Cikin mamaki Shatu ta zazzaro idanunta woje tare da cewa.
“Hehhhhh…!
Ga masu buƙatar biyan kudi littafin mutanen Niger ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 in kun biya ta wurinta ita zata turo min number ku in saku cikin group.
By
*GARKUWAR FULANI*
????????????????????????????????????????????
????️????????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 7
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????️????????????????????????????
Littafina na kuɗine, turo 1k domin karanta part 1 cikin mako biyu, ko ki turo 300 domin karanta part 1 a kwanaki talatin, da izinin ubangiji. Turosu ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank, Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta number da nake whatsapp dashi. 09097853276, in da hali bana son kati, amman in babu dama turo katin ba matsala, domin wani baida damar turowa ta bank ac.
Ayyah masuyi mun voice note Dan Allah ku rinƙa ɗaga murya, baku saniba ko inada matsalar kunne bayan na idon. In kinga kinyi min mgn ban amsaba wata ƙl fahimceki bane, ko kuma mgnarki bata da amsa a wurina, kana abubuwa suna min yawa, irin asha hira a chart ɗin nan bazai yiwuba, kuyi haƙuri masoya, yawan maimata min slm ince wslm ayi sama da sau goma yana sa in share mutun tsakani da Allah sabida kamar bashi da abin faɗane so Please na tuba,???????? a ɓari kada kice ina muku wulaƙanci.
Ido ta zazzaro tare da cewa.
“Hihhhhhhh, ya dahu?”. Kanshi ya rausayar tare daci gaba da ɓare kwan saida ya ɓaresh tas ya fito subul gwannin ban sha’awa, sai turiri yaketayi, Junainah ya miƙa.
“Karɓi kici kiji mana, kwan ya nuna ne Ƙanwaliya”.
Da sauri tasa hannu, zata amsa, cikin sanyi Aysha tace.
“Ke uwar kwaɗayi bazaki ciba”.
Rau-rau tayi da idanu alamun zatayi kuka, shi kuwa Ba’ana fuskarshi ya haɗa tare da kafeta da ido, da sauri tayi ƙasa da kanta, tana mai wasa da ƴan yatsun hannunta, dubanshi ya maida kan Junainah tare da cewa.
“Kici abinki Junainah”. Fuskarshi ya ƙara haɗawa jin Aysha ta kuma cewa.
“Dan Allah Ya Ba’ana kada taci”.
Ba tare daya kalleta ba, tace.
“Kema zakici ai bare ita”. Da sauri ta ɗago kanta tare da girgiza kan tace.
“A a ni kam ngd bazanci abinda ban san da me aka dafashi ba”.
juyowa yayi ya kalli Junainah da tuni ta fara cin kwanta, tana lumshe ido baki cike da kwan tace.
“Ya Ba’ana bari inje cikin gida in kawo mana yaji mai daɗi Addana bata cin kwai saida yaji”.
To yace mata, tuni ta juya tayi cikin gida.
Kallonshi ya maida kan Shatu cikin haɗe fuska yace.
“Mata kina tunanin zan cutar da kene?”.
A hankali ta jujjuya mishi kai alamun a’a, gyara zamanshi, yayi tare da cewa.
“To baki yarda dani bane?”.
A hankali ta buɗi bakinta tace.
“A’a ni dai tsoron abun naji, ka toni rami mai danshi da sanyin yashin damina, ka binne ɗanyen kwai mai sanyi ka fito dashi da zafi a dafe ni kam ina tsoro ban san da wutan me ka dafashiba”.
Fuskarta-ta yayi da kyau kana, ya fara magana.
“Ki yarda dani Mata, bazan taɓa cutar dakeba a rayuwa, duk abinda zakiga inayi, zanyine dan kare lfyarki da kuma baki kariyar. Jikin ki, kici kwannan, babu abinda zai miki”.
A hankali tace,
“Ni bana cin kwai dama, kuma ai shi kariya Allah ke hadashi ga dukkan bayinsa”.
hannu yasa ya amshi robar dakekken yaji da Junainah ta miƙo mishi, wacce yanzu ta dawo wurin.
Wani kwan ya kuma ɓare mata, ya miƙa mata, tanaci tana lumshe ido saida taci biyar, sannan tace.
“Ya Ba’ana na ƙoshi”. Shatu ya ɗan kalla tare da cewa.
“Saura biyar kuma nakine, in kin shiga gida kicishi, sannan kuma akwai wani haɗin maganin da zan kawo miki kiyi amfani dashi. Ni yanzu zan tafi”.
Kai ta gyaɗa mishi alamar to, kana kuma tace.
“Ina zakaje yanzu? Tunda naga lokacin tafiya kiwo dai ya wuce”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Zan shiga ƙauyen Bonon ne”.
Da mmki a fuskarta tace.
“Ya Ba’ana me zakayi kuma a ƙauye Bonon garin masafa kafurai ƙabulun Ɓachama”.
Ido ya zuba mata har saida taji tsoronshi a hankali yace.
