
Sheykh kuwa dake tsaye ganin fuskar matar da Shatu’n nasa ke kira da sunan Ummey ne yasa shi, jin wani irin abu ya daki zuciyarsa da ƙarfi, wanda hakan yasanya shi jin ƙafafunsa sunyi masa nauyi, lokaci ɗaya kuma wani irin rauni ya cika zuciyarsa, wanda har hakan yasa yaji wasu irin ƙwalla masu ƙuna suka bayyana acikin idanunsa.
Ahankali ya ɗan soma taka ƙafafunsa tare da ƙarasawa wajen da Shatu da kuma Ummey’n suke.
Durƙusa guiwowinsa yayi aƙasa a dai-dai lokacin daya iso wajen da suke, cikin wani irin yanayin dake fusgansa, ya shiga ambaton sunan Allah, a dai-dai lokacin daya sanya duka hannayensa biyu ya rungumo Shatu da kuma Ummey’n jikinsa.
Cikin wata irin sassanyar muryarsa wanda amo da kuma sautinta baya bayyana ya shiga faɗin.
“Subahanallah!. Alhamdulillah!! Hasbunallahu wani’imal wakil, innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, la haula wala k’uwwata illa billahil aliyil azim!!”
Sune tasbihan da yaketa mai-mai-tawa
Shatu dake kuka kuwa jin ya sakasu ajikinsa ne, yasa ta ɗago jajayen idanunta dake tsiyayar da hawaye, cikin matsanancin damuwa da kuma ruɗewa haɗi da tashin hankalin da ta samu kanta aciki tace.
“Hamma Jabeer Ummeyna bata numfashi.
Dan Allah kace ta-tashi, kace ta buɗe idanunta, banason wani abu ya samu Ummey na, ka taimakamin, wayyo Dedde na Umaymah kuzo Ummeyna …”
Kasa ƙarasa maganar nata tayi, saboda sosai kuka yaci ƙarfinta, sai-dai kuma amma duk da haka bata daina jijjiga Ummeyn nata ba.
Su Yah Jafar Jalal Ummi Mamma Aunty Juwairiyya Aunty Rahma Khadiya Aunty Amina Ishma, Hafsi Yah Al’ameen kuwa gaba ɗayansu zobe sukayi musu, cike da tarin al’ajabi al’hini kaɗuwa da tarin farin ciki.
Junainah kuwa da ta ƙara ruɗewa saboda ganin kukan da Shatu keyi, ƙarasowa jikin Shatu’n tayi ta raɓa jikinta, cikin muryar kuka take cewa.
“Adda Shatu Ummeynmu.
Adda Shatu Ummyen kice ta tashu mukaita asibiti kada wani abu ya sameta!”.
Sauran jama’ar kuwa.
Kowannensu fuskarsa ɗauke da hawaye suka ƙaraso garisu sosai kusa dasu Shatu, Sheykh, da Ummey’n suke.
Sautin kukan Aunty Rahma ne mai nuna tsantsar farin ciki da na Umaymah da Mamma ne suka fito fili, a dai-dai lokacin da sukayiwa Ummey’n zobe, Kowannensu kuka yake, sai-dai kallo daya zakayiwa kukan nasu ka fahimci cewar ba kukan baƙin ciki bane kukane na tsantsar farin cikin da yiwa Allah godiya, domin kuwa acikin muryar kukan nasu suke ambaton sunan Allah, suna me faɗin.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah ya Allah!! Alhamdulillahil lazi bi ni’imati hi ala tatimussalihat!!!”
Umaymah kuwa da matsanancin farin cikin mara misaltuwa da take jin kanta aciki ya kasa ɓuya, durƙushewa tayi bisa guiwowinta tare da kifa goshinta aƙasa tayi Soujjadar nuna, matsanancin godia ga Allah daya dawo mata da ƴar uwarta.
Ummey kuwa wani irin Numfarfashi taja sai gata a sume.
Dai-dai lokacin kuma Jamil da jiyo hayaniyarsu ya sashi tahowa a guje, ganinsu cike a falon kowa fuska cike da hawaye kuma sai kalmar Alhamdulillah suke maimaitawa.
Duk sun kasa bin ta kan kalaman Shatu.
Ganin Jamil ne yasata mgn cikin rauni tace.
“Jamil dan Allah taimaka min Ummey na ta suma”.
Jin hakane yasa ba tare da ya iso inda sukeba ya nufi kitchen da sauri mai kama da gudu ruwa ya ɗebo kana ya dawo.
Yana isowa gab dasu, ya zaro idonsa baki ɗaya murya can sama yace.
“Mammeyyyyy”.
Sai ga ruwan ya kwaɓe a hannunshi shima ya faɗi bisa jikin Yah Jafar a sume.
Gaba ɗaya sun gaza cewa komai sai ambaton Allah.
Da gudu Affan da tun jiya daya dawo dasu Giɗi bai gana da Hamman nasu ba sai yanzu ya nufo Part ɗin.
Jin ƙaran muryar Jamil ne ya sashi shigowa falon da sauri yana cewa.
“Me haka Jamil lfyarka kuwa?”.
