
Ita kuwa Aysha kitchin ta koma, nan suka ƙarashe aikin kana suka shirya komai a Dinning table, sannan Sara ta tafi.
Ummi kuwa da Jamil suka zauna a falo.
Ita kuwa Aysha bedroom ɗinta ta, shiga.
Bathroom ta shige sabida, wani shegen fitinenne fitsarin da takeji.
Bisa toilet ɗin ta zauna tare da lumshe idanunta, sabida jin daɗin juye nauyin mararta da takeyi.
Bayan ta gamane, tayi amfani ruwan ɗumi.
Sai kuma ta kwabe dan zafin da takeji tace bari ta ɗan watsa ruwan sanyi lumshe idonta tayi lokacin da ruwan sanyin ya sauƙo jikinta, kana dai-dai lokacin ta tuno mafarkin da tayi da safiyar yau, da sauri ta rumtse idanunta gam sabida a fili take ganin yadda Sheykh yayi ta murzata a mafarkin da kuma irin kukan da tayi sabida azabar da ya azabar da ita da sauri ta ware idon da kyau sabida sai takega kamar zai shigo yanzune ya ritsa da ita haka yasa taci gaba da wonkon da sauri-sauri.
Cikin tsananin isa da izza da tsaurin ido, take taku har zuwa tsakiyar falon kana hadimanta na Binta a baya.
Tsakiyar falon ta tsaya tare da watsawa Ummi da Jamil ido dogon tsaki taja tare da cewa.
“Ina yake ɗan masu fiffigen!?”.
Da sauri Jamil ya miƙa tsaye tare da watsa mata wani irin mugun kallo mai cike da tsana yace.
“Baya buƙatar ganin irinku da ko sallama baku iyaba”.
Cikin tsawa da ɗaga murya tace.
“Rufe min baki ƙaramin kwaro, ka bari inyi da shi jan wuyan naku”.
Da sauri Sheykh ya miƙe tsaye jiyo muryar Gimbiya Saudatu a tsakiyar falonshi.
Affan ma miƙewa yayi da sauri kana yabi bayan Sheykh daya nufi falon da sassarfa.
Yana fitowa Gimbiya Saudatu ta gyara tsayuwarta tare da buɗe al’kyabbar jikinta kana tace.
“Yauwa al’huda-huda sarkin karatu.
Zo nan zo ka gayawa wannan ɗan tayin ƙanin naka cewa.
Duk lalacin mutun ya iya sallama amman banda tsuntsaye su sai dai su gani anayi, gwarama tsuntsun da ba zunibi ne ya maidashi tsuntsuwar ba dama haka Allah ya halicc…”.
Cikin wani irin tsananin tafasan zuciya da tuƙuki da ciwo a rai.
Sheykh yayi mata wani razanenne tsawan da saida tayi tsalle ta koma baya kaɗan.
Tsawar daya danna matane yasa Aysha fito da sauri tana mai gyara ɗaurin ɗan kwalin doguwar abayar da tasa yanzu.
Cikin rawan jiki yake taku har gabanta.
Ummi da Affan da Jamil kansu jikinsu kerma yakeyi.
Jalal dake Side ɗin su ma yajiyo sautin muryarsa hakane yasa ya nufo falon da sauri.
Cikin azabar fushi ya nunata da ƴar yatsarshi manuniya murya na rawa yace.
“Duk tsuntsuwar da kika gani Allah yasan da zamanta, ki kuma sanni wannan tsuntsuwar ta fiki daraja har gaban Allah”.
Cikin jajir cewa da ƙarfin hali ta ɗan ja da baya tare da cewa.
“Eh lallai kam ta fini har gaban Allah mana tunda girman zunubanta da jafa’inta yasa Allah ya nuna mana ikonsa da aya a kanta ya sauya mata halitta daga mutun zuwa tsu..”.
Wani irin zabura Ummi, Affan, Jamil, da hadiman Gimbiya Saudatu
Sukayi sabida wani irin azabebben ihu da ta kurma da karfi sabida wasu irin gigitattun tagwayen maruka da Sheykh ya yarfa mata da hannunshi.
Wanda sukayi nasarar tafiya da jinta da ganinta.
