GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Ita kuwa Aysha juyawa tayi da sauri ta nufi falon, da nufin ta ɗauko mishi ruwan sanyi yasha ko zaiji sassaucin abinda yakeji a ransa.

Ba ruwa Fridge ɗin nasa.
Hakane yasa kai tsaye ta wuce babban falon.

A can falon kuwa Affan da Jamil, sai dariya sukeyi ganin yadda har yanzu Gimbiya Saudatu taketa lalube a inda ta faɗi kasa dirsham.
Tuni fuskarta ta haye ta kumbura tayi sintim.
Hakama bakinta.
A hankali ta fara bude idanunta, sai ta kuma rufesu.
Ummi ce tayi murmushi mai cike da jin daɗin marukan da Sheykh ya yayyarfa mata.
Cikin dakiya ta kalli hadiman Gimbiya Saudatu dake gefe suna murmushi suma tace.
“Ku matso kuyi mata jagora”.
Da sauri Gimbiya Saudatu ta gyara zamanta tare da buɗe jajayen idanun nata, cikin masifewar murya tace.
“Ke tafi daga nan Jakadiya mara galihu”.

Da sauri suka juyo suka kalli inda Aysha ke tsaye wacce ta nuna Gimbiya Saudatu hanyar fita tare da cewa.
“Ki ɓace min daga nan, sabida mijina bazai juri jin ihun haukanki ba”.
Wani mugun kallo ta watsawa Aysha da jajayen idanunta kana tace.
“To fitsarerriyar ƙauye, mai gaggawar tsiri da cewa miji Baba, waya kasa dake bare ki zari babban kashi”.
Jalal ne ya ƙaraso cikin falon, sabida yana son yaga matakin da Aysha zata ɗauka tunda ta iya fesa Hajia Mamansu ma rashin kunya.
Ummi, Jamil, Affan, suma gyara zama sukayi.
Ya Jafar da yanzu ya shigo ma gefen Jalal ya zaune.

Ita kuwa Aysha cikin isa da ƙasaita ta iso gaban Gimbiya Saudatu kujerar dake gabantan ta zauna a kai wacce kujerar zaman Sheykh ne. Kai ta jinjina tare da cewa.
“Ƙauye tushen kowa! Duk wanda bashi da ƙauye to bashi da asali kenan, shin baki san cewa da ƙauye akanyi birni ba.
Shin ke kinma san me ƙalmar ƙauye take nufi kuwa?”.
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya, kana taci gaba da cewa.
“Da fari Makka itace babban birni sabida Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cikinta.
Da yayi hijira ya koma madina kuwa sa madina ta zama babban birni mai cike da salama sabida addinin da kanshi ya koma can.
In kin gane me ƙalmar ƙauye take nufi garin da babu addini ba ilimi garinda kafurai suke, shine ƙauye, domin duk inda hasken addini yake da ilimin da masana ilimin to sun zarta ace musu ƙauyawa, domin kalmar ƙauyawa tana nufin jahilai, niko nan da kike ganina gidanmu tushene na tsanƙaya yara da dattawa.
Dan haka janye kalmarki ta fitsarerriyar ƙauye, gorinki bai samu muhalliba.”
Tsaki taja tare da cewa.
“Baki san cewa kunne ya girmi kaka ba ko? To inma baki saniba Ni nan Aysha ina sane da labarin ƙuruciyarki da rashin kunyar da fitsarar da kikayi da taraddadin da kika sawa iyayenki na alamun lalacewa, dan haka kece fitsarerriyar. Kana kuma in kin mance in tuna miki ƙauyenmu ya zarta asalin naku ƙauyen girma da daraja ko dai kin mance inane asalin ƙauyenku.
In kin mance in tuna miki, ita kanta masarautar Joɗa kafin a auroki cikinta zata amsa kiran suna ƙauyen da hausawan ke nufi.
Yau da gobe shike sauya komi da kowa.
Ni nan da kike gani da mgnarki data ɗaurerre a turu basu da maraba.”
Cikin masifa Gimbiya Saudatu tace.
“Sai dai in kece mahaukaciyar”.
Dariya tayi tare da cewa.
“A a akan bola nake”.
Miƙewa tsaye Gimbiya Saudatu tayi tare da fara gyara al’kyabbar jikinta, tare da cewa.
“Zanyi mgninku zaku gane kurenku”.
Taɓe baki Aysha tayi.
Ita kuwa juyawa tayi ta, fice hadimanta na biye da ita a baya.
Dariya sosai Ya Jafar yayi wacce saida ta basu mamaki.

Sheykh kuwa da tun ɗazu ya fito bayan yayi al’wala ganin azahar tayi,
Tsayuwa yayi yana jin yadda Aysha keyi da Gimbiya Saudatu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu ganinshi ne yasa ta miƙe maza ta fice.
Miƙewa Aysha tayi da sauri jin muryar sa yana cewa.
“Ku tashi kuje kuyi al’wala lokacin salla yayi”.
Juyowa tayi ta zuba mishi ido.
Tabbas daga jin muryarsa da yanayin fuskarsa zai iya nunawa mutun cewa har yanzu a zuciye yake.

