GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Tana shiga ta samu Junainah ta idar da sallan,
Gefenta ta zauna, tare da jawo jakarta, sweet ɗinta data seyo mata, ta kwaso ta fitar mata.
Ai kuwa tuni fushi ya ƙare, tazo ta raɓa jikin yayartata.

Ummey kuwa da Inna saida sukayi sallan isha, kafin suka, fito tsakar gida dan tuni hadarin nan ya watse sai iska mai sanyi daketa kaɗawa.

Bappa da su Ya Ladoma saida aka idar da sallan isha kafin suka dawo gida.

Gaba ɗayansu a tsakiyar gidan suka zauna bisa manyan taburmaii guda biyu mazan na kan ɗaya matan na kan ɗaya.

Abinci sukeci mai rai da lfy, tuwon faran ɗanyar shinkafa, da miyar ɗanyar kuɓewa data sha man shanu da tantakwashi, sai kifin banda sabi kifi na araha a wurinsu.

Sai kuma zazzafan kunun nono da yaji nono da zuma.

Sunaci suna ira ga hasken farin wata daya fito yayi ral ya haska ko ina na gidan.

Cikin jin daɗi, Giɗi yace.
“Shatu hutun mai tsawone ko gajere?”.
Kunun nonon data kurɓa ta haɗiye kafin tace.
“Eh to Yaya Giɗi hutun sati uku ne muka samu”.
Seyo ne ya amshi zancen da cewa.
“A hutun da ɗan yawa”.
Shi kuwa Giɗi dariyar mugunta yayi tare da cewa.
“Ai kuwa naji daɗi wlh sai kinyi kiwo kema kiji hazar da muke ji”.
Bappa ne ya amshi zancen da cewa.
“Giɗi mugunta ba kyaufa, Wato kai wuya kakeso tasha”.
dariyar ƙeta ya kumayi tare da cewa.
“Ai naga duk anfi kashe mata kuɗi kuma muke wahalar kiwo, makarantar da takeyi kawai duk shekara kusan million 1 takeci muko sai wuyar tsiya da muke ci”.
Gaini ne yace.
“To ai kuma ita bata da shanu ko ɗaya kaikuma garke biyu kakeda naka na kanka haka kuma muma”.
Ladone ya ɗanyi murmushi bayan ya haɗiye lomar da yasa a baki yace.
“Ato gaya mishi kam”.
Ummey ce ta ɗan kalli Shatu tare da cewa.
“Kici abinci ki dena shan ruwan kunu ba rike miki ciki zaiyiba”.
Da sauri Junainah tace..
“A a Ummey ai Inna tana tasa an yanka zabbi zata gasa mana Adda karkici tuwo”.
Dariya sukayi baki ɗayansu dan duk kowa yasan Junainah tsakaninta da.
Nama akwai ƙauna.

Haka dai sukaci gaba da hira da dariya,
Hatta makiyayan gidan nasu wanda ba yan gidan bane saida suka shigo akayi ta hira da dariya dasu.
Suna cikin hirar ne yaro yayi sallama cewa Ba’ana yana kiran Aysha, cikin sauri Aysha ta konta tare da lumshe idonta, ganin hakane yasa Ummey cewa yaron.
“Ayyah kaje kace mishi yayi hakuri AYSHA har tayi bacci, in ba matsala yaje sai gobe, in kuma da matsala a tada ita”.
To yaron yace ya juya ya tafi.
Fitarshi bada daɗewa ba ya dawo,
Yace,.
“Yace a barta tayi baccinta gobe da safe zaizo”.
To sukace kana yaron ya fita ya tafi. Sukuwa sukaci gaba da hira.

Gashin zabbi mai kyau Inna tayi musu gashin da yaji haɗi, nan ta ware na maza ta basu kana ta ware nata da Ummey sannan ta bawa Aysha da Junainah, nan fa sukaci gaba da ci, suna hirarsu ta zumunci wanda ko yaushe haka suke duk daren kuma anan Bappa ke karantar dasu.

Bayan duk sun fara miƙewa da dare ya fara nisa, a hankali Bappa yace.
“Aysha kinyi baccine?”.
Cikin sauri ta miƙe zaune daga konciyar da tayi kanta na bisa cinyar Ummey, a hankali tace.
“A a Bappa idona biyu”.

Tashi zaune yayi tare da fuskantar ta, ganin haka yasa ta rarrafa a hankali ta iso gabanshi, cikin kulawa yace.
“Ya karatun naki?”.
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah Bappa karatu na tafiya yadda ya kamata”.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
“Baki da matsalar komai dai ko?”.
Da sauri tace.
“Babu matsalar komai Bappa na”.

“Masha ALLAH haka nake son ji, Allah ya miki al’barka dake da sauran ƴan uwanki baki ɗaya. Allah ya miki zaɓi da miji na gari”.
A hankali suka amsa da Amin Amin gaba ɗayansu.

