GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Cikin wani irin rauni, tausayi, so, shaƙuwa, kaunarsa. ta rakasa da ido, tabbas da Side ɗinsa ya koma da ta bishi a baya, sai dai kuma kash woje ya fita.

Da yamma suna zaune a falon Umaymah ta kira Ummi bayan sun gaisa ne tace.
“Ummin Jabeer Hajia Kubra na ba lfy tunda ta dawo auren Haroon, jiya mukayi waya da ita tace har an Bata gado. Amman an sallamesu yau da safe.
Shine nake so dan Allah keda Juwairiyya kuje ku duba min ita da jiki. Nima kaina in sha Allah na kusa zuwa da zaran baƙinmu sun gama komawa, zanzo da Aunty Hafsat da Rahma”.
Cikin kula Ummi tace.
“Ayyah Allah ya bata lfy. In Sha Allah kuwa zamuje mu dubota da jiki gobe”.

“Amin Amin, yau dan Allah kuje ku duba min ita”.
Umaymah ta faɗa cikin jin daɗi.
Sai kuma tace.
“Ya jikin ɗiyar tawa”.
Juyowa Ummi tayi ta ɗan kalli Shatu dake shan tsumin data bata tace.
“Uhuhh yanzu dai anyi lfy sai kuma tsoro da raki”.
Dariya sosai Umaymah tayi dan Ummi ta bata lbrin abinda ya faru wancan ranar.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Shifa ɗan naki”.
Miƙewa Ummi tayi ta nufi kitchen tare da yin ƙasa da murya tace.
“Uhumm kedai bari ai mun zama surkan juna wlh har yau ɗin nan ban kuma ganinshi ba.
Ni ina jin kunyarsa haka shima yana jin kunyata, itako ɗiyar taki sarkin raki ko a jikinta”.
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“To yar taki zakiwa faɗa ta kula da mijinta fa bata san irinsu ba in sunji mace basa iya dogon haƙuri”.
Dariya sukayi kana suka katse kiran.

Falon ta dawo dai-dai lokacin kuma Sara ta shigo.
Gefe ta zauna jin Ummi na cewa Jamil.
“Gobe in Allah ya kaimu zaka kaimu, gidan hajia Kubra aminiyar Umaymah mu dubota da jiki nida Juwairiyya”.
Kai ya gyaɗa alamar “To”.
Da sauri Shatu ta kalli Ummi cikin zumuɗin son fita tace.
“Yauwa Ummi nima zanje”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Eh ki tambayi mijinki in ya barki sai muje”.
Kai ta ɗan kauda tare da cewa.
“Kai dai Ummi sai na wani tambayeshi ai bazaiyi faɗaba tunda aiken Umaymah ne”.
Da sauri Ummi ta jujjuya kai tare da cewa.
“A a badani za’ayi hakabs kam gsky ki dai tambaya in ya amince kinje in ya hana ki haƙura muje Salim alim”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Toh zan gwada Allah yasa ya barni”.
Amin Amin sukace.
Kana Ummi ta ɗan kalli Sara dake takure a gefe cikin kula tace.
“Saratu ya dai zazzaɓin ne?”.
Cikin rawan sanyi ta gyaɗa kai.
Shatu ce ta kalleta cike da kulawa tace.
“Allah sarki sannu Sara kinsha mgni kuwa?”.
Cikin rawan murya irin na mai fama da fitinenne masassaran cizon sauro tace.
“Naje asibitin mu na cikin masarautar Joɗa an min allurai, to kuma duk jikina rawa yakeyi.
Shine nace bari in zo in gaya muku, bazan iya zuwa muyi girkikiba.
Amman naje na samu Huwaila zata zo ta tayaku”.
Cikin tausayawa Shatu tace.
“Ba komai Sara Allah ya baki lfy je ki kwanta”.
Cikin kulawa Ummi tace.
“Allah ya sauwaƙa ko kada kice zakizo gobema Huwailan zata ke zuwa tana tayamu sai kinji sauki sosai.”
To tace kana ta miƙa ta tafi.

Huwaila ɗayace daga cikin hadiman Sashin Aunty Juwairiyya wacce asalinta hadimar Hajia Mama ce.
Kuma har gobe a sashin Hajia Mama take kwana.
Ita da gidan Aunty Juwairiyya sai in zatayi girki tana gamawa take tafiya.
Sai Indo ita kuma a sashin Aunty Juwairiyya take, kuma asalinta daga masarautarsu Sitti aka kawota da ita.

Huwaila itace idon Hajia Mama a sashin Yan Jafar, shiyasa duk motsinsu ta sani sabida itace yar rahoto ko lokacin ciwon Shatu taji Aunty Juwairiyya na Umaymah a wayene daga nan taje tana fesawa Hajia Mama, dai-dai lokacin kuma yar rahoton gefen Gimbiya Saudatu na jinsu shiyasa mgnar ta isa ga Gimbiya Saudatu.

Su kuwa nan sukaci gaba da hirarsu.

Yau Sheykh bai dawo da wuriba sai ƙarfe goma na dare ya dawo.
Ba kowa a babban falon haka yasa ya rufe ƙofar.
Kana ya wuce Side ɗinsa jiki na karkarwa sabida masifeffen zazzaɓin daya zame mishi abokin rayuwa in dare yayi tun randa ya kusanci Shatu na forko yau kusan mako biyu kenan.
Sosai zazzaɓin ya shiga jikinsa sabida har ya ɗan faɗa.