Turus yayi a bakin ƙofar ganin duk suna cike a falon sun taru wuri ɗaya kowa da irin addu’ar da yakeyi.
Cikin tsaro da fargabar kardai wani abune ya samesu ya nufosu.
Cikin kaɗuwa yace.
“Mamey”. Ya kira sunanta da ƙarfi lokacin da idanunshi suka sauƙa bisa fuskar Ummey.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli Sheykh dake mgn cikin rawan murya da rauni yake cewa.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Yah Allah na gode maka bisa wannan rahama da kaimin ko yau ka ɗauki raina burina ya cika, yau gani ga Mameyna a cikin masarautar Joɗa a suffar mutun bani Adam ba tsuntsuwar Boleru ba”.
Wani irin kuka ne mai rauni ya kwabce mishi.
Yah Jafar ma kuka yakeyi tare da cewa.
“Alhamdulillah al’ƙadarin Magauta ya karye”.
Ummi kuwa da rarrafe ta rusuna gaban Ummey tare dayin ƙasa da kanta cikin rauni tace.
“Barka da dawowa Adalar Uwar gijiyata”.
Umaymah kuwa da sauri ta jawo wayar da ta gani kusa da ita.
Saida ta danna sai taga ashema wayar Hibba ce da ta bawa Junainah nayi Game.
Jadda ta dannawa kira.
Yana ɗagawa tace.
“Assalamu alaikum Alhamdulillah Allahu Akbar Jadda! Jadda!! Jadda!!!”.
Cike da kaɗuwa Jadda dake kishinƙiɗe ya miƙe zaune tare da kallon Sitti dake yanka mishi lemu wanda tana iya jiyo abinda Umaymah ke faɗa sabida yadda take mgn da ƙarfi.
Wani irin dogon numfashi suka sauƙe a tare jin Umaymah na cewa.
“Alhamdulillah Jadda Aunty Mamey ta dawo Jadda zatonmu da tsammanin mu ya zama gsky Aunty Mameyna ta dawo gata gabanbu Jadda kace Alhamdulillah”.
A tare Jadda da Sitti suka fara maimaita kalmar hamdala.
Affan kuwa cikin wani irin sauri ya juya a guje tamkar ƙaramin yaro ya nufi Part ɗin Abbansu.
Yana shiga da gudu yana mai cewa.
“Abba Abbanmu Abbana Mamey Mamey”.
Da sauri Gimbiya Samira amaryar Abban ta fito tare da cewa.
“Affan lfy kuwa Abbanku yana fada”.
Ai bai kuma bin ta kanta ba ya fito.
Kiciɓis yayi da Hajia Mama tana cewa.
“Kai lfy kuwa kake gudu kamar yaro?”.
Ba tare da ya tsaya ba yace.
“Abba nake nema ina yaje Mamye.”
Daga nan ya nufi fada.
Ita kuwa Hajia Mama cikin wani irin masifeffen tsinkewar zuciya da fargaban jin sunan da bata ko son jin an kira ta juya ta nufi ɗakinta.
A can fada kuwa bayan sarkin ƙofa yayiwa su Bappa iso cikin ƙaton falon.
Abboi na gaba Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro suna biye dashi a baya kana sai masu tsaronshi da suka tsaya can bakin ƙofar shiga sabida dakatar dasu da yayi.
Suna shigowa Lamiɗo dake fuskantar Kofar shiga fuska cike da annuri da haiba yace.
“A a a Masha Allah lalle marhabin da Alhaji Abbo lale da zuwa masarautar Joɗa Fulle bandu fullo”.
Da sauri Wambai, Dirankadi, Ɗan isa, Ɗan buram, Sarkin fada, Ɗan kade, Galadima Ɗan maliki Chiroma Durbi Ma’aji. Duk suka miƙe tsaye cikin tsananin sakin fuska da alamun sanayya na mutuntaka suka kalli Abboi tare da haɗa baki wurin cewa.
“Marhababika da zuwa masarautar Joɗa”.
Sai kuma ɗan zagi ya fara baza rigarsa tare da cewa.
“Sarki ya gaisheka. Sarki yace ayi maka sannu da zuwa fullo Nbandu fullo manyan fada na farin ciki da zuwa ka”.
Wani irin murmushi Abboi yakeyi mai cike da kamala ya nufi gaban Lamiɗo.
Har kusa dashi ya isa kana ya rusuna, yayinda Bappa da sauran ke biye dashi a baya.
A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da ture hularshi yayi baya da ita.
Cikin alamun shaƙuwa Lamiɗo yasa hannunsa tsakiyar kansa tare da cewa.
“Allah yayi muku al’barka”.
Murmushi Abboi yayi tare da cewa.
“Amin ya Allah Baba”.
Sabida Lamiɗo yasan Abboi a matsayin ɗansa yake zuwa gareshi yana jin daɗin abokin mahaifin nashi ya sanya mishi albarka”.
A hankali ya koma ya zauna ya tanƙwashe sawunshi tare da cewa.
“Barka da hatsi”.
“Barka dai”.
Lamiɗo yace.
Abba dake gefenshi ne ya kalli Abboi tare da bashi hannu suka gaisa.