Daga nan kuma yayi ta mata nasihar ta kama kanta,
Jin sanyi ya fara yawane yasa sukayi saida safe kowa ya nufi makoncinsa.

Yayinda a can cikin garima masu hira a dandali duk sun watse.

Al’walan konciya bacci sukayi kana suka shiga, ɗakin Ummey da yake mai girma da faɗi an laileyeshi da siminti da leda carpet, kana ga jere da gadajenta biyu masu kyau,
Ita da Junainah suna kan babban gadon ita kuwa Ummey tana kan ƙaramin gadon.
Hira sukaci gaba da yi irin hira ta tsakanin uwa da ƴarta, cikin sanyi tace.
“Aysha, kinji Hashimu ɗan Arɗo ya rasu ko?”.
Da sauri cikin razana AYSHA ta tashi zaune tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun Ummey banjiba yaushe ya rasu meya sameshi?”.
Ta jero tambayoyin a tare kana ga hawaye na kwaranya cikin sanyi Ummey tace.
“Kwanan ya rasu, yankan rago akayi mishi sai tsintar gawanshi akayi a burtali ana zaton Ɓachamawa ne suka kasheshi”.
Cikin shessheƙan kuka tace.
“Allah sarki Ya Hashimu Allah ya jiƙanka da rahama yasa ka huta, Allah ya saka maka duk wanda ya kasheka Allah ya toni asirinshi.”
Sai kuma ta konta tana kuka sosai saida tayi kamar 3 minute tana kuka kafin tace.
“Yanzu shike nan Ummey duk wanda zai soni ƙarshensa yankan rago?”.
Cikin yin ƙasa da murya Ummey tace.
“Ba dukaba in sha Allah akwai wanda zai soki ya kuma rayu dake bisa lfy”.
A hankali tace.
“Ummey wa zai soni a irin yadda kullum ya Ba’ana yake kara zama masafi mugu, wa zai tsira da tarkonshi?”.
Da sauri Ummey tace.
“Wanda yake mai ƙare rayuwarsa a amɓaton Allah da kekyawar zuciya.”
Kai kawai ta kife tana mai kukan rasuwar Yaya Hashimun ta, a haka dai sukayi ta hira har bacci ya sacesu.

A can cikin masarautar Joɗa kuwa.
Bayan anyi sallan ishane, Sheykh ya fito cikin shirinsa na tafiya, riga da wondon yaɗin wagambarine a jikinsa sai bakar alkyebbarsa dayasa kana sai hiraminshi fari da kuma bakin tarden dake saman kanshi.
Sai takalman sarautar da ya saka, suma farare kalar hiraminshi.
Jamil ne ke biye dashi a baya yana riƙe da ƴar madai-daiciyar jakar Hamman nasu, kana hannunshi ɗaya na riƙe da jakar System ɗinshi, shi kuwa Sheykh woyoyinsh ya zura a al’jihunshi.

Tare suka fito, a mashigar ƙofarshi nan sukayi kiciɓis da Jalal, da Jakadiyarsu, cikin muryar da bata cika fara’aba Jalal yace.
“Please Hamma Jabeer, dan Allah karka daɗe”.
Kafaɗanshi ya dafa tare da cewa.
“In sha Allah bazan daɗeba Jalaluddin, ka kula da kanka da Yah Jafar”.
Kanshi ya gyaɗa alamar to, Jakadiya kuwa, ido ta zuma musu tana jin so da ƙaunar yaran kamar itace ta haifesu a cikinta.
Cikin girmamawa Sheykh yace.
“Ummi bari inje in sallami Yaya Jafar”.
To tace kana ta juya ta nufi sashin, Hajia Fatima, tsakar gidan Maigirma Habibullah.

Su kuwa suna shiga a falo suka samu Yayan nasu da iyalanshi, a hankali Sheykh ya ƙaraso gaban ɗan uwan nashi, cikin sanyi yace.
“Ya Jafar zan tafi Leddi julɓe Sitti ta nemi muje gidansu, can ƙasar saudia, Abba ne da kanshi yace inje badon hakaba babu inda zanje in barka a haka, zanje ƙasa mai tsarki tushen mahaifiyarmu da kakarmu da take jininsu, in sha Allah zan nemi al’farman a buɗe min ka’aba zan shiga har ciki inyi maka addu’o’in samun lfy, kuma bazan daɗe ba zan dawo kajiko Ya Jafar?”.
Bai kulashiba kana kuma bai bar karatun da yakeyiba, sai dai hawaye daya fara zubdawa a jere-a jere. Jamil kam juyawa yayi ya fita da jakar ɗan uwan nashi dan yasan zaiyi kuka.

Ita kuwa Juwairiyya cikin sanyi tace.
“Babu komai Sheykh Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy in sha Allah zanyi ta kula dashi yadda ya kamata”.
Jalal kuwa tattauna laɓɓa shi kawai yake tamkar zai hudasu, tabbas sunada ciwo a cikin zuƙatansu musamman Sheykh da yasan shike ɗaukan damuwarsu kab harda ta mahaifiyarsu”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button