Ita kuwa Aysha haka nan taji murmushi ya tsubce mata.
Shi kuwa Sheykh da sauri ya fita,
kanshi ya sunkuye yana gyara zaman Jabeer ɗin sa cikin wondon.
Yazo tsakiyar falon kenan, Ummi ma ta iso.
cikin wani irin azabebben kunya mai tsanani ya juya da tsananin sauri ya fuskanci ɗakin Aysha, gaba ɗaya jikinshi karkarwa yake dan wata iriyar fitinenneyar kunyar data rufeshi.
Itama Ummi cikin wani azabebben sauri ta juya a saba’in ta nufi komawa ɗakinta.
Shi kuwa Sheykh gani yake baya sauri hakanne yasa ya haɗa da sassarfa.
Yana shiga ya maida ƙofar gib ya rufe.
Da sauri Aysha ta ɗago kanta ta kallishi, da sauri tace.
“Lfy?”. Ganin yadda jikinsa ke kerma.
Bakin gadon yazo ya zauna, hannunshi yasa duka biyu ya dafe kanshi cikin muryar gsky da gsky cike da kunya yace.
“Aishhhhhhhh da wanne idon zan kalli Ummi Aish kinsa ta ganni dagani sai gajeren wondon, a suffar da ke kaɗaice kika dace da ki ganni da ita duk duniya.
Aish kin jawo ta fito da wannan rakin naki da kukan banza”.
Sai kuma ya juyo gareta jin tana mgn cikin shogwaɓa.
cikin sanyi tace.
“To ai zafi naji, shiyasa nayi ihu”.
Cikin takaici yace.
“A haka zamu tabbata kenan? Duk sanda zan kusanceki sai kinyi tamin ihu kina tara min jama’ar gari”.
Bakinta ta ɗan tura kana ta koma ta kwanta.
Shi kuwa Sheykh miƙewa yayi ya shiga Bathroom ɗinta.
Ummi kuwa ai fitsarin da batayi ba kenan, sabida wata iriyar fitinenneyar kunyar Sheykh ɗin data rufeta.
Dugungunewa tayi cikin borgon ta, tana tunanin tsawon shekaru ashirin da biyar kenan rabonta data ganshi da gajeren wondon.
Oh ni Zainabu meya kaini fita, gidan mata da miji gashi naje nasa yaro jin kunya, da matarsa, ashe shiyasa yaketa zirga-zirga da kora su Jalal oh Jabeer ka yafe mana mun shiga lokacin ka”.
Haka tai ta surutu har baccin ya kuma kwasheta.
Shi kuwa Sheykh yana shiga yayi wonka, towel ɗin ta da ya gani a ciki ya ɗaura.
kana yana fitowa ya kalleta cikin alamun tausasawa yace.
“Tashi kije kiyi wonka na haɗa miki ruwan ɗumi”.
Cikin sanyi tace.
“To ka tafi tukun”.
Kanshi ya gyaɗa kana ya fita,
da sassarfa ya koma Side ɗinsa.
Ita kuwa Aysha a hankali ta miƙe ta shiga bedroom ruwan ɗumi daya haɗa mata ta shiga ta zauna.
Kana tayi wonka sannan ta fito, riga kawai ta saka ta koma ta kwanta tanata numfashin gajiya a take tayi bacci.
Shi kuwa Sheykh ganin karfe huɗu yayine yasashi.
Fara nafilarshi.
Cameroon Yahunde.
Washe gari da safe. Ba’ana ne zaune gaban bokanshi, cikin tsareshi da ido cike da takaici yace.
“Yau kwana biyar kenan in binka ka bincika min lamarin Shatu na, sai kai tamin hanya-hanya. Shekaran jiyan can kace min haske yayi yawa baka ganin komai, jiya nace ka duba kaƙi dubawa me kake nufi da nine wai?”.
Cikin tsanani tsoro da shakku bokan ya kalli Ba’ana cikin sanyi da tsoro yace.
“Batun gsky bazan ɓoye maka komaiba tunda ka matsa ka sani.
Sai dai in kayi al’ƙawarin bazaka cutar da niba”.
Cikin faɗa Ba’ana yace.
“Kai ubanane ko uwata ko Shatu ce kai da zanyi maka alƙawarin bazan cutar da kaiba,. Ko ka gaya min ko in nuna maka ainihin waye ni.
Dan ubanka dubo min Mata ko inci uwarka”.
Cikin rawan jiki da sadaukar da rayuwarsa dan yasan ko ya yayi Ba’ana zai kasheshi cikin rawan murya yace.
“Koda zaka kasheni zan gaya maka gsky, ko kaso ko ka ƙi, gskya ta binne ƙarya, haske ya kori duhu.
mutumin can mijin Shatu shine gsky kaine karya shine haske kaine duhu.
Zan gaya maka gsky ko Allah zaisa ka yarda da wuri kada kayi makararran yarda irin nawa.
Babu wani makami sama da addu’a, kuma babu wani addini na gsky sama da musulunci, addini mai cike da ni’imomin duniya da lahira, Sheykh yafi ƙarfin ka domin shi Allah da manzasa ya riƙe, bazaka taba iya cutar dashi da komaiba a duniya har sai dai in dama Allah yan ƙaddara zai cutu.
Domin duk sihirina da mukayi kan cewa in ya kusanci Shatu yaji zafin dafin cizon kunamai, toshi wannan abun shegen daɗi yaji. Yakusance tun kwana huɗu baya, kuma daren jiyama kwana yayi tare da ita ya kusanceta yayi jima’i da ita babu abin daya sameshi saima lfy da girma da Jabeer ɗinsa ta ƙara dan ta samu gamsuwa da Shat..”
