
Shi kuwa Sheykh hannu yasa yana sharewa Yayan nashi hawayen, a hankali suka juyo suka kalli ƙofar ɗakin Hajia Mama ce, ta shigo hadimanta na biye da ita a baya.
Gefen Juwairiyya ta zauna ta zubawa su Sheykh ido, lokacin ɗaya hawaye ya fara kwaranyowa da idanunta, cikin rawan murya tace.
“Sheykh lokacin na tafiya, Maimartaba ya aika a kirawo ka a zatonsa kana sashina, tashi kaje, Allah ya kiyaye hanya karka damu yayanku na ƙarƙashin kulawata musamman”.
A hankali ya miƙe ga mamakinsu sai gashi shima Jafar ya mike hannunshi yasa ya kamo ƙanin nashi,
cikin rauni Sheykh yace,
“Hajia Mama kodai in tafi dashine, kingafa baya son in tafi in barshine”.
Hannu tasa ta share hawayenta kana a hankali tace.
“Bazai yiwu ka tafi da shiba, karka damu Jabeer komai zai wuce”.
Kai ya gyaɗa mata, sannan ya juya, ya nufi hanyar fita yana riƙe da hannun yayan nashi, Jalal na biye dasu a baya,
Hajia Mama da Juwairiyya da yaranta na biye dasu.
Koda suka zo tsakiyar farfajiyar gidan cikin bada umarni Hajia Mama ta kalli Sheykh tare da cewa.
“Jabeer kuje sashin Hajia Fatima ka sallamarta”.
Ɗan jim yayi, a hankali ya kalleta, ita kuwa da sauri tace.
“Umarnine ba shawaraba”.
Kanshi ya gyaɗa alamun to.
Daga nan suka shiga sashin nata, bayan Jakadiya tayi musu iso.
A folon forko suka Sameta, tana hakimce hadimanta na zagaye da ita.
Tana ganinsu ta tashi ta zauna, cikin sanyi tace.
“A a Sheykh da kanka”.
Ɗan rusunawa yayi tare da cewa.
“Zanyi tafiya Hajia mamace tace inzo in sallameki”.
Da sauri tace.
“Ayyah, to Allah ya kiyaye hanya ya kaika lfy ya dawo da kai lfy”. Amin yace a takaice kana ya kama hannun Ya Jafar ɗinshi suka fito.
Nan suka raka’a zuwa sashin Gimbiya Aminatu nan suka sameta a falon, sukayi sallama da ita.
Daga nan ya wuce fada, Hajia Mama kuwa ta koma sashinta da hadimanta bayan ta mishi addu’o’in insa lfy.
Juwairiyya kuwa parking lot ɗin su inda ta hango an jera motoci. Ta nufa inda Jamil ke tsaye da alamun waya yakeyi da Malika sahibarsa sabuwar budurwar da yayi.
Shi kuwa Sheykh yana shiga fada ya samu Waziri ne kaɗai da Maimartaba da alamun zaman jiransa sukeyi.
A gaban Maimartaba ya rusuna, tare dasa hannu ya tura hularshi ya maidashi baya,
Cikin kulawa Sarki Nuruddeen yasa hannu kan tsakiyar kanshi ya dafa tare da cewa.
“Allah ya kaika lfy, ya dawo da kai lfy, ya baka sa’an tafiya, ya kareka a duk inda kake”.
Amin Amin suka amsa baki dayansu, kana Waziri ma ya mishi addu’o’in sannan suka miƙe gaba ɗayansu sukayi woje dan mishi rakiya,
Sarki Nuruddeen da bayinshi wazirinsa da bayinshi, shina Sheykh da bayinshi, sai ya zama rakiyar ta samu taron mutane,
kana ga bayin Ya Jafar, nan suka shishshiga tsala-tsalan motoci a ƙalla motoci goma sha biyar ne sukayi mishi rakiya zuwa Airport.
A wurin rabuwarsa da Ya Jafar ne yasa zuciyar kowa raunata domin Jafar kuka sosai yayi tayi da kyar dai suka dawo gida bayan jirgin su Sheykh ya tashi zuwa birnin Jalaluddin.
Cikin abinda bai gaza awa ɗaya ba sai gasu a birnin Jalaluddin.
Kafin jirginsu ya sauƙama a ƙalla motoci goma ne suka zo tarbansa, a ciki kuwa harda mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Koda yaga jikan nasa mota ɗaya suka shiga,
suna isa fadar musulunci,
suka fito daga cikin motocin da sauri Sarki Jalaluddin ya zagayo ya kamo hannun jikan nashi, suka nufi sashin Amaryarshi Gimbiya Kulsum, jikanshi Kabir na biye dasu a baya, suna isa falonta gaba ɗaya ma’aikatanta suka fita ganin mai alfarma da kanshi, shi kuwa Jalaluddin cikin ɗan ɗaga murya yake cewa.
“UmmuKulsum! UmmuKulsum!! Ga Jazlaan ya iso, gashi na kawo mikishi har ɗauki”.
Wata kekyawar tsohuwar balarabiyace ta fito da sauri, cikin tsananin soyayyanshi ta ruggumeshi,
shima ruggumeta yayi cikin harshen larabci Sheykh yace .
