A hankali a haka dai rayuwa tayi ta tafiya, lokacin nata shuɗewa.
Zazzaɓin dare kuwa kullum Sheykh kwana yakeyi dashi, asuban fari ya worke.
Shatu na kawo mishi breakfast zai tsareta da salonshi mai gigitarwa.
Sai ya zama in ma bai sameta da safe ba.
Tofa bayan azahar sai ya ritsata.
Zuwa yanzu ya dena bata mamaki sai al’ajabi yake bata sabida ta lura in dai akan wannan fanninne to malamine mai zaman kanshi kullum da salon darussan da yake koyar da ita.
Ya ɗan rame alamun baida cikekkiyar lfy ga kuma aikin fatauci.
Zuwa yanzu kuwa Shatu ta gama gane cewa Huwaila munafukar Hajia Mama ce.
Ita takeyiwa aiki ta gano sam Aunty Juwairiyya Bata san komaiba zagon ƙasa akeyi mata.
Yanzu kusan wata biyu kenan Da Sheykh yake fama da wannan zazzaɓin da yasha mishi mgnin ya binciki kansa har ya gaji bai gano meke damunsa ba.
Yau jumma’a ne, bayan an taso sallan Jumma’a ne yana kwance a ƙasa bisa carpet.
Ita kuwa Aisha tana kwance gabanshi.
A hankali ya kamo hannunta ya manna da bakinshi kiss ya sake mata a hankali yace.
“Gobe Umaymah da Aunty Hafsat da Rahma zasu zo, jirgin magriba zasu biyo.”
Cikin jin daɗi tace.
“Eh haka Umaymah tace min, zasu zo da Ishma ko?.”
Cikin wani irin sauri.
Ya Tashi zaune y da sauri ya kamo hannunta tafin hannun nata ya zubawa ido cikin mamaki ya ɗago idanunshi ya kalleta cike da al’ajabi da kaɗuwa ya kuma kallon tafin hannunta na hagu.
Ita kuwa ido ta zuba mishi ganin yadda yake kallonta.
Cikin son tabbatarwa yace.
“Aish cik…!?
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k zaki turo ta 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. In normal group kikeso na 300 ma ta nan zaki turo, in baki da damar turawa ta ac kuma to nayi miki uzuri ki sayi katin Mtn na ɗari uku kacal ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsapp 09097853276 bana son VTU KADA KIYI min bana so.
By
*GARKUWAR FULANI*[3/31, 9:24 PM] +234 806 559 0880: "Ta Suma ne!". Da sauri Sheykh ɗin ya taso, tare da sa hannunshi ya amsheta, da sauri ya juya.
Itama Umaymah da sauri tabi bayanshi.
Side ɗinsa ya koma da sauri key ɗin motarsa ya ɗauka Umaymah na biye dashi a baya kana Haroon ma na biye dasu a baya.
Shatu kuwa cikin wani irin kuka mai rauni daya kubce mata ta koma bakin gado ta zauna gaba ɗaya jikinta kerma yakeyi.
Shi kuwa Sarkin al’adun suna, da rarrafe ya fita ya bar ɗakin yana fita falon ya miƙe a guje ya bar Part ɗin da sauri Jalal ya mara mishi baya, kafinma ya bar Part ɗin ya damƙeshi Part ɗinsu ya wuce dashi.
Mamma kuwa da Gimbiya Aminatu gefen Shatu suka zauna.
Hannunta tasa bisa kafaɗarta a hankali tace.
“Kiyi haƙuri Aysha in sha Allah babu abinda zai samu ƴarki da izinin ubangiji, zata samu lfy”.
Cikin rauni murya na rawa ta juyo ta kalli Mamma ido cike da hawaye tace.
“Mamma me tayi musu, da zasu cutar da ita ba tare da haƙƙinta ba, shike nan yanzu duk magautan Yah Sheykh sai su dawo kanta, kawai dan ta kasance ƴarsa, Mamma ya zamuyi”.
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
“Babu komai Shatu da izin Ubangiji baza suci nasara a kankuba”.
Aunty Rahma da Aunty Juwairiyya da Jannart kuwa jiki a mace suka koma falon Shatu suka zauna.
Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi.
Khadija da Aunty Amin kuwa tsoron al’amarin masarautar Joɗa ne ya rufesu.
