GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Littafin GARKUWA na kuɗine in bazaki iya biyan special Group ba a sauƙaƙe akwai Normal group 300 kacal

                        By
          *GARKUWAR FULANI*[3/15, 9:56 PM] +234 806 559 0880: Cikin tashin, fargaba, tsoro, kiɗima, gigita, ta ɗago kanta da azaban ƙarfi lokacin data ga yana sunkuyo da bakinshi nufin zai mu'alamanceta tamkar mijin aurenta, kuka mai cike da tsaro ta saki, sai  disashewar da muryarta tayi ta hana sautin fitowa fili.

Wani irin karkarwa da tsuma jikinta ya farayi, wata azabebiyar zufa ta karyo mata lokacin da numfarfashi ya fara korar juna alamun zai ɗauke.

Sam har ga Allah bai san takai wannan matakin tsorita da razanaba.
Kana ganin ababen marmarinsa yasa ya mance a suffan waye ma yazo mata.
Kanshi ya ɗago hango mutun ya fito cikin halla ɗin ya nufo harabar wurin motocin.
Da sauri ya saketa, cikin abinda bai gaza second biyu ba, ya buɗe marfin motar ta gefen da take ya fita da sauri kana ya sunkuya, a sunkuye yabi inuwar motocin dake gefenshi.

Ita kuwa Aysha ta gama gigicewa ta ɗimauce tana jiran taji ya tozarta mutuncinta da darajar aurenta wanda take fatan ta mutu yafiye mata.
Jin an buɗe marfin motar ya kuma sauƙa kan cinyarta ne, yasa ta tashi cikin azama da gigita.
Cikin tattaro sauran kuzarinta da buɗe muryarta take cewa.
“Ya Sheykh! Ya Sheykh!! Ya Sheykh!!!”. Tanayi tana gyara wuyan rigar tare da maida caɓɓullenta ta killacesu, sai dai duk tanayin abin a gigice ne kuma har lau numfashin ta na fuzga.
“Ya Sheyyyyykh!.” Ta kuma danna kiran da ƙarfi numfashin ta na fizgewa.
Dai-dai lokacin kuma taji an buɗe marfin motar ta gefen driver, cikin tsananin zabura da kaɗuwa ta juyo a firgice.
Shima Sheykh da yanzu ya iso wurin da sassarfa,
da sauri yasa kai ya shiga cikin motar ba tare da ya ida shiga motarba ya zauna.

Ita kuwa Aysha. Wani irin yunƙura tayi ta abko jikinsa da ƙarfi.
Da sauru yasa hannunshi ya riƙe kujerar kana ya jawo marfin motar ya rufe da ƙarfi sabida jin da yayi yana baya alamun zai koma baya ya faɗi.
Cikin mamaki da ɗaga murya yace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, ke me hakan? Zaki kadamu fa!.”
Ina gaba ɗaya jikinta rawa tsuma karkarwa yakeyi tamkar mazari, cikin fizgar numfashin ganin tsira tace.
“Ya Sheykh Jahan! Jahan!! Jahaaaaan!!!”.
Ta ƙarashe mgnar tare da shigewa jikinshi da kyau ta cusa kanta cikin ƙirjinshi, wanda yake bugawa dib-dib yana harba sama da sau ɗari a cikin ko wacce daƙiƙa.
Yayinda nata ke harbawa samada sau ɗari da hamsin a cikin ko wanne daƙiƙa sabida tsananin tashin hankali da kiɗima da firgici.

Cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da ƙarfi kana ya buɗesu da sauri, yayinda tuni suke jazir kana shima jikin nashi tsuma yakeyi.
Hannunshi yasa ya ruggumeta gam-gam a jikinshi da kyau, al’kyabbar jikinshi ya ware da kyau ya buɗa ta kana ya rufeta dashi rib. Sabida yadda jikinta ke rawa abin ya zarta zaton mutun.
Cikin wata iriyar murya mai cike da diriricewa tausayi rauni murya a sarƙafewa yace.
“A’ich! A’ish!! Kiyi haƙuri I’m so sorry, in sha Allah bazan sakeba, ki yafe min kinji”.
Ina babu amsa sai ƙara cusa kanta da takeyi jikinshi bata kuma haiyacinta har yanzu bare ta fahimci me yake faɗin.
Cikin taune lip ɗinsa na ƙasa yace.
“A’ich ki nitsu ki kwantar da hankalinki babu abinda zai sameki. Kinji ba gani ba.
Babu kowa da zai cutar dake da izinin Allah”.
Ina ita dai sai ƙara ƙwaƙumarshi takeyi.

A hankali ya juyo ya kalli gefenshi jin ana ɗan ƙwanƙwas glass ɗin motar,
Ƙasa yayi da glass ɗin.

Ya Hashim ne da Affan da Jalal Imran da Sulaiman sai Kabir ƙanin su Haroon wanda suka haɗa uba, kuma a motarsa suke da kuma motar ɗaya Haroon dake hannun Jalal,
kasan cewar bai sauƙe gilashin sosaiba, basa iya ganin Aysha dake kwance a jikinsa.
Affan ne ya ɗan motse kana yace.
“Ya Sheykh mufa gobe sammako zamuyi, shiyasa muke son key ɗin motar ya kwana a hannunmu”.
Kanshi ya jingina da jikin kujera kana ya kalli Ya Hashim da Sulaiman da Imran yace.
“Ku bari sai jibi ku tafi, mana kunzo jiya, gobe kuce zaku koma ku dai bari jibi”.
Kai Sulaiman da Ya Hashim suka gyaɗa alamun yarda.
daga nan suka juya suka nufi motar Kabir tare da cewa.
“To sai da safe”.
Allah ya bamu al’khairi yace kana ya ɗaga glass ɗin.
Su kuma suka shiga mota sukaja suka tafi.

