GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Aysha haka nan yau take jin bege da kewar ahlinta ta kasa tsaida hawayenta Especially Ahlin Abboi.

Tana tuno Didenta su Yah Al’ameen da Innayinta.
Bappa’nta Ummeynta, Ya Giɗi, Ya Seyo, Ya Gaini, da Ya Lado.
Shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata ganin yadda hawaye keta shatata a fuskarta babu ƙaƙƙautawa.
Remote ɗin A/C’n dake hannunshi ya meda a masaƙalinshi kana, bakin ƙofar ya koma ya rufe ƙofar kana yazo ya wuce.
Side ɗinsa.

Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
“To nan dai Side dinmu Sara ta gyara mana komai amman nasan Side ɗin Sheykh ba a share yakeba, tunda tare muka dawo da Jamil, dan haka tashi kije ki ɗan kimtsa mishi bedroom ɗin”.
Miƙewa tayi itama tare da share hawayenta kana a hankali tace.
“Naji kafin jirginmu ya tashi yayi mgn da Affan yana ce mishi ya share mishi ɗakin ya amshi key a wurin Gimbiya Aminatu”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh hakafa ni na mance ai Affan na nan”.
Falon Aysha suka nufa, suna shiga kowa ta nufi ɗaukinta.

Ummi Al’wala tayi kana tazo ta kwanta.

Ita kuwa Aysha tana shiga, ta ajiye jakarta gefe kana ta faɗa kan gado ta kwanta a kife, ta kifa kanta bisa pillow kuka mai ƙarfine ya kwabce mata, sabida suya da zafin da zuciyarta keyi na tuno ƴan uwanta da suka ɓace.
Duk da kuma kontar mata hankali da Bappa keyi na cewa anji lbrinsu har an gansu.

Kuka tayi tayi sosai wanda ita kanta bata san tsawon lokacin da tayi tana kukanba.

Sai ƙarfe uku dai-dai ta samu bacci ya saceta.

Shi kuwa Sheykh yana shiga,
yayi ajiyan numfashin sabida ya samu komai tsab-tsab a gyare a killace ko ina na ƙamshi.
Kasan cewar ana zabga zafin da rashin ruwan sama da akayi kwanaki ba’ayi bane yasa, garin ɗinkewa da zafi.
Gudun A/C’n ya ƙara kana ya ajiye jakarshi cikin drower’nshi.
Rage kayan jikinshi yayi kana ya shiga bathroom wonka yayi tare da al’wala sannan ya kimsa cikin tattausan rigan bacci riga da dogon wondo ne.

Yana fitowa ya rage hasken ɗakin kana yazo ya zauna bakin gadon.
Ya buɗe hannunshi ya ɗagasu sama alamun zaiyi addu’o’in kwanciya baccine, kiran Haroon ya shiga wayarsa.
Yasan idan ba ɗagawa yayiba Haroon ba barinshi zaiba, hakane yasa ya amsa kiran da sauri.
“Alhamdulillah mun iso lfy yanzuma bacci zan kwanta”.
Ya faɗa da sauri. Dariya Haroon yayi tare da cewa.
“Ya haka dai malam kamar korata kakeyi, nima sabon ango banma hakaba sai kai tsohon ango, to a huta gajiyar hanya, ni yanzu zan kama hanyar fatauci ne”.
Wani gajeren tsaki yaja tare da katse kiran.
Dariya Haroon yayi kana ya jawo hannun Jannart ɗinshi suka nufi ɗauki shi.

Shi kuwa Sheykh addu’a yayi ya tofa a tafin hannunsa ya shafe jikinsa duka kana ya kwanta bisa hannun damanshi.
Lumshe ido yayi tare da sauƙe numfashi kana ya fara tasbihi kamar yadda ya saba, lokaci ɗaya bacci ya samu nasarar ɗaukeshi.

Haka sukayi bacci a gajiye gaba ɗayansu.

Ƙarfe biyar saura kwata, ya fito cikin shirin tafiya masallacin Masarautar Joɗa domin limancin sallan asuba.
Da sauri ya buɗe ƙofar kana ya fita sannan yaja ƙofar ya rufe.

Dai-dai lokacin Ummi kuwa ta farka daga baccin da ya samu nasarar sata makara, da sauri ta miƙa bathroom ta faɗa al’wala tayi kana ta fito.

Aysha kuwa can cikin bacci take cin sautin karatun Alqur’ani da yakeyi na suratul Al-Burooj. Sosai sautin muryarsa ke ratsa ko ina na cikin masarautar Joɗa, a hankali take buɗe kwayar idanunta wadanda bacci da kukan da tayi ya kumburasu suka yi wani ɗan ja haka mai gauraye da farin.
meda idon tayi ta lumshe jin yadda yaja tsakiyar aya ta 8.
Yadda yaja illahhhhhhhh ɗin cikin taƙib mai ja shida, kana ya maida numfashi.
Saida taji tsikar jikinta na tashi yar-yar, da sauri ta buɗe idonta kana miƙa zaune, cikin kasala da yanayin bacci bai isheta ba sam ta miƙe tsaye ta faɗa bathroom.
Wonka tayi da ruwan sanyi sabida wani irin zafin da ake zabgawa, kai baka ce tsakiyar damuna bace.
Al’wala tayi kana ta fito, wata tattausar doguwar riga ta zura a jikinta, kana tasa hijabi.
Sannan ta shimfiɗa sallayarta.