Jiki na rawa ya ɗan rage kayan jikinshi,
a daddafe yayi al’wala kana yazo ya kwanta.

Haka ya kwana da masifeffen zazzaɓin ya dai sa a ransa gobe zaije yabinciki lfyarsa.

Washe gari da safe.
Bayan sun gama aiki.

Ummi ta kalli Huwaila cikin kula kamar yadda ta saba da Sara tace.
“Yauwa ga naki tafi dashi kije ki huta sai anjima kizo muyi na dare dan zamu fita anguwa yau ɗin”.
Cikin wani irin kallon ƙasa-ƙasa ta kalli Ummi tare da cewa.
“To sai kun dawo”.
Tana faɗin haka ta fita.

Tana fita ba jimawa su Jalal suka shigo.

Dinning area suka wuce kai tsaye.
Dai-dai lokacin Shatu ma ta fito cikin shigar doguwar riga mai masifar kyau da taushi sai ƙamshi take bazawa.

Gefen Ummi ta zauna kana ta kalli Jalal dake cewa.
“Adda Shatu Hibba ta kiranki bakya ɗagawa”.
Kai ta ɗan juyo ta kalleshi tare da cewa.
“Fushi nayi da ita ai”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu.
Ita kuwa Shatu ido ta zubawa kular soyayyan Arish ɗin da Ummi ta buɗe.
da sauri ta rufe idonta cikin sanyi tace.
“Ummi wannanfa waya kawo mana shi?”.
Jamil ne ya amshi zancen da cewa.
“Wa kuma zai kawo mana tunda duk wanda ya kawo korarsa da abinsa kikeyi”.
Cike da mamaki da tsoro ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi waya kawo mana wannan?”.
Dafe kai Ummi tayi tare da cewa.
“Babu wanda ya kawo mana shi Shatu.
A nan mukayi girkin nida Huwaila”.
Shiru Shatu tayi tare da jan dogon numfashi kana tace.
“Ohooooooh Allah sarki ba laifi Ummi rufe kular”.
Cike da mamiki suka haɗa baki wurin cewa “Meyasa?”.
Miƙewa tsaye tayi tare da tattara kulolin duk tayi cikin kitchen dasu tana mgnar zuciya.
“Yah ilahi ya mujibadda’awati meyasa? Me mukayiwa Aunty Juwairiyya?”.
Ajiye abincin tayi gefe.
A take ta fara kiciniyar yi musu wani girkin.

Su kuwa a Dinning area da ido suka rakata.
A hankali Ummi ta biyo bayanta.
Ganin tana jajjaga kayan miya ne, yasa Ummi matsowa kusa da ita kana tace.
“Shatu meyasa zargina kikeyi ne nima ɗin?”.
Cikin sauri tace.
“A a Ummi har abadan bazan zargeki ba.
Amman naga abinda nake gani a abincin Hajia Mama da Aunty Juwairiyya ko na wasu gidajen in an kawo mana.
Ummi akwai mgni a ciki.
Ban zargekiba Amman zargina ya ƙara ƙarfi kan Aunty Juwairiyya duk da kareta da wonketa da kikeyi da nunamin ita yar uwarsuce.
Tunda kinga dai yar aikinta ce tazo ta tayaki aiki mukaga abin nan”
Wani irin dogon nazari da tunani Ummi ta faɗa can kuma sai ta nisa tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil.
Shatu anya kuwa matsalar nan Juwairiyya tasan da ita, anya ba zagon ƙasa akeyi mata ba ita kanta da mijinta da ƴaƴan taba”.
Da sauri ta juyo ta kalli Ummin tare da cewa.
“To Ummi ina dai Huwaila yar aikinta ne?”.
Da sauri ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Allah sarki Juwairiyya ashe bamu saniba magautan sun samu damar tura wakilai sashinki, sunaci gaba da rarakarmu”.
Cikin sanyi Shatu tace.
“Ummi me kike nufi?”.
Cikin sanyi da zubda hawaye tace.
“Juwairiyya tasha yin kuka tana rantse min da abunda zai kasheta bata san me kike gani a abincin taba.
Tace min Ummi inrasa wanda zan cutar sai ƴan uwana.
Shatu shiyasa Juwairiyya tayi fushi ta dena zuwa sashinki.
Sai yanzu na tuno asali Huwaila hadimar Hajia Mama ce, daga baya ta bawa Juwairiyya ita wai aiyukanta sunyi mata yawa”.
Wani irin ajiyan zuciya Shatu ta sabƙe tare da cewa.
“Uhummm makashinka taburmanka, Ummi ko dai har yanzu baki yarda da wacece Hajia Mama ba, ko baku cemin ba ita mahaifiyar Yah Sheykh ba na sani ba ita ta haifeshi ba kuma nasan kuma kun san ita majirace, sai dai bansan dalilinku na zuba mata ido kuka meda kanku baku saniba, wata ƙil ƙofar rago zakuyi mata.”
Sai kuma ta juyo taci gaba da aikinta tare da cewa.
“Kwantar da hankalinki Ummi barni da ita ai nida aita kar tasan kar.
Jeki zauna bari in tafasa mana ko indomei”.
To Ummi tace kana ta fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button