GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shi kuwa Sheykh da sauri ya isa tuni an karance fatiha ta raka’ar forko har an fara suratul Al-Burooj, yana isa kuwa ya wuce sahun forko.
miti bakwai tsakani aka tafi ruku.
A hankali ya sunkuyo dan yin rukun, sai kuma ya rumtse idanunshi da ƙarfi sabida wani irin masifeffen ciwo da yaji cinyoyinsa sunayi,
Ciwon da duk na mijin da bai taɓa kusantar maceba kuma yazo yayi katari da yage cikekken (tattani) budurci tofa dole yaji wannan sauyin da ciwon cinyoyi.
A hankali ya taso daga ruku’un sabida sosaifa cinyoyinsa da ƙugunsa sukayi sami da fitinar gwatson da yayi daren jiyan wanda bai taɓayi ba.

Taune lip ɗinsa na ƙasa yayi lokacin da aka tafi Sujjadar forko.
Sabida ciwon yafi na rukun.

A haka dai akayi sallan aka idar.

Bayan an idarne, kamar koda yaushe ya fara Du’a’u Azkar.

Abbansa da Lamiɗo da Galadima suna gefensa.

Suma sunayi koda suka ida
a hankali ya miƙe tsaye ganin Abbanshi ya yafitoshi da hahhunsa.

Bayan Abba da Lamiɗo da Galadima da Baba Kamal yabi.
Affan, Jamil, Jalal, Ya Hashim, Imran, Sulaiman, Laminu. Suma suna biye dasu can baya da sauran zaratan jikokin Lamiɗo da sauran ahlin masarautar Joɗa.
Kana jan baya kuwa dogaraine.

Side ɗin Lamiɗo ya nufa Abbansa da Galadima da Lamiɗo na gabansa.

Suna shiga suka wuce can cikin special Side ɗin Lamiɗo.

Bayan sun zauna ne ya kalli, Abbansa a hankali yace.
“Abba ina kwana”.
Tsura mishi ido yayi tare da cewa.
“Lfy lau Muhammad ya gajiyan hanya”.
A hankali ya gyara zamanshi ya tonƙoshe sawunshi kana yace.
“Alhamdulillah, Jiya naje mu gaisa sa Hajia Mama tace baka nan”.

Kallonshi Abba yayi tare da jijjiga kai.
Shi kuwa Lamiɗo ya ɗan kalla da Galadima kana yace.
“Kun kirani kunyi shiru, kunata bina da kallon tuhuma, me yake faruwa in da wani abune ku faɗa kawai mana ku dena min kallon tuhuma”.
Murmushi sukayi dukansu kana a hankali Galadima yace.
“Babu komai, kawai dai yau ɗin ranace da al’amarin auren ka ya tabbatar da nuna kanada damar mulkar masararutar Joɗa”.
Fuska ya taɓe tare da cewa.
“Bafa nason kuna min haka, bani son haka, nace bani da ra’ayin wannan abun ku dena alaƙantani dashi.
Me haɗina da sarauta, kuma me ruwanku da lamuran gidana”.
Cikin Murmushin Lamiɗo yace.
“Uhumm toh ai ba mune muka kiraka ba, Abbanka ne ya kiraka.
Kuma ba mune muka alakantaka da Masarautar Joɗa da sarautarba Allah ya alaƙamtaka dasu tunda ka fito a jininmu.
Mu dai ya nuna mana alamomin dole watan wata rana zaka mulki masarautar Joɗa.”
Cikin tsuke fuskarsa yace.
“Uhum zadai a tarwatsa min rayuwa, tunda kuna sane Galadima kawai aka bawa Yah Jafar cikin mako biyu, aka rabamu da gatanmu aka birkita masa rayuwa.
Shin Jalal da Jamil ma sun tsirane, kallon me akeyi musu.
Jamil mazinaci mai yawon bin mata, Jalal mashayi ɗan shila, nima ɗin dole ana wani abin, da ƙudurar ubangiji kawai nake tsira, kuma wanda ake nema gabas da yamma kudu da arewa wata ranafa zasu cimmin musamman in suka samu zantukanku”.

Dafa kafaɗarshi Galadima yayi kana a hankali yace.
“Uhum Muhammadu ai sunyi nasara a kanka tun a baya yanzu dai karyewar al’ƙadarinsu ne kawai ya rage.
Tashi kaje ka kula da matarka, muna sane da gyallen yarinta, kada kace zaka ɓoyeshi ko zaka wonkeshi, a ma’ajiyin tarihi za’a ajiyeshi shaidar yarinta da tarbiyyar matar sarki uwar wani sarkin kuma a wata rana”.
Kanshi ya sunkuyar cike da takaici yace.
“Wai meyasa kukeyi min hakane? Shin bani da wani sirri a rayuwata da iyalina ne dole sai kunbi diddigin komai kun sani”.
Haɗe fuska Abbansa yayi kana yace.
“Tashi kaje, kada a wonke komai a ka bawa Umminku ta kawoshi.
Umarnine ba shawara ba”.

Cikin sanyi ya miƙe ya tafi.

Shiru babban falon ba kowa,
sai dai bisa alamu Ummi na Kitchen dan yaji motsinta.

A nitse ya wuce Side ɗinsa.

