GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jalal ne da Hibba suka miƙa tare da cewa.
“Mu zamu tafi.”
Bai kulasu ba, Jalal ne ya ɗan matsoshi tare da cewa.
“Umaymah tace ka kai mata Ɗiyarta taga ya ta kwana da jikin”.
Kai ya gyaɗa alamar to.
kana Hibba ta kalleta tare da cewa.
“Aunty Aysha sai kin dawo, Allah ya ƙara sauƙin”.
Amin tace tana gyara zamanta tare da jawo ƴar jakar kayan da Hibba ta kawo mata. Wai na anko ɗin fansan idon da za’ayi.

Su kuma nan suka fita.

Suna fita, ya miƙe ya rufe ƙofar, kana ya dawo ya hau kan gado ya kwanta.
Da ido ta bishi tare da cewa.
“Yah Sheykh gado kuma to yaushe zamu tafi ko inbi su Hibba kawai ne?”.
Lumshe idonshi yayi alamun bacci zaiyi, a hankali tace.
“Dole ne kullum sai kayi baccin tsakanin azahar da la’asar ɗin nan”. Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh.
kana ya juya mata baya.

Dole itama ɗin ta hau ta kwanta, tana konciya ya jawota jikinshi nan take sukayi bacci.

Ƙarfe uku da minti arba’in da biyar ya farka, da sauri ya zareta daga jikinshi kana ya shiga bathroom, wonka yayi fes kana yayi al’wala ya fito.
zaune ya sameta bakin gado.
“Tashi kiyi wonka mu tafi tunda ke bakya cikin masuyin salla”.
Cikin sanyi tace.
“Ah ina cikin masuyin salla mana”.
Kai ya gyaɗa yana zura tattausan al’kyabbar shi. Yace.
“Eh amman ni dai tun jiya banga kinyi salla ba”.
Cikin rashin fahimtar wayon da yake mata tace.
“In Sha Allah gobe dai da safe ai zan fara”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“To tashi kiyi wonka kafin inyi sallan”.
To tace kana ta miƙe ta shiga Bathroom da ƴar jakar kayanta.
Shi kuwa ya kabbarta sallan la’asar.

A cikin bathroom ɗin ta canza kayanta bayan ta kimtsa jikinta.
Kana ta ninke wanda ta cire ta saka a ciki ta feshe jikinta da turarenta mai sanyin ƙamshi, sannan ta fito.

Zaune ta sameshi bisa sallayar yasa System ɗinshi a gaba ya maida hankalinshi kab kanta. Bisa alamun wani abu mai tarin mahimmanci yakeyi.
Dan gaba ɗaya yatsun hannunshi aiki sukeyi sai kwayar idanunshi da yake jujjuyawa kan screen ɗin na’ura. Yanayi kuma yana motsa lips ɗinshi alamun still kuma tasbihi yakeyi bincikar number da ake tura masa text a rufe yakeyi yadda zai samu ya buɗe layin yabi diddiginshi.
A hankali ta kalleshi da kyau, kana ta kalli kayanshi da ya cire ɗauka tayi ta ninninkesu ninkewa mai kyau, tasa a ƴar jakar ta zuge zip ta rufe.
Sannan ta koma gefenshi can ta zauna bayanshi.
Cikin sanyi tace.
“Ni dai banga wayata ba”.
Bai kulata ba, domin aikin da yakeyi ya tunzura mishi nitsuwa.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah to dan Allah. Sammin wayarka in yi kira”.
Tura mata wayarshi dake gefenshi yayi sabida ya samu ta rabu dashi dan tana raba mishi hankali”.
Ɗaukar wayar tayi sai kuma taga akwai security code a jiki.
Matsoshi tayi da mamaki dan tasan akwai woyoyin shi biyu data taɓa riƙewa basa da security, jujjuya yar wayar tayi ganin yar micilace kuma harda liƙa mata matakan tsaro, taɓe baki tayi tare da cewa.
“Me code ɗin buɗe shi”.
“Mamey”. Yace mata ba tare da ya kalleta ba.
jujjuya yar mitsitsiyar wayar tayi a tafin hannunta, contacts ta danna da nufin ta ɗan duba ko da number sai ta samu nanma a garƙame yake.
Ikon Allah tace a hankali kana ta danna. Phone na ma kirib yake, cike da mamaki tace.
“Wayarfa tako ina ansa mata kan tsaro”.
Da sauri ya juyo ya kalli wayar da ke hannunta. Hannunshi yasa ya amshi wayar da sauri tare da zurata a al’jihunsa kana ya yasa kan yatsunshi ya ɗan bugi goshinsa tare da kwaɓe fuska kana ya kalleta cike da alamun damuwa yace.
“Kai Alhamdulillah, Allah na gode maka daka jarabceni da wannan fitinenneyar yarinya Aish mata, kinzo kin tasani gaba da surutu, kuma kina gani aiki nakeyi, ko so kike na ki rikitamin tunani ne”.
Kanta ta langoɓar tare da kwaɓe fuska tace.
“A a, Ni kawai wayata zan kira”.
Cikin zubawa lips ɗinta ido yace.
“Ba kin barta a motaba”.
Da sauri tace.
“Laah hakafa ni na manta ma”.
Kanshi ya gyaɗa kana ya gyara zamanshi ya fuskanci System ɗin nasa.
Gefenshi ta ɗan kalla tare da cewa.
“Yah Sheykh!”.
Shiru bai amsa ba yaci gaba da aikinshi.
a hankali ta kuma cewa.
“Yah Sheykh!!”.
Bai amsaba bai kalleta ba.
A karo na huɗu ta kuma kiranshi.
“Yah Sheykhhhh”. Ta ƙarashe kiran murya can ƙasa da alamun bacci ya fara kamata, a hankali ya ɗan juyo kwayar idanunshi ya kalli inda take.
Cikin lumshe ido tace.
“Mu tafi mana, za’ayi fansan ido da bamu jeba”.
Kanshi ya gyaɗa alamun to, daga nan ya meda kai yaci gaba da aiki.

