Suna shiga, ɗakin.
A hankali ya miƙa mata ledodin.
Sannan ya juyo ya rufe ƙofar, duk da yasa Jamil ya bincika masa ɗakin saida ya ƙara duba jikin ƙofar da makunnin fanka da A/C da kyau. Kana ya dawo tsakiyar ɗakin ya ɗaga kanshi sama ya kalli sanan sosai hakama ya shiga bathroom ya duba komai saida ya tabbatar ba komai daga cikin ababen da ya kamata duk musulmi in larurar zuwa hotel ya kamashi ya tabbatar da ya bincikesu da kyau Especially in ku mata da miji ne.
Ita kuwa Aysha da Ido take binshi, ta rasa me yake nema a duk ɗakunan hotel da suka taɓa zuwa.
Bathroom ɗin ya koma, bai daɗe sosai ba, ya fito, bisa alamu ruwa ya watsa, kana dan al’kyabbar shi na hannunshi yanzu dagashi sai jallabiya.
ninke al’kyabbar yayi, kana, ya ajeshi gefe, inda ya ajiye hiraminshi da wayoyinshi.
Ledodin hannunta ya amsa tare da cewa.
“Je kiyi wonka kizo ki kwanta”.
Cikin sanyi tace.
“Ni nayi wonka ɗazu”.
Kanshi ya gyaɗa dan ya lura har yanzu a tsorace take.
Zama yayi bisa sallayar da yasan Jamil ne ya shimfiɗa misa kana yace.
“To zauna kici abinci”.
Da sauri tace na ƙoshi”.
Ido ya ɗan zuba mata, kana yace.
“Uhummm, to kwanta kinga gani nan kusa babu abinda zai sameki da izinin ubangiji”.
Da sauru tace.
“Toh”.
Ta ƙare mgnar tana nufar kan luntsumemen gadon.
Ledodin da Safiyyah ce ta ajiye musu cewa na abincin walimar ne kuma tace mishi Ummi da Umaymah da Mamma ce da kansy sukayi aikin ne yasa, ya gamsu da aikin kuma zaici.
Sosai yaci naman zabuwar da Arish ɗin.
Ɗan saura kaji akayi na zabbin na musamman ne shiyasa su Umaymah suka yishi da kansu.
Ruwa yasha, kana ya gyara zamanshi tare da tattare sauran bakin ledar ya ƙulle. Jingina bayanshi yayi da jikin gadon.
Kana ya fara rairai karatun al’ƙur’ani cikin zazzaƙar muryarsa haka yasa yaji sanyi zafin da zuciyarsa keyi na fahimtar sharrin magautanshi har baiwar Allahr da bataji bata ganiba, kawai dan ta kasance matarsa magautansa ke bita da sharri.
A hankali Aysha ta sauƙe ajiyan zuciya, tana mai jin daɗin sautin muryarsa da karatun da yakeyi a hankali.
Mirginowa tayi bakin gadon.
Kana ta kwanta tayi lib ta matso da kanta kusa da kafaɗunshi.
Lokacin ɗaya taji bacci na fizgarta.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya juyo ya kalli wayarshi daketa haske alamun ana kiranshi.
kasan cewar yazo ƙarshen suratul Maeda sai yayi addu’a ya shafa.
Kana ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar, Ummi ya gani a saman screen ɗin ya kai yatsarsa kenan kiran ya katse.
Dama shima katse kiran zaiyi shi zai kuma kiranta.
A can gida kuwa Umaymah ce ta ɗan kalli Ummi tare da cewa.
“Sake kiranshi ni naji tsoro ita a kirata bata ɗagawa kuma shima a kirashi bai ɗagawa”.
Cikin gyara zama Ummi tace.
“Zai kira, in yaga kiranmu inaga baya kusa da wayane sanda kika kirashin.”
Shiru suka ɗan yi.
da sauri Ummi ta kalli wayarta.
“Yauwa gashi ma ya kira”.
Ta faɗa tana amsa kiran.
“Assalamu alaikum, Ummi”.
Cikin jin daɗi tace.
“Wa laikassalam Sheykh kana lfy”.
“Alhamdulillah”. yace
Yana gyara zamansa.
Da sauri tace.
“To Masha Allah. Aysha fa munyi ta kiran wayarta bata ɗagawa, hankalinmu ya tashi tana lfy ko?”.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta kana yace.
“Uhummm to ga dai ta nan Ummi, wannan tsoron nata ne yau kuma ya dawo a cikin mota kafin in fito tace, wai Jahan yazo, gaba ɗaya ta gigice shiyasa ma ban kawota nan wurinku ba”. Ya ƙarashe mgnar a kunyace wai kada suyi zaton rashin kunyane da jarabar mace ya sashi ɗauketa.
Cikin tsoro Ummi tace.
“Subahanallahi Jahan kuma, Sheykh ya kamata kasa ido sosai fa a kan abun nan”.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta, tayi shiru ta zuba mishi ido.
A hankali yace.
