suna motsawa yana mai ci gaba da cewa.
Kanshi ya sunkuyar sosai, babu mai iya ganin kwayar idanunshi cikin tarin al’kunya yace.
“Haƙƙin jima’i haƙƙine wanda yake tsakanin miji da mata.
Amman ƙarfin haƙƙin yafine gashi mijin, shi yake da haƙƙi mafi girma. Kuma shi wannan jima’in yana daga cikin manufofin aure, domin shi aure shi yake tabbatar da mutane su wanzu, su tabbata akan ma’aunin mutane su ba nau’in dabbobi ba.
Domin shi dabba duk lokacin daya buƙaci biyan buƙata yin jima’i zai tare dabba mace ƴar uwarsa ne a hanya nan take ya biya buƙatarsa ya rabu da ita, kamar yadda muke gani a tsakaninsu yana faruwa.
Shiyasa duk mazinaci bashi da banbanci da Dabba!.
Jima’i babban al’amari ne cikin auratayya, domin biyawa kowa buƙatar sa, kana jima’i wata iriyar sutura ce wadda ma’aurata suke suturce junansu, kamar dai yadda Allah maɗaukakin sarki yace a cikin suratul baƙara aya ta 187:-
(UHILLA LAKUM LAILATASSIYAMIRRAFASA ILAA NISA’A IKUM HUNNA LIBAASULLAKUM WA’ANTUM LIBAASULLAKUM) A halasta muku matanyenku kuyi jima’i dasu a dararen Azumi, domin su mata sutura ne a gareku, kuma suturce a garesu.”
Ɗan ɗago kwayar idanunshi yayi ya fuskanceta Aysha, kollon kwayar idanunta data zuba mishi yayi na ƴan wasu daƙiƙu kana yaci gaba da cewa.
“A wata ayar Allah maɗaukakin sarki ya siffanta mata da cewa gonakine a garemu maza, ku zowa gonakinku a duk lokacin da kuke so.
Ayar itace.
(NISA’UKUM HARSULLAKUM FA’ATUN HARSUKUM ANNAA SHI’ITUM) Matanku gonakinku ne ku zowa gonakinku a duk sanda kuke so”.
Haroon ne ya ɗan matse hannun Jannart dake cikin nashi kana ya ɗan juyo ya kalleta.
yana wani ja’irim murmushi.
Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ƙanƙance kwayar idanunshi ya watsasu cikin manyan idanun Aysha ya tsareta dasu.
harshenshi ya ɗan turo woje ya ɗan lasi lips ɗin shi kana yaci gaba da cewa.
“Kamar yadda aka faɗa shi jima’i Saduwa haƙkine ga kowa wanne ɗaya daga cikin mauratan, hakan ya sanya ya zamo wajibi ga mace lallai ne dole ta bada haɗin kai a duk lokacin da mijinta ya nemeta da jima’i matuƙar dai bata cikin haila ko jinin biƙi ko kuma da rana cikin watan Ramadan. Ko tana cikin wani uzurin wanda zai iya hanata biya mishi buƙatar sa. Uzurin kuma ya zama na Shari’a yardajjen kamar rashin lafiya mai tsanani. To in ba waɗannan uzurorinba babu wani dalilin da zai sa mace taƙi bada haɗin kai ta biyawa mijinta buƙatar sa.
In kuwa taƙi bashi haɗin kai da son ranta, to zata haɗu da tsinuwar mala’ikun Allah kamar yadda yazo a hadisin Bukhari da Muslim wanda ke cikin.
Minhaju Muslim shafi na 380 sun ruwaito daga Annabi (S.A.W) yace.
( Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa don yin buƙatar sa, Saduwa da ita, sai taƙi yarda ta bashi haɗin kai, sakamakon hakan sai mijin ya kwana cikin fushi da baƙin cikin hakan da tayi mishi. To Mala’ikun Allah zasuyi ta sinemata har sai gari ya waye.
Lallai ne mace ta sani mijinta yana da ikon biya buƙatarsa da ita a duk lokacin da yaso hakan.”
Juyowa yayi ya fuskanci mazan da kyau kana kwayar idanunshi a sunkuye yace.
“Haƙƙin mace kuwa a kan jima’i malamai sun karkasu kan wannan hukuncin kamar haka.
1 Mafiya yawan malamai suna ganin wajibi ne ga miji ya biyawa matarsa buƙatar ta jima’i a duk sanda ta nema. Domin yin hakan yana cikin kekkyawan zamantakewa kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya yi umarni dashi inda yace.