Kallonta yayi a fizge kana yaja idonshi yayi gaba su Affan na biye dashi a baya.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Dai-dai kenan yau dai Sheykh ya sawa Gimbiya Saudatu tsoron zuwa nan ta baje kolin rashin kunyar ta.”
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
“Uhummm Ummi an dukan tenki akefa aka bar jaki a ɗaure”

Cikin sauri Ummi tace.
“Kamar yaya?”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Muje muyi salla, Ummi”.
To tace tana mai son nazartan kalaman Aysha.

Bayan sunyi salla ne suka fito falon.

Suna zama Sheykh Jabeer ya shigo.
Affan, Jalal, Jamil, Ya Jafar. Na biye dashi a baya.
Su duk Dinning table suka nufa.
Ummi na biye dasu a baya.

Abinci ta fara zuzzuba musu.
Shi kuwa Sheykh tuni ya wuce Side ɗinsa.

Ita kuwa Aysha waya takeyi da Aminiyarta Rafi’a.
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
“Rafi’a naji kamar an nememu a makaranta ko?”.
Ɗan gajeren tsaki Rafi’a taja tare da cewa.
“Haka dai akayi ta cewa, to amman zancen Babu tushe, ance ƙaryane, gwamnatin ma bata nemi malaman ta zauna dasu ba.”
Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah aini wannan yajin aikin da aka shiga yamin rana, kinga da wannan tsarkafeffen auren da aka liƙamin da ya sani a tsaka ba fita.
To amman yanzu kinga duk muna a tare, zan kuma dage inyiwa Umaymah batun karatun nawa, kafin a nememu, in tayiwa Yah Sheykh mgna dai nasan zai barni.”
Tsaki Rafi’a ta kumayi tare da cewa.
“Hegiya Aysha wato ke murna kikayi”.
Dariya tai kana tace.
“Sosai ma kuwa”. Kauda zancen Rafi’a tayi da cewa.
“Yauwa su Ummey sun dawo kuwa? Ɗan na kwana biyu banyi mgn da suba.”
Jingina kanta tayi da jikin kujera kana ta fesar da numfashi a hankali tace.
“Uhummm basu dawoba, Rafi’a bani da kowa nawa a kusa dani, tunda nazo gidan nan ban sake ganin Ummey naba gwara Bappa na da Ya Al’ameen sunzo da bani da lfy, ina kewar Junainah, ina kewarsu Yah Giɗi in na tunosu hankalina na tashi ina masifar kewa da son ganin Dedde na”.
Cikin tausayawa Rafi’a tace.
“Ba komai Aysha kiyi ta musu addu’a in sha Allah zasu baiyana kuma Allah zai karesu.
Su Ummey kuwa kwanaki da mukayi mgna da Junnu tace min wai sun kusa dawowa”.
Cikin sanyi tace.
“Wasa sukewa Junnu, sabida ta matsa wai ita zata zo wurina kuma ita ko a gidansu Junaidu zata zauna”.
Dariya Rafi’a tayi tare da cewa.
“Uhmm su Junainah manya wato ita fa da gaske har ranta take son Junaidun fa”.
“Sosai ma kuwa”.
Aysha ta faɗa tana kallon Ummi dasu Affan da suka miƙe tsaye alamun sun gama cin abinci.
“Yauwa ga Umma wai tayi kewarki kwana biyu baku gaisaba”.
Rafi’a ta faɗa tana miƙawa Ummanta wayar.
Amsa Umma tayi tare da cewa.
“Aysha ya gida ya kwana biyu”.
Cikin jin daɗi tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Umma yasu Jamila”.
“Lfy lau suna gaidaki”.
Tace.
Kana ta miƙawa Rafi’a wayar tare da cewa.
“Tashi kije kinyi baƙo”.
To tace kana ta katse kiran sannan ta fita.

Ita kuwa Aysha juyowa tayi ta kalli Ummi dake miƙa mata wayarta tare da cewa.
“Amshi Umaymah ke son mgna da Sheykh ta kira wayarsa baya ɗagawa ke kuma ta kiraki taji kina waya.”
Amsa tayi da sauri kana ta kara a kunne tare da cewa.
“Assalamu alaikum, Umaymah ina wuni”.
Umaymah dake kwance kan gado Mamma na gefenta,
Murmushi tayi tare da cewa.
“Lfy lau Alhamdulillah Aysha, ya gajiyar hanya?”.

“Alhamdulillah Umaymah inasu Hibba da Safiyyah”.

“Suna lfy, suna can Side ɗin Jannart”.

Ayyah tace, ita kuwa Umaymah gyara kwanciyarta tayi tare da cewa.
“Yauwa Aysha Kaiwa Jazlaan waya”.
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
“To Umaymah bari in Kai mishi”.
Corridor’n ta shige, tana tafiya tana gaisawa da Mamma data amshi wayar.
A hankali ta kutsa kanta cikin falon shiru, babu kowa sai hasken wuta daya karaɗe falon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button