A hankali ya taƙo ya fito falo.
Nan take su Haroon Suka miƙe, kasan cewar duk abokansu sun tafi sun watse tunda bikin maza ya ƙare, sai su uku suka rage sai kuma su Ya Hisham, Affan, Jamil, Jalal, Azeez, Sadiq, imran, Kabir, Kamal, Sulaiman, da dai sauran ƴan uwa da wasu makusanta.
Haka suka fito a tare,
Tuni harabar wurin ta cika tayi maƙil manyan matane tako ina matan sarakuna da manyan yan kasuwa da siyasa, aminan Umaymah da matan abokon Abbansu Haroon, sabida ranar tasuce ko wacce tasan Umaymah da Jazlaan ɗin ta sun san soyayyarsa a ranta fiye data Haroon ce sun kuwa san biyayyarsa gareta.
Shiru wurin babu hayaniya, hakane yasa Sheykh bai damuba dan baiga abun kiɗe-kiɗen da ya tsana ba.
Kuma gashi babu wasu taron maza, duk ƙannenshi ne.
Sai kuma iyayenshi, duk da har ga Allah har ransa baiso wannan tsarin ba sai dai bisa dole Umaymah’nshi da Abba Hajia Mama da Ummi suka tirsasashi.
Kuma suma basu san Aunty Rahma ta tsara kayan kiɗa da bushe-bushen sarewa da al’gaitanba.
“To ma in banda su Umaymah ya za’ayi ayi abu salam”.
inji Aunty Rahma da take tare da mabusan. Hibba ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
“Ai kuwa Hamma Jabeer zaiyi faɗa”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Me ruwana”.
Sai kuma ta juyo ta kallesu tare da cewa.
“Kuna ganin amaren sun fito ku fara buga tambura da kakaki ayi bikin gidajen sarakuna haka Salam”.
Ai kuwa bata ida rufe baki ba.
Aunty Juwairiyya ta buɗe ƙofar babban falon Umaymah ta fito ita da Jazrah.
Jannart na bayanta Aysha na bayanta.
Sai kuma Safiyyah ta biyosu.
Wani irin murmushi da gyaɗa kai Aunty Rahma tayi lokacin da taji an saki sautin tamburan.
“Uhum yauwa haka mana asan ana biki kam”.
Ta ƙarashe mgnar tana tahowo kusa dasu Umaymah cike da mamaki suke kallonta ita kuwa tana musu murmushi Yar autar Sitti kenan.
A hankali Aysha ta lumshe idonta sabida wani irin yam da taji tsikar jikinta na badawa.
Hannun Safiyyah dake riƙe da nata ta ɗan juya itama ta riƙe.
A hankali sukaci gaba da taku cikin irin wasu masifaffun kaya masu masifar kyau, irin dai kayyakin nan da yan gayu ke sawa mai shara-sharan tattausan yadin cikin pink guava ne, kana net ɗin saman kuwa mint green ne. Anyi ɗinkunan dogayen riguna masu kyau cib cib da jikinsu.
Sai wasu takalma masu ɗan karen tsini kalar azurfa da yar karamar fosa sai a goggoronsu shina kolon takalman. Sosai sukayi kyau,
A hankali suke shigowa cikin taron ana mc ɗin yana mai bin waƙar da ya saki ta.
“Ku-martsa-ku-martsa ga amarya ta iso”.
Wani irin murmushi mai cike da jin daɗi Umaymah tayi kana ta kalli Hajia Mama dake gefenta tace.
“Kinga surkanki masha Allah”.
Uhummmm tace tare da kaɗa ƙafarta.
Sheykh kuwa wani irin rumtse idanunshi yayi lokacin da yaji an saki kuɗin badujalan injishi da faɗin.
Tsayawa yayi cak ba tare da ya ƙara koda taku ɗaya ba.
Haroon da sauran tawagar ma tsayuwa sukayi, Ibrahim ne ya ƙara matsoshi tare da cewa.
“Dan Allah kayi haƙuri mu ƙarasa koda 5 minute ne kayi sai ka tashi. Dan Allah muje Umaymah zataji daɗin hakan”.
Cikin takaici yace.
“Bazan jeb..”.
Bai rufe bakinshi ba yaji an riƙe hannunshi na dama da sauri ya juyo, Aunty Hafsat Mamma kenan
Cikin sanyin murya tace.
“Dan Allah Muhammad muje na roƙi wannan al’farmar kayiwa Allah da Manzonsa muje, koda zaman daƙiƙu ukune kayi. Kada mu kunyata wurin aminan Umaymah”.
Ya zaiyi sun gama ɗaureshi da jijiyoyin jikinsa,
Wani nannauyan ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi kana ya gyaɗa kanshi yaci gaba da tafiya.
Still Mamma na rike da hannunshi a haka har suka iso, farfajiyar wurin.
Har gaban kujeru inda aka shirya wurin zamansu taje ta ajiyeshi kusa da Aysha, tuni shi Haroon ya zauna kusa da amaryarsa.
Shi kuwa Ibrahim shima ya zauna gefen Safiyyarshi.
Kana su Affan kuwa duk suka zauna tare dasu Jazrah da Azeema da Hibba da sauran cousin sisters ɗin su.
Mc ne ya fara shelan Amare su fito, surkansu su nuna musu gata.
