GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ummi na ganinta ta mike zaune tare da cewa.
“Sai yanzu”.
Gefen Ummi ta zauna a ƙasa bisa carpet tare da cewa.
“Eh Ummi gajiya. Ina kwana”.
Fuska a sake tace.
“Lfy lau Alhamdulillah gsky kam kinsha bacci”.
Kai ta rausayar tare da yin wata hammar, miƙewa Ummi tayi ba tare da tayi mgna ba, ƴan kananun Foodflaks ɗin da ta zuba mata breakfast ɗin ta jera a tray da flaks ɗin tea da plate spoon and cup. Gabanta ta ajiye kana tace.
“Yauwa ga abinci maza kici ki shiga kitchen ki shiryawa Sheykh nasa karin dan inaga ya tafi asibitinshi”.
Jawo tray’n tayi tare da cewa.
“Toh”. Soyeyyen dankali da kwai ta zuba a plate kana ta haɗa tea sannan ta ɗan sa ferfesun zabbin kaɗan kana ta faraci suna, hirar bikin haron.
A nan Safiyyah ma ta kira nan akayi yar hira da ita.

12:00 Sara ta shigo.
“Ina kwana Aunty”. Tace tana kallon Aysha, cikin sakin fuska tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Sara ya gida”.
Alhamdulillah itama tace.
Tray’n ta tura mata gabanta tare da cewa.
“Yauwa muje kitchen ki ɗan tayani aiki Arish zaki ɗan fere min kaɗan. Sai ki gyara min kayan miya.”
To tace tana muƙewa rabi bayanta.

Itama Ummi bayansu tabi, ita ta fara aikin Lunch su kuma suna aikin na Sheykh.
Jan nama mai kyau ta ɗiba tayi musu yanka yan mitsi-mitsi ta wonkesu kana ta juyesu a tukunya, tasa al’basa da Curry Maggi kanamfari citta tafarnuwa kaɗan da dai sauran kayan ɗan-ɗano ta rufe tukunyar bayan ta ɗaura a wuta,
Bayan an fere mata dankalin ne, ta amsheshi tayi mishi ƙananun yanka, sannan ta amshi tattasai, attaruhu da al’basa, da Sara ta jajjaga mata.
Ta ajiye a gefe tuni naman nan yaketa sulala yana zuba ƙamshi yayi lugub.
juye naman da ruwan tayi a wani ɗan kwano na tangaram kana tasa mai a tukunyar ta meda kan wuta.
yankekken al’basa ta watsa a man take ya baza ƙamshi a Side ɗin gaba ɗaya, kayan miyar tasa ta soya ya soyu da kay, sannan tasa ɗauki ruwan naman nan da naman ta juye ciki.
Kana ta rufe sannan ta ɗan ɗauko maggi da gishiri ɗan ƙanƙani ta watsa ciki.
Sannan ta rufe, wata ƴar ƙaramar tukunya ta ɗaura tasa ruwa kaɗan kana tasa kwai guda bakwai ciki kana ta rufe.
Sannan ta ɗauko sufageti rabin ledar ta karya tasa a cikin haɗin tukunyar.
tare da watsa dankalin nan a ciki sannan ta maida ta rufe.

Tukunyar kwan nan ta buɗe ganin sun dafu ne yasa ta sauƙesu, ta tsanesu kana ta sasu a plate.
ɗan motsa taliyar da dankalin tayi kai ta gyaɗa ganin yayi yadda takeso naman ya wadaci girkin sosai,
Kwan ta fara ɓarewa, saida ta baresu fes kana, ta rufesu gefe, buɗe tukunyar taliyar tayi ganin yayi dai-dai da Dan ruwa-ruwane yasa ta ɗauki caras da al’basan da ta yanka tare da dafaffan kwai ɗin ta sasu ciki.
sannan ta rufe ɓol-ɓol yake wani kekkyawan ɓararraka.
Wata kekkyawar Foodflaks mai marfin glass ta ɗauko ta fara ɗiban taliyar gefe-gefe tana sawa a wani kekkyawan kwano gudun kada garin sawa a Foodflaks ɗin ya ɗan ɓata kular, daga cikin kwanon ne ta juye a kular sannan ta dawo ta yaɗe al’basa da caras da kwan da namomin ta jerasu saman kular kana tasa marfin ta rufe.
Sosai tsarin yadda tasa abincin yayi masifar kyau.
Sauran na tukunyar ta sawa Sara a plate da kwai ɗaya da Nama dasu karas ɗin sauran kuma ta sawa Ummi shi a wata ƴar kula.
Cikin Murmushin Ummi tace.
“Gsky kam Aysha koda a ƙoshe nake zanci girkin nan”.
Murmushi tayi tare da ɗauko lfaks ɗinshi da Ummi tasa mishi tea, kasan cewar ɗan ƙaramine yasa ta jerashi kan tray kusa da kular,
ferfesun da Ummi tayi ta ɗan ɗuma tasa mishi a ƙaramar kula, kana tasa plate, cup, tea spoon and fork. ta kimtsa komai, kana ta tura tray’n can gefe, sannan ta matso kusa da Ummi tana cewa.
“Ummi miyan me zakiyi mana”.
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Ɗanyar ƙuɓewa”.
Da sauri tace.
“Ummi yaushe zamuyi miyar kase”.
Cikin dariya tace.
“In sha Allah gobe zamuyi”.
Allah ya kaimu tace cikin jin daɗi.