(WA’ASHIRU HUNNA BIL MA’ARUF)
Kuyi musu kekkyawan zamantakewa babu cuta ba cutarwa.
2 Su kuma shafi’iyyah suna ganin cewa shi jima’i haƙƙin mijine sabado haka baza’a tilasta shi yayi dole ba.
3 Hanabila kuwa suna ganin cewa.
Baya halasta miji yaƙi yin jima’i da matarsa fiye da wata huɗu.
Saboda haka wajibi ne miji ya sadu da matarsa cikin ko wanne wata huɗu.
4 Ibn Hamza yana cewa wajibi ne miji ya sadu da matarsa cikin ko wanne tsarkin hailan da tayi.
Matuƙar yanada halin yin hakan, domin yin hakan shine mafi ƙarancin tarawa da zaiyi da ita.
Amman a karan kaina a fahimtata ni dai Muhammad nafi nitsuwa dana forkon nan wanda mafiya yawan malamai suka yarda dashi matuƙar yana da ikon yin haka, ya biya mata buƙatarta duk sanda ta nemeshi, domin yin hakan shine zai kiyaye mutuncinta da addininta kamar yadda Musulunci ya umarceshi da ya yi”.
Numfashi ya ɗan fesar kana cikin nitsuwa yace.
“A gaggauce ga laduban jima’i.
Wasu abubune wanda ake buƙatar aikatasu lokacin da mata da miji sukayi nufin saduwa. Jima’i da junansu, idan ka aikata waɗannan abubuwan zaka ƙara samun lada a wannan ibadar saduwar da zakiyi, amman kuma in baka aikata ba, bakayi zunubi ba,sai dai kayi asarar wannan ladan wanda aka tanada domin waɗanda suka aikata waɗannan abubuwan wojen koyi da sunnar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama.
Domin su waɗannan laduban Sunnah ce da.
Masu yawa amman ga kaɗan daga ciki:
(1) Addu’a ana son miji idan zai sadu da matarsa yace.
“BISMILLAH ya kuma yi addu’a to idan yayi hakan yayi abinda ake so aiki da ladabi kamar yadda yazo a Hadisin Bukhari da Muslim, Tirmiziy Ibn Majah, Abu Dauda suka ruwaito Hadisin Abdullahi ɗan Abbas cewa.
Manzon Allah (S.A.W) yace.
Da ace ko wanne ɗayanku lokacin da zai zowa matarsa yin jima’i zai ce.
(BISMILLAH ALLAHUMMA JANNIBAL SHAIƊAN WA JANNIBAL SHAIƊANA MARAZAƘTUNA) to idan Allah ya ƙaddara samun ɗa a wannan saduwar to shaiɗan bazai cutar da wannan abinda za’a haifaba har abada.
Saboda haka ya kamata duk mijin da zai sadu da matarsa ya kiyaye wannan, in kuma kinga mijinki shagalellene ke mace kike tunasar dashi. Dan samuwa ya’yan da zaku haifa kariyar Allah.
2 Wasanni kafin jima’i.
Yin wasanni gabanin jima’i domin samun cikekken jin daɗi, kamar yadda aka ruwaito.
Daga Annabi (S.A.W).
“Kada ku aukawa iyalanku da gaggawa, har sai wani abu na sha’awa ya fito musu, irin wanda ya fito maka, domin kada ka rigata yin inzali fidda manniyi.
Sai wani daga cikin Sahabbai sukayi tammabaya.
“Shin wannan jin daɗin mata daga gareni ne?
Ma’ana Ni zan sa taji daɗin.
Sai yace,
Na’am zaka sata taji daɗi ne ta hanyar sumbatarta haɗa baki da baki ruggumarta da abinda yayi kama da haka.
Idan kaga wani abu ya zo mata, na ruwan maniyyi irin wanda yazo maka, daga nan sai ka sadu da ita.
3 Tanadar kyalle domin goge maniyyi.
4 Kada ayi jima’i tsirara.
5 Yin al’wala idan zaka sake mai-maita na biyu ko na uku, ko fiye da haka.”
Ɗan tsagaitawa yayi ya kalli hadimai mata dake ta jere ababen ci da sha akan ko wanne table yawan adadin mutanen dake zagaye da table ɗin yawan abubuwan da ake ajiyewa.
Idonshi ya ɗan juyo ya kalli gefen maza. Nanma hadimai mazane keta jera abubuwan cin da na sha, kana.
Ta gaba gaba kuma wurin VIP sukuma Jamil, Jalal, Azeez Sadiq sune suke ta jerawa.