“Ummi babu batun wani Jahan fa, Ni inaga Ja Ha N nefa Ummi suka bada Jahan.
Kawai dai magautanna ke mata barazana da sunan.
Dan suna da wata manufa akanta akayi katari kuma akwai mai suna Jahan sanane a gari aikinsa kuma sirrine, shi kuma an bani tabbacin ma baya ƙasar mafa tun watannin baya kawai mutanenta ne”.
Da sauri ta tashi zaune cikin rauni tace.
“Wallahi mutum ne, ba iska bane, Ni bani da iska ka dena cewa iskokaina, wlh Ummi mutum ne”.
Ummi da taji muryarta cikin kula tace.
“Sheykh ka ƙara kula kan iya linka”.
“To Ummi”. yace
Ita kuwa Umaymah ta miƙawa wayar.
Jin muryar Umaymah ne ya sashi cewa.
“Umaymah ba komai fa ku kwantar da hankalinku”.
Cikin kula da so tace.
“To Jazlaan Allah ya kare mun ku, saida safe ko”.
Amin Amin yace kana ya katse kira.
Miƙewa tsaye yayi, tare da wayar a hannunshi inbox ɗinsa ya ɗan shiga text ɗin da aka turo mishi ɗazu da pravate number, ya Kuma zuwa ido.
“Da kyau kayi tabsir mai zafi, sai ka kula da yar iskar bororiyar da aka auro maka, mai son maza.
kayi amfanin da wannan damar ko zaka gaskata abinda muke gaya maka, na son maza da binsu.”
Idonshi ya rumtse da ƙarfi kana ya buɗe su a hankali.
Su kuwa can sashin magautan Sheykh sun dade da fara turo mishi irin waɗannan saƙonnin a saninsu dai sun san sun kashe mazakunta Sheykh bazai iya raɓar maceba.
Shiyasa suke nuna mishi ita Aysha yar iskace dan su samu su haddasa zargi a tsakaninsu, shiyasa suke cewa ya gwadata duk da su a zatonsu wani zai wakilta ya gwada masa ita.
Sabida basu san yanada wani sashi na sirrin aikinshiba. Wanda yake bibiyar komai wanda Shatu kuma ta taɓa yin karo dashi a lokacin da yake fita aikin nashi da dare.
So shiyasa yake amfani da wannan damar.
Numfashi mai zafi ya fesar.
A hankali ya kalleta ganin ta mirgina ta koma can tsakiyar gado tana mgna kaɗan-kaɗan.
“Ni bani da iska Allah ma ya sani, koma menene ai a gidanka ne ya fara min, komai sai kayi ta cewa inada iska, har kana gayawa mutane, zakasa ayita min kallon mai iska.
Na tambayi Bappa na yace min iya tsawon rayuwata basu sanni da iskaba, kuma ai da sun sani da zasu gayawa Lamiɗo”.
A hankali yasa hannunshin ya kashe wutan ɗakin.
Da sauri ta taso zaune lokacin da duhu ya mamaye ɗakin.
“Dan Allah ka kunna wutan”.
Da sauri ta matso kusa dashi jin yayi mgna kusa da ita yace.
“Ni bana iya bacci in haske na kunne. Kwanta gani nan babu wani al’jani Jahan da zaizo da yardar Allah”.
A hankali ta zame ta kwanta kusa dashi.
Yayinda shi kuma yake zaune.
“Tashi ki zauna kiyi addu’a kafin ki kwanta”. Yace mata lokacin da yaji ta kwanta.
Cikin bacci tace.
“Na gaji kayi min mana”.
Kanshi ya jinjina jin wai ai ta gaji.
Tafukan hannunsa ya hada ya buɗa, kana ya karanta ƙulhuwa 3 falaƙi 3 nasi 3 Ayatulkursi’u 1 ya tofa, kana ya shafawa jikinsa.
Sannan ya kumayi kamar yadda yayi ya tofa kana ya juyo kanta, daga kan fuskarta ya kife tafin hannunshi ya shafa mata har zuwa kan yatsun ƙafarta kana ya shafa kanta, sannan ya kwanta kan gefen damanshi.
A hankali yasa hannunshin ya juyata yace.
“Kwanta ta gefen dama”.
To tace ya zama baya ta bashi.
Shiru tayi tanajin alamun kamar karatu yakeyi.
tsawon lokaci sukayi a haka batayi bacciba shima baiyi baccinba.
A hankali ta juyo sabida gajiya da gefen daman yayi mata.
Lumshe ido tayi.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya yunƙuro ya matsota sosai, cikin sanyi tace.
“Ka matseni fa”.
“To ki koma can baya mana.”
Yace mata. Yana lumshe idonsa.
A hankali ta mirgina zata matsa, sai kuma ta ɗan tsaya jin tama isa bakin gado, daga ita sai katanga, juyowa tayi ta fuskanci katangar ta kwanta tayi shiru.
Shi kuwa Sheykh shima shirun yayi, yana dogon nazari kan al’amarin Jahan da yake girmama kullum a wurinta, ya lura yau saura kiris ta suma.