A hankali yayi parking gab da bakin ƙofar falon nasu, Allah ya sani ya gaji ga yunwa.
A hankali ya fito, dai-dai lokacin kuma Jamil da Affan suka iso wurin.
Affan ne yasa hannun ya amsar mishi jakar system ɗinshi.
Tare da ce mishi.
“Sannu da dawowa Malam”.
Kai ya gyaɗa musu, yayi gaba kana suka bishi a baya.
Da sallama a bakinshi ya shiga.
Suna shiga kai tsaye Side ɗinsa ya wuce, Affan na biye dashi a baya.
Jamil kuwa kitchin ya nufa yana cewa.
“Salamu alaikum Ummi”.
Da sauri ya iso kusa da Ummi.
“Ummi me kuke dafawa haka naketa jin ƙamshi ya ƙare zancen yana jan kular dake kusa da Ummi.
Yana buɗe wa yace.
“Kai badon a ƙoshe nakeba da nayi tafiyar ruwa da kular nan”.
Dariya Ummi tayi shi kuwa cewa yayi.
“Dan Allah wa akawa wannan girkin?”.
Da sauri Ummi tace.
“Hammanku”.
Juyowa yayi ya kalli Aysha tare da cewa.
“Uhum son kai. To ya dawo sai a kai mishi tare muka shigo”.
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
“Ba ni naiba Ummi ce ta mishi”.
Dariya sukayi duka, ita kuwa Ummi kallon Aysha tayi tare da cewa.
“To ɗauki ki kai mishi, kinga fa ɗaya tayi”.

To tace tare da ɗaukan tray’n ta nufi Side ɗinsa.

Ummi da Sara kuma sukaci gaba da aiki Jamil na zuba musu surutu.

A hankali tayi sallama tare da kutsa kai ciki jin muryar Affan a ciki yana surutu shi ɗaya kai kace zarerrene shi kuwa Sheykh bakace yana falon bama sai dai kaji yana cewa.
“Uhmm, uhum, ehh, ko?”.
Iya amsar kenan.
Ganin suna tsakiyar falon ne yasa ta iso tsakiyar falon, a hankali ta sunkuyo ta ajiye tray’n bisa santa table dake tsakiyar falon.
A hankali ya ɗago idonshi ya zubasu kanta, da sauri ya juyo ya kalli Affan ajiyan zuciya ya sauƙe ganin Affan ba ita yake kalloba duk da ita yakewa mgn, amman wayarshi yake latsawa.
wuyan rigarta da yake mai faɗine ya samu nasarar baiyana raɓin ƙirjinta a woje sabida sulewar da gyalenta yayi.
murmushi ta ɗanyi jin Affan na cewa.
“Ƙaro plate da spoon Aunty Aysha nima nan yunwa nakeji”.
Cikin tsokana tace.
“Ina Maman Amal”.
cikin kwaɓe fuska yace.
“Uhum ita kuwa yar zuriya tana can wai suna auren ƴar autarsu Zeenart”.
miƙewa tayi kana ta ɗan kalli Ya Sheykh haɗe fuska yayi tare dasa yatsarshi kan ƙirjinshi yaja kana ya nuna mata ƙirjinta da idonshi sannan ya nuna mata Affan da babbar yatsarshi wanda yayi alamun kamar gashin girarsa yake kwantawa.
Da sauri ta janye idonta kanshi kana ta gyara gyalenta.
Sannan ta juya ta ɗauko plate sannan tazo ta zuba musu.

Kana ta juya ta fita sabida wani irin mayataccen kallo da Ya Sheykh ke cilla mata.

A hankali Sheykh ya lumshe idonshi lokacin da yasa abincin a bakinsa taunawar da yayi yaji ɗan-danon ya sashi jin kunnenshi na amsa amo.
Affan kuma haɗiye lomar dake bakinshi yayi tare da cewa.
“Kai abincin yayi daɗi Malam jolof ɗin kwai ne ko na dankali ko na taliya ko daima jolof ɗin nama ne?”.
Murmushi Sheykh yayi tare da kurban tea kana yace.
“Ko zan riƙe maka takalminka kaje kayi tambaya ne?”.
Dariya Affan yayi tare da cewa.
“Wallahi ba santi bane”.
hannusa yasa ya ɗan make ƙeyan Affan kana yace.
“Kai ana zafi a garin nan ƙara gudun A/C’n nan ɗazu da zan fita na rage.”
Mikewa yayi tare da cewa.
“Gsky ana zafi koda yake naji ɗazu Gimbiya Aminatu na cewa yauwa kwana goma kenan ba’ayi ruwan samaba jiya har roƙon ruwa aka fita”.
Ya ƙare zancen yana dawowa ya zauna kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
“Har kwana goma, to Allah ya bamu mai Al’barka mai cike da ni’imomi”.
Amin Amin Affan yace kana sukaci gaba da cin abinci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button