GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shiru tayi tana nazartan kalamansa, da kuma abubuwan da suka wakana.
Wannan nafila raka’a biyu da addu’arga da yayi ya ɗura mata ruwa a cikinta, ya kuma kaɗa mata hanjin cikinta tsoronshi ya rufeta.

Ta lura gaba ɗaya ya sauya komanshi na yau wani sabon al’amari ne.
Jawo plate ɗin tayi sabida tasan ya fita sanin girman al’ƙawari da mahimmanci cikashi.

Fork ɗin tasa tana sokan naman tana sawa a baki tana tauna tana haɗiyewa, sabida ɗanɗanonsa yayi mata daɗi.

Ci takeyi tana kallon ƙofar Bathroom ɗin.

A hankali ta ajiye fork ɗin kana tasa hannunta ta ɗauku cup ɗin madarar, tasa a baki.
Ido ta lumshe sabida wannan shine haɗin da tafi so.
Sabida dashi Ummey ta raineta.
Zuƙeshi tayi har kusan rabi.
Kana ta janyeshi daga bakinta, tare da buɗe idonta data lumshe cikin sanyi tayi wata gyatsa mai tabbatar da ƙoshi.

Dai-dai lokacin kuma ya fito daga bathroom,
daga ƙafarshi ta fara kallo har zuwa sama.
wasu tattausan riga da wondo masu masifar kyau Sky blue ne mai ɗigo-ɗigon fari.
Wondon dogone har ƙasa rigar kuma irin mai hular manne ya kwantar da hulan a bayanshi bisa kafaɗunsa.

Hannun rigar yan dadai.

Wani irin ƙamshi yakeyi mai masifar daɗin shaƙa.
Sejenshi yayi lib sai sheƙi yakeyi.

Kanshi ya ɗan jujjuya kana yace.
“Kada ma kiyi ta turawa a dole, barshi kawai kin faɗi sharaɗin.
Janye plate ɗin yayi kana ya juye naman cikin kular.
Cikata mata cup ɗin yayi da madarar zuman kana ya ture tray’n can gefe, sannan yace.
“Shanye madarar kizo ki hau gado ki kwanta”.

Tura baki tayi alamun zatayi mgna, sai kuma tayi shiru ganin ya shimfiɗa sallayarsa can gefe, ya kuma ɗauki al’ƙur’ani,
alamun karatu zaiyi.

Hakane yasa tayi shirun.
Shi kuwa karatu ya fara kamar yadda ta zata.

A hankali tasa kofin a baki taci gaba da shan madarar, tanayi tana lumshe idonta, sabida haɗin yayi iri ɗaya sam dana Ummeynta kamar itace ma ta haɗashi.

A hankali ta shanyeshi tas, kana ta ajiye cup ɗin kan stoll dake gaban gadon.

Zama tayi tana jin ƙira’arsa mai daɗin sauraro.
Ƴar ƙaramar wayarshi dake gefenta ta kalla, ƙarfe goma harda rabi.
Zuwa yanzu kuma ruwan saman ya tsaya cak sai walƙiya da rugugin da akeyi tako ina wanda haka ke nunin da hadarin bai gama hucewa na zubda ruwanba, ko ma wani hadarin ne ke tasowa daga ƙasa.

Wani sassanyan hamma tayi mai cike da bacci.
Inda yake ta kalla, sam hankalinsa baya kanta.

Hakane yasa ta miƙe a hankali, sabida hankalinta ya ɗan kwanta dashi ganin bai kulata ba.

A hankali ta zagaya can gefe, ta zauna bakin gadon.
Tana mai lullumshe idanunta.
Minti talatin tsakani ta ɗan gyara zamanta ta mirgina ta kwanta, kana ta bashi baya.
sannan ta gyara ƙaton hijabinta ta duƙunƙune a ciki.

A hankali take jiyo muryarsa yana karatun.
Shi kuwa Sheykh duk abinda takeyi yana sane bai kulata bane, dan yana son ta nitsu.

Sha biyu dai-dai agogon wayarsa ya nuna masa.
A hankali yayi addu’an samun zuriya ta gari da Addu’o’in kariya da kuma cikar burinshi ya shafa sannan ya miƙe ya ninke sallayar,
ya ajiye al’ƙur’ani.
Kana ya tako ya iso jikin gini, gudun A/C ya dai-dai-ta kana ya kashe wutan ɗakin.

Sannan ya kunna hasken wayarsa ya nufo kan gadon.
A hankali ya zauna a bakin gadon bakinsa ɗauke da tasbihai.

A hankali ya ɗaga hannunshi ya haɗesu kana ya buɗe tafin hannunshi yayi addu’o’in bacci ya tofa, ya shafawa jikinsa.
Kana ya hawo saman gadon da kyau.
Cikin sanyi da nitsuwa ya isa inda take.
A hankali yasa hannunshin ya fara jan ƙaton hijabin dake jikinta.

