Cikin ƙarfin hali yake tuƙin, sabida gaba ɗaya zazzabin ya rufeshi ji yakeyi duk gabbanshi kamar ana sossoka mishi allurai.
A hankali yasa hannunshin ya kashe A/C’n motar sabida sanyin da yakejin har jikinsa na rawa.
Cikin ƙarfin hali ya juya akalar motar tasa ya nufi Valli Hospital.
Wayarshi ya ɗauka Dr Kabir ya kira.
“Assalamu alaikum,”.
“Wa alaikassalam, Sheykh Barka da yamma”.
A takaice yace.
“Barka dai Dr Kabir kana Valli ko?”.
Cikin kula tace.
“Eh ina nan”.
“Na’am to gani nan zuwa banda lfy fa”.
“Subahanallahi, to sai ka iso, ko dai inzo in dubaka a gida?”.
“A a gani ma na kusa”.
Yace mishi dai-dai lokacin da ya
Iso bakin wani irin tamfatsetsen Hospital mai masifar kyau da girma.
Valli Hospital kenan.
Da sauri mai gadin ya buɗe mishi gate ɗin.
Tare da ɗan matsawa gefe.
Cikin rawan sanyi yayi parking cikin rumpar da sunanshi ke rubuce a sama.
Da sauri mai gadin ya buɗe mashi marfin motar tare da cewa.
“Barka da zuwa mai gida”.
Cikin sanyi yace Barka dai kana ya fito.
A hankali ya ɗan jingina da jikin motar yana kallon farfajiyar asibitin.
Wani irin ƙaton filine mai girma.
Wanda akayi mishi ƙawanya da bishiyoyin namijin gwanda.
Kana ƙasa kuma fulawowine a jere iya ganin mai hange wani faffaɗan titine ke malale, wanda tsakiyarshi dogayon ƙarafunan wuta ke jere iya ganin ka.
Can gefen dama wani tamfatsetsen gidan samane mai zaman kashi ya kai hawa uku.
Gefen hagu kuwa wata hanyarce ta kuma shiga.
Sai wani irin tamfatsetsen gini mai masifar kyau inda marasa lfy ke kwanci gefen mata.
Komai kalan kayan asibitin royal blue and white.
Can gaba kuwa kuwa jerin Offices ɗin Dictors ne.
Sai Side ɗin Nurses.
Tsab-tsab cikin asibitin.
Sai motoci keta gilmawa.
Haske kamar rana.
Kai faɗin tsatuwar asibitin sai wanda ya gani.
A hankali ya nufi gefen Office ɗin Dr Kabir.
Yana shiga Nurses ɗin dake zirga-zirga tsakanin wurin suka rinƙa ɗan bashi hanya suna.
“Ur welcome sir”.
Kai kawai yake jinjina musu kana ya wuce su wuce dan zazzaɓin ya fara damunshi sosai.
Yana shiga Office din Dr Kabir da sauri ya miƙe tare da cewa.
“Barka da zuwa Sheykh”.
A hankali ya zauna tare dafe kanshi.
Cikin sanyi yace.
“Kabir test nake so ayi min yanzu-yanzu gaba ɗaya na rasa meke damuna kullum da zazzaɓi nake kwana”.
Cikin kula Dr Kabir yace.
“Tsawon kwana nawa ya fara maka?”.
Jingina kanshi yayi da jikin kujerar tare da cewa.
“Two weeks ago”.
A hankali ya gyaɗa kanshi kana ya juya ya koma kan table nashi abubuwan aikinshi ya ɗauko kana yazo ya zauna kusa dashi, cikin kula yace.
“To test ɗin me da me za’ayi maka?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Widal, Mp, Emergency, fa.”
Kai Dr Kabir ya jinjina kana ya kamo hannunshi.
Ba musu ya miƙa mishi bayan ya tattare gariyar tasane.
Ya ɗebi jininsa.
Lab ya wuce Direct. shi kuma ya zauna a nan yana jiranshi.
Yana zuwa yace, to jinin ogonane da kanshi kuma Emergency ne.
ai kuwa cikin awa ɗaya suka gama bicikan jininsa kab. Bayan sunyi ƴan rubuce-rubucen sune.
Ya amshi takardar ya koma Office ɗin sa.
Inda ya barshi nan ya sameshi sai dai yanzu, yana karatune, ganin ya dawone ya ɗan sahirta.
Takardan ya miƙa mishi.
A hankali ya gyara zamanshi kana ya meda idonshi kan takardar.
Tests result ɗin yake dubawa.
Cikin sanyin zazzaɓin yace.
“Widal risult ɗin bani da matsala, 40% da 80% kaga kenan bani da Typhoid”.
Kai Dr Kabir ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh gsky kam babu matsalar Typhoid wanda ni da fari shi nafi zargi”.
Kanshi ya sunkuyar tare da buɗe fefa ta gaba yana cewa.
“Nima haka naiyi tunani”.
Rubutun ya zubawa ido ganin. Mp 1+.
Kanshi ya ɗago ya kalli Dr Kabir a hankali yace.
“Ina da Malaria’n amman ba sosai ba 1+ baici ace ina jin irin wannan zazzafan zazzaɓin ba. To me matsala ta?.”