Kanta ya sake nufa da azama alamun zai tabketa da iyakar iyawarsa
Cikin rawan jiki Ummi tace.
“Sheykh kayi haƙuri barta kasan hannunka”.
Ina wani marin ya kuma yarfa mata wanda saida taji wani fitsari ya tsarto mata.
Ihun data kurma yayi dai-dai da kife kanta da tayi da jikin kujera.
Cikin wani irin azama da sauri haɗi da kiɗima Aysha tayi sauri ta nufi gaban Sheykh sabida ganin baya cikin hayyacina.
Affan da Jamil da sukayi nufin riƙeshi ne ya yarfawa maruka wanda yasa suka ja da baya.
Cikin azama tasha gabanshi tare dasa hannunta ta riƙo hannunshi da ya ɗago zai mari Gimbiya Saudatu, cikin azaban fushi ya juyo ya kalleta da rinannun idanunshi.
Da sauri ta kuma ƙara riƙe hannunshi tare da matsoshi kana murya na rawa tace.
“Yan Sheykh! Kayi haƙuri”.
Fusge hannunshi yayi da ƙarfi ya nufi kan Gimbiya Saudatu domin idonshi ya rufe rib baya ji baya gani kamar yadda itama Gimbiya Saudatu idonta da kunnenta suka dena aiki kana fitsari ke tsiyayo mata.
Da sauri Aysha ta kuma shan gabansa, kawai sai ta faɗa jikinshi ta ruggumeshi gam-gam a jikinta,
cikin rauni take cewa.
“Yah Sheykh ka bari, kada ka kulata Please Yah Sheykhhhh kada ka sake barin hannunka mai daraja da kullum yake cikin taɓa al’ƙur’ani mai girma ya taɓa fuskarta kada ka bari fuskarta ta samu darajar da hannunka zai taɓata.
Kar-kar haka jikinshi ke rawa da tsuma tamkar mazari, yana mai jiyo amon sautin muryar Aeech cikin kunnuwansu.
Ita kuwa Aysha a hankali tasa tafin hannunta ta tallabe gefe da gefen fuskarshi ta karkatoshi gareta, cikin sanyi da tattausan lafazi tace.
“Mai hankali keyin mgn ya dami mutane ba, majanuniya irinta ba. Bata da ma dafa, ita fa bushiyace mai baya kamar allurai, Please kada idonka ya sauƙa a kanta”.
Ta ƙare mgnar tana jan hannun sa na dama tana ja ta nufi Side ɗinsa.
Cike da mamaki Ummi, Affan, Jalal, Jamil, Hadiman Gimbiya Saudatu suka bisu da ido ganin ya bita a baya, tuni ta sarrafa fushinsa.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu har yanzu lalube takeyi wanda yasa Affan da Jamil murmusawa dan sai tafi kyau da makanta.
Ita kuwa Aysha Kai tsaye har bedroom nashi ta wuce riƙe da hannunshi suna shiga ta faɗa jikinshi.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da ruggumeta tsam a j…!
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 zaku turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.
Bana son VTU in kinyima ni ba ruwana. In ya kama dole ma baki da damar tura kuɗin ta Account ɗina to katin mtn zaki saya ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsapp 09097853276.
Gareku Murmushi group ngd da halaccin ku, zumuncin kenan.
By
*GARKUWAR FULANI*
[3/16, 9:48 PM] +234 806 559 0880: A jikinshi, ya matseta da ƙarfi, sabida tsananin fushin da yake ciki da tafasar da zuciyarsa keyi, ji yakeyi tamkar ya matseta ya medata cikin jikinshi kanta ya danni zuciyarsa ko zaiji sassaucin.
Ƙuna da ƙuncin da kalaman da Gimbiya Saudatu ke jifarshi dashi da mahaifiyasa dasu.
Haƙiƙa ita kaɗaice mutun da ta samu nasarar gano abinda ke ta’azzara fushinsa har ya kasa control ɗin kanshi ta tunzurashi.
Wani irin wahaltaccen numfashi Aysha ta fesar a hankali sabida jin wani fitinenne rugguma da yayi mata tamkar zai gamesu ya cure jikinsu wuri ɗaya.