Bai ƙarasa zancenba ya kurma wani irin gigitaccen ihu mai azaɓan ƙarfin amo, sabida wani irin zabura da Ba’ana yayi ya caka mishi ƙahon rago a dai-dai kan ƙahon zuciyarshi.
Nan ya faɗi kwance jini na zuba cikin rawan murya na magagin fitar rai yace.
“Baka da nasara, kada kaje Nigeria in ka koma ka kai kankane, babu abinda zaka iya yiwa wanda yake riƙe da addinin Musulunci da gsky da al’ƙur’ani littafin Allah.”
Yana faɗin haka ya rai yayi halinsa.
Shi kuwa Ba’ana cikin wani irin masifeffen tashin hankali da kiɗima ya kurma wani ƙaƙƙarfan ihu tare da kiran Shatu da karfin kana yace.
“Mata ganinan dawowa duk da nasan da wuya in iya shiga masarautar Joɗa, amman dole zan faɗaɗa bincike na, zan zama dodon tsafin kaina zanzo na saceki, dole sai na aureki na kusanceki naji daɗin ni’imomin jikinki na baki ciki kin haifu dani, bazan yi renon banzaba ko nononki ban taɓa taɓawa ba, wani can yazo ya cinye min budurcinki dole zai ɗanɗani azaba mai girma, sai na sake yi mishi ka ciya dan kan uwarsa”.
Tulun tsafin ya jawo gabansa yafara aikin da kansa.
A can gefensu Bappa kuwa.
Ummey ce zaune Junainah na gefenta amaryar Bappa nayi mata kitso, cikin sauƙe ajiyan zuciya Ummey ta kalli Bappa dake gefensu yana al’walan yin walaha cikin sanyi tace.
“Bappan Shatu yaushe zamu koma Rugar Bani? Ina kewan Shatu, ina yawan mafarki da ita, ina son inje inda take”.
Murmushi Bappa yayi kana ya kalli Junainah dake cewa.
“Bappa ai ni dai Addana tace dan Allah Yah Al’amin ya kai mata ni, ina ka yarda?”.
Cikin sanyi ya gyaɗa mata kai kana ya juyo ya kalli Ummey cikin tausayawa yace.
“In sha Allah zamu koma Rugar Bani, amman da sauran lokacin komawarmu”.
A hankali Ummi tace.
“Zai kai kamar yaushe?”.
Cikin sanyi yace.
“In sha Allah zuwa wani ɗan lokacin”.
Kai Ummey ta jinjina dan ta fahimci ba rana kenan.
A can Masararutar Joɗa kuwa, wunin ranar Sheykh wasan buya yakeyi da Ummi sabida masifar kunyarta da yakejin.
Yau kwana biyu kenan da faruwar abin kuma, jikin Shatu yayi sumul yanzu bata jin ciwon komai.
Ummi kuwa wani tsumi na musamman ta haɗa mata na masarautar Joɗa tana bata safe da yamma kofi ɗaɗɗaya, ita da kanta ta gamsu da kyan tsumin sabida ita kanta takanji tana tsiyaya duk sanda ta tuna Yah Sheykh.
A hankali yake taku, har ya iso bakin corridor’n, kanshi ya ɗan turo, ya leƙa cikin babban falon, da sauri ya dawo da baya, sabida hango Ummi na tsaye tana miƙa wa Shatu wani abu a kofi.
Ido ya ɗan lumshe tare da cewa.
“Allah ya sani ina jin kunyan Ummi tayaya zan fito”.
Sai kuma ya ɗan leƙo, da sauri ya sako kai ya fito sabida hango Ummi bata wurin.
A hankali ya iso tsakiyar falon.
Ido ya ɗan zubawa Shatu dake kallonshi babu ko ƙebta ido.
Yayi masifar kyau cikin shigarss, gaba ɗaya ta kasa janye idonta kanshi.
Girarshi ɗaya ya ɗaga mata tare da cewa.
“Aishhhhhhhh ya dai? Kinada matsala ne?”.
Cike da mamaki tayi ƙasa da kanta tare da sake gajeren murmushi. Cikin sanyi tace.
“Ina kwana”.
Bakinshi ya ɗan taɓe tare da cewa.
“Bana so riƙe gaisuwarki, tunda ban kai aje a gaisheni ba.
Na lurama guduna kikeyi ko faloncan bakya son zuwa”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“To ba kai bane”.
Da sauri yace.
“Nine me?”.
bakin ta kuma turawa tace.
“Kaine kake min”.
Sai kuma tayi shiru, murmushi yayi kana ya matso kusa da ita.
gefenta ya ɗan zauna a hankali ya kamo hannunta ya manna kan wuyanshi tare da cewa.
“Aishhh.” Cikin kula ta kalleshi jin jikinsa zafi jau-jau a hankali tace.
“Yah Sheykh baka da lfy ne”.
Kanshi ya jinjina kana ya miƙa tsaye dan gudun kada wani ko wata yazo ya samesu a hakan, cikin sanyi yace.
“Nima ban saniba Aish amman yau tsawon kwana bakwai kullum da zazzafan zazzaɓi nake kwana.
Babu wanda ya sani da yake bani da gata, Umaymah na bata kusa, Mameyna bata kusa da ko ƙuda bazata bari ya sauƙa a kainaba.”
Ya ƙarashe mgnar jijiyoyin idanunshi na tsastsafo da wasu tafasassun hawaye masu ƙuna a zuciya.
sai kuma yayi sauri ya juya ya fita.