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Dr Kabir.
Cikin kula Dr Kabir yace.
“To yanzu dai bari muyi allurar Malaria’n mu gani wata ƙil jininka bazai juri 1+ ɗin ma zai wahal da kai.
Gashi dama na biya Pharmacy na amso allurar bari inyi maka kawai muga zuwa gobe ya abun zaiyi”.
Cikin gamsuwa da hakan yace.
“To”.
Hannunshin ya kuma kamowa ya tsira mishi allurar.
Kana ya bashi wasu magunguna a take a nan ya shasu.
Nan sukayi sallama ya tafi gida.
A gida kuwa tuni su Shatu sun shiga dan basu dawo da wuriba shiyasa suna dawowa basu tsaya hiraba.
Shiru ya samu falon babu kowa.
A hankali ya wuce Side ɗinsa.
Dan wani irin masifeffen karkarwa da jikinsa ya fara.
Ga wani irin tsuka da zazzaɓin ke mishi.
Da kyar ya rage kayan jikinshi.
A daddafe ya shiga yayi fitsari yayi al’walan kwanciya bacci.
Yana fitowa ya kwanta.
Kar-kar haka yake rawan sanyin masifeffen zazzaɓin nan kamar zai ɗauke ransa.
Allurar tamkar ƙara mishi ciwon tayi.
Haka ya kwana wannan ranar da masifeffen zazzaɓin.
Ana kiran sallan forko, yaji zufa na karyo mishi alamun zazzaɓin zai ɗan sauƙa kamar yadda yake mishi kullum.
Ai kuwa lokaci ɗaya zufa ta jiƙashi.
Jikin sanyi ya tashi AC ya kunna kana ya dawo bakin gadon ya zauna yana maida numfashin jin daɗin sanyin ac lokacin ɗaya kuma ya jishi garau kamar bashi ba, ƙamshin turaren jikinshi da sanyin ac yasashi jin wani irin sassanyan yanayi yana rufeshi.
Kusan 5 minute yayi kana ya miƙa ya shiga Bathroom.
Allah ya sani da Shatu na kusa dashi zai raɓeta ko zaiji daɗin rayuwarshi.
Ruwan sanyi ya watsa kana ya fito. Da al’walan sa.
Nafila ya fara. Kana ɗaya sallame ya fara karatu.
Jin anyi asslatune ya sashi fita ya nufi Masallacin masarautar Joɗa.
Ƙarfe bakwai dai-dai ya turo ƙofar falon jiki a mace. Wani fitinenne yanayi nata ɗawainiya dashi.
Yana zuwa tsakiyar falon Ummi na fitowa cikin kitchen.
Da sauri ya sunkuyar da kansa cike da kunya.
Domin tun randa Ummi ta ritsashi ya fito ɗakin Shatu bai sake yarda sun haɗa idoba sai yanzu.
Cike da kunya yace.
“Uhmm Barka da safiya Ummi”.
Cikin kula da mamaki, ramarsa ita kuma Ummi ta bishi da kallo tare da cewa.
“Barka dai Sheykh lfy kuwa, meke damunka”.
Murmushi yayi cike da kunya yace.
“Uhum Ummi me kika gani?”.
Cikin tausayawa tace.
“Sheykh kaga yadda ka rame kuwa, anya kanada lfy kuwa?”.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana a hankali yace.
“Lfy ta lau Ummi kawai dai ɗan zazzaɓin dare ne ke yawan damuna, in gari ya waye kuma sai inji sauƙi”.
Da sauri tace.
“Ina kuwa sauƙi Sheykh nadai lura sam baka son cin abinci.
gashi gaba ɗaya ka faɗa”.
Ci gaba yayi da tafiya tare da cewa.
“Ina ci fa”.
Da sauri tace.
“To kaje kaga likita ne?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh naje. Jiya da dare”.
Cikin sanyi tace.
“To Allah ya sauwaƙa”.
Amin yace kana ya wuce.
Ita kuwa Ummi sosai taji ba daɗin ganin yadda ya ɗan faɗa.
Suna cikin yin aikin breakfast ita da Shatu.
Huwaila ta shigo kamar yadda Sara take zuwa tayasu aikin.
Kai Shatu ta jinjina kana ta nuna mata Arsh tace.
“Fere minshi in kin gama kije kawai sai anjima kizo yanzu mun gama”.
Cikin kallon ƙasa-ƙasa Huwaila tace to.
Bayan sun gama komai na aikin breakfast sun shiryashi a Dinning table ta kalli Shatu data nufi ɗauki ta.
“Zo ki kaiwa Sheykh abincinsa kinga ba lfy ce da shiba”.
Cikin gajiya tace.
“Ayyah Ummi to bari inje in watsa ruwa wlh zafi nakeji.
Watsawa kawai zanyi yanzu zan fito”.
Kai kawai Ummi ta gyaɗa mata.
Bayan tayi wonka, mai kawai ta shafa ta fesa turare.
Ta zura doguwar riga ko bra bata saba.
Jin Ummi na kiranta
tana fitowa ta samu Jalal, Jamil, Affan, Sulaiman Imran duk suna yin karin kumallo su.
Tray’n da Ummi ta miƙa mata ta amsa kana ta wuce falonshi.