Gaba ɗaya jikinshi rawa da kerma yakeyi tamkar mazari.
Cikin fizgo numfashin ta kwantar da kanta bisa ƙirjinshi dai-dai kan ƙahon zuciyarsa,
Kana tasa hannun ta saƙalo wuyanshi, ta ware yatsunta manya tana yin sama da ƙasa dasu a kan tattausan sajensa
Cikin sanyi tare da muryar kwantar da hankali tace.
“Indai har ikon Allah kan iya yaye duhun dare da hasken rana ya meye gurbindun.
To tabbas yaye baƙin ciki i zuwa farin ciki a zuciyar bawansa al’amarine mai sauƙin gaske.
Abin sani kawai shine su mumanai girman jarrabawa ko ƙalubalen rayuwa baya sasu fidda tsammanin samun rahamar ubangijin taliƙai.”
Murza kanta ta kumayi bisa ƙirjinsa sabida tanajin wuya da zafin ruggumar da ya mata cike da fushi.
Cikin sassanyan murya tace.
“A shawarce kayi ƙoƙarin jagorantar zuciyarka, kayi baya da lamuran kowa ka ruggumi naka.
Sabida kana zagaye da Magauta makusanta yau da gobe ita ce zata ganar da kai abubuwa da yawa, ka fuskanci magautanka ka dena dukan dungu.”
Mutsu-mutsu ta farayi a jikinshi sabida kalamanta na ratsashi kuma suna sashi zafafa ruggumar da yayi mata. Koda yake hakan baya rasa nasaba da hautsunewar kwanyarsa a kan kalamanta.
Cikin ɗan buɗa murya taci gaba da cewa.
“Kafin ka yarda da mutane to ka rinƙa morar Kekkyawar ƙwaƙwalwarka mai tarin basira da nazartarsu, ka dena yarda da mutun a bisa fuskarshi ta zahiriya.
Kafin ka buɗe musu zuciyarka ba basu kekkyawan mazauni na mutane masu amana.
Da yawan mutane dake da kaifin basira da iya tsara zance, har su sanyaya zuciyar mutun su sa mishi yardarsu a ransa.
Da idan zaka shiga zukatansu zaka samu dafin guban dake zuƙatansu yafi na baƙin kumurci.
Yah Sheykh kada ka damu da sauyin ɗan Adam tunda dama shi halittace mai rauni kan rikon amana da halaccin.
Har kullum ka jingina da kanka, duk wanda ya nuna zai zamto tsanine a gareka, koma yake ganin shine tsaninka, nuna mishi tun kafin zuwasa gareka.
A tsaye kake da ƙafafunka.
Ta hakane zai san ƙaucewarsa bata nufin faɗuwarka.”
Ɗan tsagaitawa tayi ta ɗago kanta, ta kalleshi sabida jin yadda tattausan gemunshi ke shafa goshinta.
Lip ɗinshi na ƙasa ya taune tare da girgiza gemun.
Ya kuma rumtse idanunshi sai dai yanzu ya ɗan fara sassauta ruggumar da yayi mata.
A hankali taci gaba da cewa.
“Gimbiya Saudatu fa, ba belbela bace, Yah Sheykh ka nazarci kalamai na, ita bushiyace ko ince kunkuru.
Zanfi son ka ɗauki zancenta dana mai taɓun hankali a ma’auni ɗaya.
Ni dai ban san menene tsakaninku ba, sabida bani da damar sanin komai naka, da ace na sani da ni zanji da ita, sai dai batun gsky ka dena yankewa littafi hukunci a bisa bongon bayanshi, ka buɗe littafi ka nazarceshi shafi zuwa shafi kafin ka yanke wa littafin hukunci”.
A hankali ya buɗe idanunshi.
Ya zuba matasu, tabbas yaji wani abu ya ɗarsun masa a zuciya, da zai samu yanzu duk suturan jikinta zai kekketashi ko zaiji sassaucin abinda yakeji.
A hankali ya saketa.
Kana ya zauna a bakin gado,
Kanshi ya dafe da hannunsa duka biyu.
Still har yanzu jikinshi kerma yakeyi.