A hankali Jannart ta miƙe tsaye sabida ita duk yan uwanta ne, ita kuwa Aysha gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi Allah ya sani ita dai tana tsoron idon mutane, ganin bata miƙe tsayeba ne, yasa Aunty Rahma yin sauri ta iso garesu sunkuyowa tayi ta kamo hannun Aysha tana miƙar da ita tsaye.
Ɗan juyowa tayi ta kalli Sheykh.
Cikin tsuke fuskarsa yace.
“Zabiya kiyi a hankali dai dan dujal da ganga yake baiyana tsoro nake jiye miki kada ki zama cikin mabiyansa”.
Murmushi tayi kana taja hannun Aysha suka shiga cikin taron tare da Jannart.
Wani sassanyan waƙa aka saki.
Kana su Hibba suka taso da sauri suna feffesa turare mai ƙamshi kana da bada wani kala na musamman.
Cikin tsananin jin daɗi Umaymah, Mamma Aunty Rahma, Hajia Mama. Suka fito bisa dandamali buɗe bakin jakukkunansu sukayi, wani irin liƙi na musamman sukeyiwa amarenta tamkar babu talauci.
Gaba ɗayansu da 1-1k suke liƙi cikin ƙasaita.
Kusan 5 minute sukayi suna liƙi kana MC yace su koma su zauna su huta.
Wani irin banbaraƙwai Sheykh yake ganin abun sabida shi dai a iya tsawon tarihin rayuwarsa bai taɓa zuwa ba, kuma shi bai taɓa ganin tsarin wannan bidi’o’inba.
Ina dalili wannan abun, ai ko basuyi hakaba tabbas an san dai suna cikin farin cikin.
Baya zamansu kamar da mintuna 3 MC ya kuma kiran amare dasu fito tsakiyar taron.
A hankali suka miƙe tsaye,
kana suka fara tafiya a hankali,
wani irin masifeffen zubawa tsikar jikin Aysha yayi tare da bugawan ƙirji da ƙarfi.
Sabida sarewa da al’gaita da tamburan da kakakin da aka sake gaba ɗaya a lokaci ɗaya.
A hankali dai suke takowa, suna nufo tsakiyar taron.
Nan MC ya kuma cewa yana buƙatar uwar angwayen Gimbiya Khadijah Umaymah kenan da tawagar ƙawayenta.
A nitse Umaymah ta miƙe kana Su Hajia Kubra, Hajia Rakiya, Gimbiya Ruƙayya Hajia Maimunatu sai kuma Ummi da dai sauransu.
Suna shigowa Umaymah taci gaba da yin liƙin 1-1k duk sauran kuma 5-500 suka fara miƙa wa.
Yadda ake busan sarewa ne yake ta’azzara tashin tsikar jikinta da kuma bugawan zuciya.
Busar sarewan yakeyi mai busar cike da iyawa da ƙwarewa da bajinta,.
Kana ga tamburan da aketa dokawa, a hankali Aysha ta sunkuyar da kanta tare da rumtse idanunta jin naman jikinta ya fara tsuma da karkarwa.
Cikin haka MC ya buɗe muryarshi da azaban ƙarfi tare da cewa.
“In kaji tambura sai Babbar fada kakaki da al’gaita mabusar masarauta ne.
ai duk daren daɗewar tsuntsu a sararin samani bai kai tala-talaba kaga jefa garma a caɓe sai ɗan gada kiɗan shantu sai mata.
Ina angwayen Gimbiya Aysha da Gimbiya Jannart fili dominku ku shigo gaban iyayenku”.
Wani irin haɗe fuska Sheykh yayi to waima ta yaya ta ina zai fara.
Haroon kuwa tuni ya miƙe dan gaba ɗaya tsikar jikinshi tashi yakeyi sabida kirarin da akayi musu.
Hannunshi yasa ya kamo hannun Sheykh kana yaja,
Ƙin miƙewa yayi. Sai dai kuma ya ɗago kanshi ya kalli can tsakiyar taron tsakanin kafaɗun Ummi da Hajia Kubra ya hango Aysha, Ido ya zuwa fuskarta da kyau, kasan cewar shi a zaune yake ita kuma a tsaye take ta kuma rusunar da kanta yasa yana kallon fuskarta ras.
Cike da mamaki Haroon ya kalleshi ganin ya miƙe ya kuma nufi wurin.
juyawa yayi kana yabi bayanshi suka fara taku a tare.
MC ne ya ɗan dakada daga kirarin da yakeyi kana ya buɗe murya tare da cewa.
“Gimbiya Khadijah Umaymah ga yaranki angwayen a bayanki a basu wuri su ƙarasa kusa da amaren.
Da sauri Umaymah da Ummi suka ɗan ja da baya suka basu hanya.
A hankali Haroon ya matso kusa da Jannart.
wani sabon liƙi Umaymah da ƙawayenta suka fara, shi kuwa Sheykh a hankali yake ƙara matso inda Aysha take tsaye.
Ita kuwa Aysha wani irin tsuma da karkarwa jikin ta yakeyi tuni numfashinta ya fara fizga.
Ido Sheykh ya zubawa goshinta ganin yadda zufa ta tsastsafo mata, har tana kwaranya ta gefen kunnenta.
A hankali ya ƙara matsota wanda hakan yasa mutane zaton wani salone kawai nashi.
Haka yasa Mamma da Aunty Rahma da Hajia Mama suka shigo suma aka ci gaba da liƙin dasu.