“Kema watan watarana zakije, ki tuna da kyau Mamata ƙabilar ɓachama ce, ƴar garin Bonon kinga kuwa dole inje can tunda kawuneina ƙannen Mama da yayunta da iyayenta duk suna can”.
Ya ƙarishe mgnar kamsr yaji zafin zancen ta,
ganin hakane yasa a hankali tace.
“Kayi haƙuri”. Kai ya juya mata alamar babu damuwa.
Daga nan ya juya ya tafi, ita kuwa tacewa Junainah su shiga gida.
Suna shiga cikin gidan ta harari Junainah tare da kai mata bugu cikin faɗa tace.
“Hegiya kwaɗayayya maza ki zubar da sauran kwanan jakar yarinya ai sai ya ciyar dake guba tunda kince ke kwaɗayayya ce”.
Ihu Junainah ta kurma tare da cewa.
“Wayyoooooooo Inna kin ganta ko tana cin zalina”. a guje tayi gaba, ita kuwa Shatu tabi bayanta da sassarfa tana cewa.
“Wallahi sai kin zubda ƙoyayen nan”.
A haka suka isa har gaban Ummey da inna da suketa tafasa nonon da aka tatsa a sanyin safiyar yau, wanda a ƙalla ya kai jarka goms sha uku, so masu gidajen fura da nono na cikin Shikan ɗin nema suke saya, dan matan gidan Bappa kab bai lamunce da zuwansu tallan nono ba.
Inna ce tayi saurin kare Junainah dan saura ƙiris ta abka cikin tafasasshen nono da yanzu aka sauƙeshi, cikin tsoro tace.
“Kai ya ilahi ku dai bazaku zauna lfy ba”. Cikin nitsuwa Shatu ta zauna gefen Ummey nan ta labarta musu abinda ya faru da yadda ya dafa kwan ta ƙara da cewa.
“Amman da yake Junainah uwar kwaɗayi ce, a take a gabanshi taci kwai biyar cas tanaci tana lumshe ido”.
Cikin tarin mamaki Inna da Ummey sukayi ta salati tare da tafa hannu, a tare sukace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun, oh wannan yaron anya kuwa mutun ne ba shaiɗan ba?”.
Cikin rau-rau da ido, Shatu tace.
“Ni ina jin tsoronshi, bana sonshi bazan aureshiba, mutumin da komai nashi na tsafine Inna ki cewa Bappa ya rabani dashi mana”.
Cikin alhini, Inna tace.
“Rashin sani yasa Bappanki dama ke kanki kukayi mishi al’ƙawarin shine mijinki duk rintsi, gashi yanzu ya zame mana masifa.
Juyowa sukayi suka kalli Ummey da idonta ya ciki da hawaye a hankali tace.
“Dana sani wlh da ban bar haka ta faru ba”.
Shiru sukayi cirko-cirko a wurin, saida suka jiyo ƙaurin nono na zuba cikin murhune suka dawo haiyacinsu.
Kana suka juya suka ci gaba da aikin su.
A birnin Jalaluddin kuwa ƙarfe tara na safiyar ranar, dai-dai jirginsu Sitti da jikanta Sheykh ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki da sauran taro al’ummar Annabi masu zuwa Umrah.
Soyayyar da Sitti keyiwa Sheykh soyayyace mai tarin yawa, wanda ko uwa iya son da zatayiwa ɗanta kenan, tana ji dashi tamkar ranta, wata ƙil hakan baya rasa nasaba da tsananin kamanni da yakeyi da mahaifinta wanda shine baida lfy yanzu kuma shine tsohon Limamin Harami yanada zuriya mai tarin yawa yayansa na cikinsa zalla su arba’in da bakwai.
Bar jikoki da ƙanne da yaran yan uwa, sai dai ya tsufa sosai tun shekaru ashirin da suka gabata ya ɗaura babban ɗanshi wanda yake ƙanin Sitti ne uwa ɗaya uba ɗaya a matsayin shi.
Zuwa yanzu tsotsai tsufa ya kama Sarki Abdulkarim, Hairan wanda yake da shekaru ɗari da biyar a duniya, sai dai sufarsa suface mai tsabta tsuface da ka gani kasan an rainin ƙuruciyarta da tsoron Allah da ibada. Shiyasa babu gigita ko fita haiyaci, yana son diyarsa Sitti kakarsu Sheykh kenan so mai tarin yawa ko dan tayi nesa da shine, wacce ita kuma tun tanada shekaru ashirin da uku, Sarkin Musulmai na ƙasar Kautal na wancan ƙarnin yazo da babban ɗansa, Jalaluddin wanda a nan yaga UmmuKulsum Sitti kenan, ya sota, kuma Allah cikin ikonsa suka dai-dai ta, haka yasa kafin ya koma ma da amaryarshi ya koma dan sitti ta kafe ita dai tana son Bahaushen ga, duk da tasan yanada mata biyu, tace ai a gidansuma bata tashi ta samu mahaifiyarsu ita ɗaya ba.