Da sauri Mamma ta miƙa ganin Shatu ta zabura ta miƙe tsaye da sauri tare da tallabe breast ɗinta.
“Aysha zauna”.
Murya na rawa tace.
“Mamma maman Afreen na tsastsafo da ruwa,
Ina Yah Sheykh ya tafi da ita? Ni kam zanje inga halin da take ciki”.
Ajiyan zuciya mai nauyi Hajia Kubra dake tsaye gefen Mamma tace.
“Asibiti suka tafi, kuma insha Allah zataji sauƙi”.
Kai Gimbiya Aminatu ta gyaɗa tare da cewa.
“Sosai ma kuwa tunda har kikaji haka to ta farfaɗo ne”.
Dai-dai lokacin kuma Umaymah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin da Sheykh da wasu manyan likitocin su na Valli Hospital Suka shiga da Afreen a sume.
Ta sauƙe wata ƙaƙkarfan ajiyan zuciya jin kukan da Afreen ta cillara da ƙarfi.
A cikin ɗakin kuwa.
Kusan a tare sauran likitocin suka sauƙe ajiyan zuciya tare da ɗagowa suna kallon Sheykh daya ruggumeta jikinshi tare da cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!”.
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Dr Lukman Ibrahim babban likitan yara kenan na asibitin na cewa.
“Ina Maman baby a yi maza a bata mama tasha shi zai taimaka wurin ƙara ƙarya ƙarfin gubar”.
Da sauri Sheykh yace.
“To”.
Kana ya juya.
Yana fitowa Umaymah tabi bayanshi.
Tana tambayarshi.
“Ta farfaɗo ko?”.
Cikin ƙara saurin tafiyarsa yace.
“Eh Umaymah”.
Suna shiga motar yaja da sauri ya nufi masarautar Joɗa a guje.
A can part ɗinsu Jalal kuwa.
Wani irin gigitaccen mari Jalal ya yarfawa Sarkin al’adun suna.
Wanda yasa shi jin fitsari ya kubce mishi.
Ba tare daya gama dawowa hayyacisa ba ya kuma jin saukan wasu tagwayen maruka a gigice ya kurma ihu tare da cewa.
“Wayyoooooooo Allah na na shiga uku ni ilu Jalaluddin kayi haƙuri”.
A fusace Jalal yasa ƙafarshi ya taɗe sawunshi har saida ya faɗi tib! A ƙasa hannunshi yasa ya tallabe ƙeyarsa tare da sakin wani gigitaccen ihu.
Da sauri Jalal yasa ƙafarshi ya taƙa yatsun hannunshi tare da cewa.
“Sheeeyyt rufe min baki, uban me kuka sa a cikin fatar ragon sunan?”.
Cikin kerma da zare ido yace.
“Wlh bani ne na sakaba”.
Ƙara taka yatsun yayi tare da murjesu da ƙarfi yace.
“Me akasa a cikin fatar ragon? kuma waya saka? Nawa kuma aka biyaka?”.
Cikin sakin fitsarin azaba yace.
“Madarar fiyafiya ce aka saka cikin fatar. Hajia Mama ce ta saka! Dubu ɗari bakwai ta biyani”.
Wani irin murza yasun yayi da ƙarfi tare da cewa.
“Okay bari in daddage yatsun hannun da zaiyi kisan kai da amsar kuɗin yin kisan kai ɗin”.
Zuwa yanzu ya gigice ihu kawai yakeyi, shi kuwa Jalal rufe Windows ɗinsa yayi ya mishi ɗan karen duka.
Kana ya kira ɗaya daga cikin ma’akatansu na jami’an sirri na soja yazo ya tafi dashi.
A nan falon Shatu kuwa, a hankali Jamil da Yah Jafar Suka koma suka zauna.
Yana gaba Umaymah na binshi a baya a haka suka shigo.
“Aish Aish Aysha!”. Ya ɗan ƙare kiran da ƙarfi.
Da sauri Shatu ta miƙe da sauri ta nufo falon.
Ummi da sauran na biye da ita a baya.
Aunty Amina da Khadijah kuma suna zaune.
Da sauri ya kamo hannunta bisa kujera ya ajiyeta gefen Aunty Rahma da sauri yace.
“Bata nono yi sauri”.
Da sauri tace to tare da fara kiciniyar ɗago rigarta.