A can gida kuwa, tuni anyi fansan idon amarya da ango gaba ɗaya an gama komi da komai.

Har an fara shirya farfajiyar Side ɗin Umaymah wanda anan za’ayi shagalin mother’s day ɗin.
An gyara wurin an kimtsa an shirya komai yadda ya kamata.

Ƙarfe biyar dai-dai duk an gama shirya amarya cikin shiga ta al’farma, hakama ango Haroon ɗan ayi.
Aunty Rahma kuwa tasa mabusan masarauta da makaɗa yan kakaki da tambura da al’gaita duk sun shiryawa shagalin tunda abu na jinin sarauta ai dole a gwada iyawar.

Safiyyah ce ta shigo bedroom ɗin Umaymah inda ta wuce zugan ƙawayen ta duk suna falo cikin kwalliyar ƙasaitattun mata, matsowa kusa da Umaymah tayi tare da cewa.
“Umaymah Aysha fa har yanzu fa Hamma Jabeer bai kawota ba,”.
Cikin sauri Aunty Juwairiyya tace.
“Dan Allah Umaymah kirashi ya kawota Mamma tace su Haroon ma bazasu fitoba sai sun iso”.
Murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
“Uhummm Jazlaan fa ba son waɗannan abubuwan yake ba. Bana son tirsasa masa yin abinda baya so ku kuma kun dage, ala dole tunda bikinsa ba shiri ba’a zoba yanzu sai kunyi shagalin”.
Ummi ce ta ɗanyi murmushi tare da cewa.
“To bari ni in kirashi”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Yauwa yama fi min”.
Ita kuwa Ummi wayarta ta kara a kunne bayan ta danna mishi kira.
Bugu biyu ana uku taji ya katse kiran.
Jim kaɗan kuwa sai ga kiranshi.
Bayan sun gaisane sai kuma ta ɗan yi shiru.
Jin hakane ya sashi cewa.
“Na’am Ummi meke faruwa ne?”.
Cikin tausasa murya tace.
“Eh dama duk an gama shirine ku kaɗai ake jira”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Haroon dake ta murmushi kana a hankali yace.
“Ummi ai mun dawo, yanzu muka shigo, bata iso wurinku bane?”.
Da sauri Ummi ta juyo ta kalli bakin ƙofar jin muryar, Aysha tana sallama.
“Yauwa gata ta iso”. Ta faɗa mishi tare da katse kiran”.
Safiyyah ce tayi sauri kamo hannun Aysha tare da cewa.
“Yauwa zo muje ɗakin Hibba ki shirya”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Safiyyah barni mu gaisa dasu Umaymah mana”.
Murmushi Mamma da yanzu ta shigo tayi tare da cewa.
“Uhumm Safiyyah kuwa da gaggawa”.
Cikin ladab da biyayya ta rusuna ta gaidasu kana, Safiyyah ta jata suka tafi ɗakin Hibba.

A can Side ɗin dasu Haroon suke kuwa, Ibrahim ne ya ɗauko wasu tattausan kaya masu masifar kyau da taushi, yadin Getzner ne mai ɗan karen kyau kalar pink guava mai masifar kyau, riga da wonɗone da babbar riga gariya an watsawa mats aiki da surfani mint green color irin mai sheƙin nan, sai baƙin hula mai ɗan karen kyau shima da ratsin mint green da fari,
amsa yayi tare da kallon Haroon da Ibrahim ɗin sosai kayan sukayi masifar musu kyau, kanshi ya ɗan juya ya kalli takalman da Ibrahim ke nuna mishi baƙaƙene irin masu sheƙin fatar nanne.
Fita sukayi, dan bashi wuri yasa kayan.

Sosai kayan sukayi masifar amsar fatar jikinshi da surarshi ya fito ras balaraben asali. Komai.
Hular ta zauna ras a kanshi, gefe da gefen kan nashi duk tattausan sumanshi ya ɗan fito, Especially ƙeyarshi da sumar ta kwanta lib kana farar fatarshi tayi ras ciki sajenshi da girarshi komai tubar kalla masha ALLAH.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button