Da sauri tasa hannun ta ta kamo nashi,
sabida dama baccin nata ba wani nauyi yayiba.
Jin yadda ta riƙe hannunshi ne yasa ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa da kunneta kana yace.
“Addu’a zan shafa miki, kuma bazan shafawa hijabiba”.
Cikin muryar bacci tace.
“Sanyi nakeji ai”.
Ci gaba da janye hibajin yayi tare da cewa.
“In na shafa miki sai ki meda”.
Sake mishi hannun tayi kana, tayi shiru tana jinsa yana karanto addu’o’in yana tofawa a tafin hannunsa.
Saida ya gama kana ya sunkuyo ya kife tafin hannunshi kan fuskarta. Ya fara shafawa daga saman kanta har zuwa ƙasa kana har bayanta.

A hankali tace.
“To bani hijabin”.
Konciya yayi tare da cewa.
“Yayi nisa”.
Shiru tayi tana jin wani irin fitinenne ƙamshin jikinsa da sanyin ɗakin suna ratsata.

A hankali ta fara fidda numfashi.
walƙiya kuma in ya haska har cikin ɗaki.
Har yana ɗauke ido.

Hannunsa yasa ya kamo hannunta na dama ya joyota rigingine.
Ɗan sunkuyowa kanta yayi.
Hakan yasa suka ɗan fidda numfashi a tare,
Cikin nitsuwa taji ya manna mata kiss a goshinta,
tare dasa tafin hannunsa bisa nata tafin hannun.
Cikin wani irin sassanyan numfashi ya cusa kanshi tsakankanin wuyanta da kafaɗarta hancinshi ya manna kan fatar wuyanta, idonshi ya lumshi tare da ƙara shaƙan ƙamshin jikinta.
Iya kuwa Aysha wani irin harbawa zuciyarta ya fara can ƙasa yake.
Dib-dib-dib.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya dawo da kanshi kan fuskarta.
ƙasa yayi da bakinshi.
Harshensa ya ɗan zaro ya manna da tattausan lips ɗinta,
lasarsu yayi tare da fidda wani matacce sauti.
“Hiehhhhhhh”.
shiru tayi kamar mai bacci,
sai kuma taji ya zira mata harshensa cikin bakinta,
A hankali ya lalimo tong ɗin ta wanda haka yasa jikinta ya fara tsuma rumtse idanunta tayi da ƙarfi jin ya,
naɗe tong ɗinta cikin nasa, tare da fara tsotssarshi tamkar ya samu tom-tom mai yaji.
Ƙasa yayi da hannunsa cikin wuyan rigarta yasa yatsunshi yana neman inda zip ɗin.
gaban rigar tata yake.
meda hannunshi yayi ya tallabeta da kyau.
Kana yasa yatsunshi biyu kan zib ɗin gaban jacket ɗin.
hannunshi yasa cikin gashin dake wuyan jacket ɗin.
Zib ɗin ya kamo kana yaja yayi ƙasa dashi, yayinda kuma tong ɗinsa na kanainaye da nata.
da sauri ta riƙe hannunsa tare da alamun kada ya cire mata shi.
Bai kulata ba kuma bai sake zib ɗin ba.
a hankali ta kuma riƙe hannunsa tare da fara jujjuya kanta.

Wani kiss ya ƙarayi mata mai cike da sabgogi masu birkitarwa.
A hankali ya ture hannunta kana ya zuge zip ɗin da ƙarfi yayi ƙasa dashi.
kana ya buɗa rigar tare da wareta.
shiru tayi tana jinsa sabida karkarwan da jikinta keyi ya fara yawa. hannunta ya zare cikin hannun rigar, ya zare shi kana ya jefar dashi gefe.

Ya rage daga ita sai Baby top da jeans ɗin jikinta.
zare bakinshi yayi daga nata.
Haka yasa ta juya da sauri ta bashi baya tare da haɗe hannunta a ƙirjinta ta ƙanƙame kanta gam tana jin yadda zuciyarta ke buga lugude.
shi kuwa matsowa ya kumayi a hankali ya manna ƙirjinsa da bayanta,
Ɗan ronƙofowa yayi kanta ya cusa fuskarshi tsakanin wuyanta da kafaɗunta.
yana shaƙan ƙamshin turaren dake jikinta hannunshi ɗaya kuma bisa cikinta ya ɗaurashi a hankali murya can ƙasa yace.
“Aish!”. Shiru tayi ba amsa mishiba, sai wani tsuma da jikinta keyu.
“Aich”. Ya kuma kiranta a hankali cikin kunnenta.
Murya can ƙasa tace.
“Na’am”.
Kanshi ya ɗan manna da fuskarta kana a hankali yace.
“Bana son wanna shigar a irin ya wannan lokacin”.
Kawai ta tsinci bakinta da cewa.
“Kayi haƙuri”.
Kafaɗarshi ya maƙe tare da cewa.
“A a bazanyi haƙuri ba.”
A hankali murya na rawa tsoro da sanyi tace.
“To Yah Sheykh ya zanyi”.
Ƙara manneta da jikinsa yayi tare da cewa.
“Cireshi zanyi”.
Da sauri tace.
“Yah Sheykh”.
Bai bari taci gaba ba yace.
“Na’am Ya Aish”.
hannunshi yasa ya tura rigar sama, ya zama cikinta ya baiyana woje,
tafin hannunsa yasa yana shafa cikin a hankali.
wani irin numfarfashi take fiddawa a hankali a hankali,
yayinda zuciyarta ke buga dib-dib ya zatayi? Me yake nufi? Me yake so? Me zaiyi? Sune abubuwan da suka taru suka sa mata taraddadi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button