A can gida kuwa bayan duk sun watsa ruwa kowa yayi shirin baccine, sai kuma duk suka firfito falo suka kafa hira irin ta ƴan uwa in an haɗu a biki.
Umaymah ce ta kalli Aunty Rahma dake kwance gefenta tayi pillow da cinyarta tace.
“Wai ina Safiyyah da Aysha ne, su ban gansuba”.
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
“Safiyyah dai tabi mijinta, ita kuma surkar tawa inaga itama suna tare da ɗan naki”.
Ummi ce ta ɗan kallesu tare da cewa.
“Ai kuwa ni tun ɗazuma naketa kiranta bata ɗaya wayar”.
Mamma ce tace.
“Halan suna can tare”.
Hajia Mama dake zaune gefen Umaymah ce ta ɗan kishiƙiɗa da tum-tum tace.
“Uhummm”. Daga nan bata kuma cewa komaiba.
Ummi kuwa ci gaba da kiran Aysha tayi, wayar tana shiga amman ba’a ɗagawa.

A can kuwa wurin Sheykh da Aysha.
Gyara zamanshi yayi da kyau bayan, abokan Abbanshi duk sun tafi.
Gyara mata zamanta a jikinshi yayi da kyau yadda bazata takurashi yin tuƙiba gaba ɗaya zuciyarshi a hautsine take, ya rasa gano wake tura mishi wasu pictures ɗin Shatu da mishi zantukan ita yar iskace.
Allah ya sani baya zarginta ko wannan abun ya fara faruwa ne dan ta ganshi da kamanninsa na sirri, da fari tsiya yake mata, sai kuma yake jin dadin yanayin yakanyi ta murmushi in ya tuno tsoron da yake gani a kwayar idanunta, yana mmkin yadda take gaza gane muryarsa, to batun hotunanta fa da ake tura mishi da wani yanzu ya gama gamsuwa aiki magautansa ne.
Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi tare da tada motar, A/C’nta ya kunna, sabida wata iriyar fitinenneyar zufar dake tsastsafo musu su duka biyun.
Ƙafarshi ya murza ya kaita kan birki, lokacin da ya iso gab da bakin gate, ɗan tsayawa yayi aka buɗe musu gate ɗin, kana ya cilla hancin motarsa woje.
Da hannun ɗaya yake murza siterin motar, hannun damanshi.
Kana hannun hagunshi kuma na ruggume da ita.
Zuwa yanzu yaji rawanda jikinta keyi ya fara tsagaitawa.

Ita kuwa Aysha cib tayi a jikinshi tana jin yadda bugun zuciyarshin ke harbawa da sauri-sauri kana kuma da ƙarfi-ƙarfi.

Tafiya mai tsawo sosai, har ya fara fitowa wojen gari.
A hankali ya ratsa wani titin ya shiga, tafiya kaɗan yayi ya ratsa cikin wani tamfatsetsen hotel mai masifar kyau wanda yake killace a bayan gari, sabida manyan mutane ba kasafai suke son hotel ɗin dake sarari ba.

Bayan ya gyara parking ya kashe motar.
Ɗan sunkuyar da kanshi yayi kanta
sannan a hankali yasa tafin hannunshi ya tallabo kanta, cikin sanyi ta buɗe idonta.
Ta ɗan kalleshi kana ta medasu ta lumshe.
Manyan yatsunshi yasa yana ɗan shafa kuma tunta dasu.
Kana a hankali yace.
“A’ish kiyi haƙuri kinji bazan sake yin nesa da keba”.
Sai kuma ya ɗanyi shiru kana ya kusanto da fuskarshi gareta sosai, a hankali ya hura mata iskar bakinshi kan idanunta tare da cewa.
“Buɗe idon Yah Sheykh ɗinki ne, ba Jahan ba”.
A hankali ta buɗesu, ta kalleshi.
Wani dogon nannauyan ajiyan zuciya ta sauƙe tare meda kanta saman ƙirjinshi”.
A hankali yace.
“Wayyo Mamy zata karya min cinya, sauƙa muje ciki.”
Bata kulashi ba, ganin hakane yasa ya buɗe ƙofar kana ya ɗan mirginata gefe, sannan ya sauƙo.
Gyara tsayuwarshi yayi tare da gyara hiraminshi ya rufe fuskarsa da kyau sannan yace.
“Aish fito ko Boɗɗi”.
Da sauri ta zuro ƙafafuwanta woje sabida gani take yana matsawa Jahan zai zo.

Marfin baya ya buɗe. Wasu ledodi masu kyau ya ɗauka kana ya rufe motar tako ina, sannan ya juya, ya nufi ciki da sauri ta bishi a baya.
Tafiya kaɗan sukayi suka haɗu da Jamil.
cikin sauri ya iso gabansu, key ya miƙa mishi tare da cewa.
“Room number 37 VIP Side”.
Kai ya gyaɗa tare amsar key ɗin.
“Sai da safe”. Yace yana mai wucewa.
“Allah ya bamu al’khairi yace kana.
Suka wuce shima ya wuce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button