Idonshi ya rumtse sabida jin suna mishi wani yaji-yaji dan rashin baccin da baiba tun na yammacin jiya na tsakanin azahar da la’asar ɗin daya zame mishi jiki da kuma na daren da bai samu yayi ba.
A hankali ya tura ƙofar Bedroom,
da sauri ya ƙarasa bakin gadon cike da mamakin ganin tana kwance, kuma kuka takeyi.
Sunkuyowa yayi kanta tare da cewa.
“A’ish Ahh’ihch kuka kuma? meya saki kuka. meya sameki?”.
Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalleshi hawaye na kwaranya murya na rawa tace.
“Meya sani kuka? Bayan kai, kaji min ciwo, bazan iya tashiba, ƙafafuwana ba ƙarfi, jiri nakeji yunwa nakeji kaina ciwo, kafata ciwo, idona ciwo, komaina ciwo, zogi nakeji”.
Ta ƙarashe mgnar murya na rawa alamun zazzafan zazzaɓi da zafin ciwo.
Cikin wani irin rauni da tsananin tausayinta yace.
“Afwan kiyi haƙuri, sannu ko ki gafarceni”.
Da sauri ya juya ya nufi Bathroom, ruwa mai ɗumi sosai ya cika baf dashi, kana ya fito.
Al’kyabbar ajikinshi ya zare tare da hiramin kana ya matso bakin gadon.

Hannunshi yasa ya fara janye blanket ɗin.
Da sauri tasa hannu ta riƙe hannunsa a raunace tace.
“Banda sutura a jikina”.
Kanshi ya ɗan kauda kana a hankali ya janye borgon tare da cewa.
“A’ish gani kuma wanne suturan zaki nema bayan ni, yanzu baki da wata sutura sama dani, kiyi haƙuri ki dena kukan kinji ko bana son jin kukanki”.
Ya ƙare zancen yana cicciɓota.
Da sauri ta rumtse idanunta tare da cusa kanta cikin ƙirjinsa.
Bathroom ya wuce.
A hankali ya sauƙeta cikin ruwan ɗumin.

Wani irin zillo tayi tare da yarfa hannun da kuma sakin ihu mai sautin rauni.
“Wash Allah na Yah Sheykh zafi- zafi.”
Cikin sanyi yace.
“Sorry kiyi haƙuri zakiji daɗin hakan, yanzu zaki worke”.
Ina sai zillewa take son yi.
Da sauri yasa hannunshin ya danne ta cikin ruwan ta zauna daɓas.
hannunta ta fara yarfawa tare da zubda hawaye,
Bakin baf ɗin ya zauna,
kanta ya jawo ya manna da jikinsa, kana yayi shiru yana jin yadda jikinta ke karkarwar tamkar mazari.

Wata fitinenneyar zuface ta fara karyo mata tako ina na, jikinta, sai kuma ta fara sauƙe ajiyan zuciya.

Ummi kuwa, ferfesun zabi tayi, tare da dama kekyawan kunun kanwa mai ɗan karen daɗin yaji citta da kanamfari da kanwa.
Kana ta daka mazarƙoila ta zuba a ciki a madadin Sugar.
Babban flacks ta cika da kunun.
Kana ta juyo ferfesun zabi guda biyu cikin Foodflaks mai kyau.

Tuƙeƙƙen tuwon masarar tsari, mai tauri tayi, da kuma miyar ɗanyar kuɓewa da man shanu sai kifi da nama yasha citta da yajin daddawa sai ƙamshi yakeyi.
A Foodflaks ta saka,
sai kuma gashesshen jan nama, anyi Normal gashi irin na mutanen da.
Wanda murhun garwashi ta hura ta gasashi.
Sai kuma tea data tafasa ta tsula zuma da citta a ciki.
Shi kuma tasa a ƙaramin flacks.

Jerasu tayi a manyan tray guda biyu.

Sai lokacin kuma Sara ta iso nan suka fara haɗa wani girkin.

Sheykh kuwa a hankali ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye.
Tana cikin bathtub ɗin shi kuma yana ta woje.
Zubda ruwan yayi tare da ruggumeta a hankali yace.
“Zamu ƙara wani ruwan ɗumin kinga wannan duk kinyi masa fitsarin jini a ciki, duk kin ɓatashi raguwa kwai sakaliyar Ummey”.
Ƙara tsune kanta tayi jikinsa, tare da manne ƙirjinta da nashi wai bata son yaga breast ɗinta.

Wani ruwan ɗumi ya kuma sawa, kana ya zaunar da ita ciki.

Sannan a hankali yace.
“Aha Gud gerl kiyi wonka da kyau, in kin gama jin ɗumin ruwan sai kiyi wonkan tsarki, kin iya ai ko?”.
Ya ƙare mgnar yana kallonta, cikin sanyi ta gyaɗa mishi kai still hawaye na zuba, a hankali yace.
“To niyar wonkan me zakice”.
Shiru tayi bata kulashi ba kuma bata kalleshiba sai hawayen da takeyi.
“Okay to bari in shigo muyi wonkan tare sai in koya miki”.
Ya faɗa yana sako ƙafarsa cikin bathtub ɗin da sauri tace.
“Na’iya”.
fuskarta ya ɗan tallabo tare da cewa.
“Kin iya me?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button