“Ana uhubbiki hubban axeeman ya Sitti”.
Kanshi ta shafa cikin tsananin son jikan nata tace.
“Laisa li misluka abadan ya habibee”.
Murmushi mai faɗi yayi tare da bin bayanta, kai tsaye dinning area ta nufa dashi Kabir da Sarki Jalaluddin na biye dasu, da kallon sha’awa.
Kujera taja ta ajiyeshi, kana ta jawa Jalaluddin tasa kujerar nan kabirma ya zauna,
Suna zama sai ga wasu dattijan mata su uku sun shigo a jere a jere, suna zuwa duk kanshi suke shafawa shi kuwa sai murmushi yayi tare da kallon Mai alfarma Sarki Jalaluddin yace.
“Malam kace su dena shafa min kai haka na gaji”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu kana suka zauna, cikin kulawa babbar cikinsu tace.
“Kazo lfy, ya jikin Jafar?”.
A hankali ya ɗan kalleta tare da cewa.
“To Alhamdulillah jiki da sauƙi zance”.
Allah ya ƙara sauƙi cewar Jalaluddin Amin Amin suka amsa baki ɗayan su, ƙaramar cikinsun ce ta ɗan kalleshi cikin tsokana tace.
“Ina mai gidanmu Sarki muminai”.
Taɓe baki Sheykh yayi tare da cewa .
“Uhumm Jalal ne Sarkin Musulmai ko? Baki sanshi bane”.
Dariya sukayi duka kana suk gaggaisa sannan suka fita gaba ɗayansu, ita kuwa Sitti abinci tayi ta bashi har saida ya kwaɓe fuska tare da cewa.
“Na tuba ki barni haka na ƙoshi”.
Kai ta gyaɗa kana suka dawo falo zata fara hira, yace shi dai ya gaji bacci yakeji hakanne yasa, Jalaluddin da kanshi ya kaishi makwancinsa.
Asuba ta gari al’ummar Sokotawa
A nan Ɓadamaya kuma cikin Rugar Bani
Washe gari da hantsi, bayan duk sun karya, kowa makiyaya duk sun tafiya kiwo, manoma kuma duk sun tafi noma, kana mata masu shiga tallan nono cikin gari sun tafi, garin yayi tsit kamar yadda aka saba
Ba’ana kuwa da Shatu suna zaune a ginɗin bishiyar mangoro dake bakin zauren su, ita tanata.
Ciki shi kuma yanata woje, cikin sakin fuska ya kalli Junainah dake gefensu yace.
“Junainah je cikin gida kice a baki ɗanyen kwai ki kawo mana in dafa mana”.
Da mmki Shatu tace.
“Ka dafa mana kuma?”. Kai ya gyaɗa mata, ita kuwa Junainah uwar kwaɗayi tuni ta tafi cikin gida Inna na tambayarta me zatayima Bata kulataba, sai ɗan kwano data ɗauko a konɗonsu kwan zabbi ta ɗebo a kalla sun kai goma, kana da gudu ta dawo wurinsu.
Da sauri yasa hannunshin ya amshi robar, ita dai Shatu Ido ta zuba mishi taga ta ina zai dafa kwan,
shi kuwa Ba’ana hannunshi yasa ya fara tona ɗan ma dai-dai cin rami, da mmki Shatu tace.
“Ya Ba’ana me zakayi da tona rami kuma?”.
Cikin murmushi yace.
“A ciki zan dafa mana kwan”.
Junainah kam gabanshi tazo ta zauna, tana kallonshi har ya gama tona ramin.
Kana ya zuba kwayayen a ciki ya maida ƙasar ya binnesu.
Sannan ya juyo ya kalli Shatu yace.
“To musha hirarmu kafin kwan ya nuna”.
Junainah ce tace.
“Ya Ba’ana ta yaya zai nuna kuma babu wuta?”. Kamo hannunta yayi tare da cewa.
“Ke dai zauna ki jira ki gani ƙaƙara”.
Kai ta gyaɗa tare da gyara zama, shi kuwa Ba’ana murmushi yake a baiyane a ranshi kuma cewa yakeyi.
“Uhummm shi Bappa dan ina son yarsa bazai hanani yashe Garkensa ba, kuma da koyayen gidanshi kawai zan iya karya kafin da yayiwa garkenshi”.
A zahiri kuwa kallon Shatu a yayi tare da cewa.
“Zakiji girkina mai daɗi”. Kai ta jinjina tare da cewa.
“Uhumm girki ko al’mara.”
Kanshi kawai ya gyaɗa alamun zaki gani daga nan sukaci gaba da hira.
Bayan kamar 42 minutes ya fara tono wannan ramin daya tona a gabansu babu wuta ko ɗigo ya binne ɗanyen koyaye, sai gashi ramin yana tururi tamkar an bude tukunyar dake tafasa, da sauri Aysha ta waro idonta.
Junainah kuwa sai tsalle take,
shiko Ba’ana saida ya kwatso ƙoyayen kab kana ya sasu a robar da aka kawosu a ciki,
Ɗaya daga ciki yasa a gefen dutsen da yake zaune ya konkotsashi kaɗan kana ya ɗagoshi, yatsunshi biyu yasa yafara ɓarewa.