Ina gani yake bata sauri shiyasa cikin sauri ya ɗaura mata ita kan cinyarta.
Kana yasa hannunshi ta baya ya zuge zip ɗin rigar yayi ƙasa da ita.
Hannunshi yasa ya fito da breast ɗinta na dama.
Tare da ɗago kan Afreen daketa fidda wani irin numfarfashi alamun har yanzu numfashin bai dai-dai taba.
Da sauri kuwa ta damƙi nonon tare da fara zuƙa.
Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe a tare shi da ita.
Lokaci ɗaya kuma hawayensu ya kwaranyo bisa fuskokinsu.
Cikin sanyin murya yace.
“Alhamdulillah Aish kada kiyi kuka kiyi mata addu’o’in samun lfy ke wuce addu’aki gareta bata da hijabi”.
Hannunta tasa tana ƙara tallaɓe kan Babyn murya na rawa tace.
“Yah Allah ka bawa wannan baiwa taka lfy ka yaye mata wahalar shaƙar numfashi ka sauƙaƙa mata shi al’farmar Annabi da al’ƙur’ani.”
“Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati my Dear”.
Ya faɗa yana share mata hawayen fuskarta da hannunshi na hagu.
Su kuwa saura kab ajiyan zuciya sukayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”..
Sai lokacin ya ɗan kalli Aunty Rahma dake gefen Shatu tana zubda hawaye a hankali yace.
“So sorry my Aunty in Sha Allah babu komai likita yace, da shayar da ita shi akayi zaifi mata illa yanzu kuma shaƙane an mata duk wani taimakon gaggawa daya kamata”.
Cikin gamsuwa ta gyada kai.
Sai kuma ya ɗan taso tsaye sai lokacin yaga yawansu.
A hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin sanyi yace.
“Gimbiya Aminatu in sha Allah daga yau wannan al’adar zata kau a masarautar Joɗa dama duk wasu tarkacen al’adun daba addiniba ki gayawa Lamiɗo”.
Cikin jin daɗi tace.
“Ai ba ita kaɗai ba in dai ka yarda ka mulki masarautar Joɗa duk wata al’ada na masarautun gargajiya kana da damar datsesu ka wanzar da Sunnah”.
Wani irin dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe.
Tabbas masarautar Joɗa tana buƙatar sabon Sarki sabon tsari sabon zubi bisa koyarwar musulunci da sunnar manzon Allah a kauda bidi’a a kawo sunna.
To amman shi baida ra’ayin mulki.
Cikin sanyi yace.
“Gyaran ba lallai sai ni ɗaya zan yi shi ba ai, kuma ko bani ke mulkiba zan iya bada shawara in an yarda a amsa”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Idan dai har kana son kauda al’adun a wanzar da sunna to dole ka mulki masarautar Joɗa da kanka”.
Kanshi kawai ya jingina jikin kujerar kana a hankali ya sunkuyo yana kallon Shatu dake cewa.
“Baiyi mulki Bama Umaymah ana neman ransa da na ahlinsa”.
Lamiɗo da Galadima dake shigowa ne dan jin lbrin abinda ya faru a bakin Jalal ne.
Suka haɗa baki wurin cewa.
“Ƙi gudu sa gudu, Shatu ke muke zaton zaki bashi ƙarfin guiwa kuma sai ki karaya da wuri haka.”
Da sauri su Umaymah kab suka ja da baya suka basu wurin zama.
Suna zama dai-dai lokacin kuma Shatu ta zare mamanta daga bakin Afreen ɗin cikin tsoron ganin yadda ta ke ɗan yunƙuri tana kwaro amai.
Da sauri Sheykh ya matso tare da cewa.
“Innalillahi”.
Ita kuwa Shatu ɗagota tayi da sauri ganin yadda taketa yunƙirin kakarin amai ba ƙaƙƙautawa.
Da sauri Gimbiya Aminatu ta matso tana cewa.
“Subahanallahi”
Shi kuwa Sheykh wayarshi dake cikin al’jihun rigarsa ya zaro da sauri ya kira Dr Lukman Ibrahim yana ɗagawa yace.
“Dr Baby fa sai amai takeyi ba tsayawa”.
Da sauri Dr Lukman Ibrahim yace.
“Alhamdulillah tasha Mamanta ko?”.