Bayan ta idar da sallan ta fara du’a’u Azkar tanayi tana lumshe idonta sabisa sam da baccin bai isheta ba.
Koda ta ida addu’o’in ta shafa, a hankali ta miƙa ta ninke sallayar da hijabin kana ta ƙara ƙarfin A/C’n sannan ta kashe wutan ɗakin ta koma ta konta,
Mustsuke idon tayi jin har wani yaji-yaji suke mata, gyara kwanciyar ta tayi take kuwa baccin yayi awon gaba da ita.

Bakwai dai-dai Ummi ta fito asalin babban falon.

Kitchen ta nufa jiyo motsi a ciki alamun Sara tazo kenan.

Tana shiga kuwa ta samu Sara na fere Arish ga kuwa ruwan tea ta ɗora ta zuba citta kanamfari sunata ƙamshi.
“Ina kwana Ummi”.

“Lfy lau Alhamdulillah Sara mun sameku lfy”.

“Alhamdulillah”.

“Masha Allah”. Tace tana haurawa saman steps ɗin da zasu sadata da inda freezer yake.
Buɗewa tayi, zabbi uku ta ɗauko kana ta sasu a wata ƴar madai-daiciyar roba.
Kana ta dawo jikin sink wuƙa ta ɗauko sannan tazo ta fara gyarawa.

Sheykh kuwa karfe bakwai da kwata ya fito cikin wasu tattausan farin yaɗin boyel riga da wondo da malum-malum yadin irin mai gidan dara-daran nanne. An watsa gariyar aiki da surfani Royal blue mai masifar kyau, hular kansa itama farace mai rashin Royal blue.
Hakama takalmin shi half cover suma Royal blue ne masu azabar kyau, sajenshi ya kwanta lib gwanin burgewa.
Jakar System ɗinshi ya rataya a kafaɗarshi ta dama, kana ya fito ya nufi Valli Hospital ɗinshi.

Ƙarfe tara saura kwata Jalal, Jamil, Ya Jafar, Imran suka shigo falon.
Jamil ne ya lumshe idanunshi tare dacewa.
“Wow Ummi wannan ƙamshin na girki shine ƙungiyar yunwa, duk yawunmu ya tsinke.”
Dariya Ummi dake Dinning area tana jera Foodflaks bisa table ɗin tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kuwa kun iso a Sa’a an gama kenan kun iso, maza ku ƙara so nan.”
Jalal dake riƙe da hannun Ya Jafar dake karanta Suratul Al-monafiqoon a hankali yake motsa laɓɓansa saɓanin da da yakanyi da ƙarfi.

Zama sukayi baki ɗayansu, kana suka fara yin karin kumallon da kekkyawan girkin Ummi.

Ita kuwa Ummi kitchen ta koma, ta sawa Sara nasu, kana tace.
“Yauwa kije ki ɗan huta sai shabiyu sai kizo mu ɗaura na rana”.
Ɗaukan kularta tayi kana ta fita ta tafi.

Ita kuwa Ummi ɗakin Aysha ta nufa jinta shiru-shiru bata fiton ba.
Sallama tayi a bakin ƙofar, shirun da tajine yasata ƙarawa, still ba amsa,
Sallama ta uku tayi kana ta tura ƙofar a hankali sannan ta kutsa kai ciki.
Can ta hango Aysha konce lib tana sharan bacci cikin salama, murmushi tayi kana ta juya ta koma falon ta ɗebi nata abincin taci kana ta koma ɗakinta dan yin walaha.
Su Jalal kuwa sai goma da rabi suka bar falon, ya zama shiru.
Bayan fitansun ne Ummi ta fito ta kimtsa Dinning table tsab, sannan ta zauna a falon.

Sha ɗaya dai-dai Aysha ta farka daga baccinta mai cike da mafarkai, bathroom ta kuma shiga, ruwa ta watsa sabida zafin da akeyi.
Tana fitowa ta zauna gaban dreesing mirror body lotion ɗin ta mai ɗan karen kanshi ta shafa, kana ta ɗanyi light mackup akan Kekkyawar fuskarta tayi kyau sosai kuwa, wata atamfar Super Engla mai kyau, green, red, and white color, yanada zanen tsintsiya a jikinshi ɗinkin doguwar rigace takoyi dabas a jikinta gwanin burgewa, ɗan kwalin ta murza a kanta irin ɗaurin mai stpes ɗinnan sosai fuskarta ta fito ras, ta kitse jelar gashinta ta konto bayanta, gyale ja ta yafa turare ta fesa, sannan ta fito ta nufi falon tana ɗan hamma alamun yunwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button