Cikin rawan murya Shatu ta kamo hannun Ummey ɗaya Junainah kuwa ta kwantar da kanta bisa cinyar Ummeynta a tare suka haɗa baki wurin cewa.
“Ummey kin mance mune?”.
Da sauri Shatu ta saki wani irin kuka tare da faɗawa jikin Ummey jin tace.
“Ban mance kuba Boɗɗo na Autata”.
Murmushi sukayi baki ɗayansu falon ita kuwa Shatu da Junainah kukan farin ciki sukeyi.
A hankali Bappa yasa tafin hannunshi ya share hawayensa dake gangarowa hakama Abboi sai suke tuno kamar yau suka samu ɓoleru’n nan.
A cikin masarautar Joɗa kuwa gaba ɗaya labarin dawowar Mamey ya riski kunnuwan mutanen cikinta da kewaye.
Cikin wani irin mamaki Gimbiya Saudatu ta miƙe tsaye tare da kallon Babba Basiru daya kawo mata lbrin cike da kaɗuwa tace.
“Kai Basiru muje mu gani”.
Ai kuwa da sauri suka juyo suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Yayinda Babban ɗan ta Yah Hashim da Laminu mai binshi suka mara mata baya.
Gimbiya Samira ma amaryar Abban da Mom mai bin Mamey da sauri suka nufi Part ɗin Sheykhhhh ɗin.
Gimbiya Aminatu da Matar Galadima ma jiki na rawa suka nufi can.
Hajia Mama kuwa wani irin ihu tayi tare da rugawa a guje ta nufi Part ɗin Sheykhhhh a gigice.
Baba Kamal da ɗansa Sulaiman da sauri suka nufi can.
Dr Aliyu ma da matarsa da ƴarsa Rahima da sauri suka nufi can.
A cikin falon kuwa da sauri Shatu ta amshi gorar zam-zam ɗin da Bappa ke miƙa mata, ta sawa Ummey ita a baki.
Sosai tasha kana ta janye goran.
Da sauri ta miƙowa Aunty Amina hannu alamun ta bata Afreen miƙo mata ita tayi.
Ita kuwa amsa tayi kana ta miƙa wa Ummey ita tare da cewa.
“Ummey sa mata al’barka tunda kece kaka mahaifiyar uba da mai renon Uwa sai ki bawa Dedde na ita tasa mata al’barka itama”.
Murmushi Ummey tayi tare da amsarta sai kuma ta kalli Sheykh tare da cewa.
“Jabeer na ya girma”.
Murmushi dake baiyana tsantsar jin daɗi sukayi.
Nan suka ɗanyi shiru jin Lamiɗo yayi gyaran murya tare da cewa.
“To Alhamdulillah wannan shi ake cewa ƙudurar Ubangiji babu bawan daya isa kaudashi.
Sai kuma ya kalli Bappa da tare da cewa.
“Dan Allah malam Liman bani lbrin yadda akayi Aisha ta kasance tare daku da kuma sanadin haɗuwarku da samun lfyarta?”.
Cikin sanyi Bappa yace.
“Bazamu bari ta hutaba tukun?”.
Da sauri Ummey ta jujjuya kai tare da cewa.
“A a Bappa gaya musu kawai domin nasan gaba ɗayansu wannan tambayarce a ransu.
Duk da zanso inji ya lbrin Jaddana da Sittina naga kowa sune ban ganiba”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Aunty Mamey Jaddanmu da Sittinmu suna lfy suna gab da tasowa zuwa nan suma”.
Cikin tarin farin ciki tace.
“Alhamdulillah to Bappa gaya musu ko ince gaya mana meya faru?.”
Shiru Bappa yayi sai kuma ya kalli Umaymah dake cewa.
“Dan Allah gaya mana a wacce suppar ka samu yar uwata a wani yankin”.
Cikin nitsuwa Bappa ya gyara zamanshi kana ya ɗan yi gyaran murya a hankali yace.
“Ranar wata jumma’a data gabata tsawon shekaru goma sha uku a can ƙasar Cameroon a yanki dake gefen babban birnin Yahunde cikin Rugar Arɗo Babayo…!
Da sauri suka juyo suna kallon bakin ƙofar shigowa sabida jiyo muryar Hajia Mama daga nesa tana cewa.
“Zancen banza zancen wofi kenan ta yayama za’ayi ta dawo mutun har ta dawo nan cikin masarautar Joɗa”.
Ta ƙarashe mgnar da ƙarfi tare da banko ƙofar ta shigo a fijajan.
Yayinda duk sauran tawagar masarautar Joɗa ke biye da ita a baya.
Tana shigowa tayi wani irin zabura tare da zaro idanunta gaba ɗaya sai kuma tayi kan Ummey da gudu.
Da sauri Shatu ta miƙe ta tsaya gaban Ummey tare da cewa.
“Da dakuka cutar da ita kuka fitar da ita haiyacinta da halittar ta a zatonku a haka zata tabbatane?”.
Da sauri Sheykh yasa hannunshi ya kamo na Shatu yajata ya zaunar da ita.
Ita kuwa Ummey idanu ta zubawa Hajia Mama tamkar zata manna matasu a jikinta sai jujjuya kai takeyi.
Ita kuwa Hajia Mama ganin idon Ummey cikin natane yasa duk wani sihirinta ya dawowa jikinta kamar yadda Ba’ana yace musu zai bawa Ummey mgnin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya duk randa tayi Ido biyu da wacce tai mata sihirin zai dawo jikinta.
Bayan kwanaki biyar zata koma tsuntsuwar Boleru kamar yadda sukayi mata.
A lokacin Bappa yaƙi shi dai yace ta samu lfy ta fara mgn amman da gaiya Ba’ana ya bata wannan mgnin sabida zalumcin da akayi mata ya tsananta.
Cikin wani irin gigita Hajia Mama ta kai hannunta ta taɓa fuskar Ummey tare da cewa.
“Kika dawo mutum kenan bokana yamin ƙarya yace min har abadan yadda matacce bazai dawo duniyaba haka bazaki dawo mutunba bazaki taɓa dawowa Masarautar Joɗa ba.”
Sai kuma ta kai hannu ta bugi gefen bayanta ta sosa tare da karkata baki kana tasa hannun ta ɗaya ta cire ɗan kwalin kanta ta cillashi gefe tare da cewa.
“Shigayar balarabiya mai nacin tsiya ki aure min miji ki haife mishi zaratan maza harda tagwaye kana ace cikin ƴaƴan ki za’a samu mai gadar mulkin Masarautar Joɗa ai wlh bazata saɓuba”.
Sai kuma ta fara yatsuma gashin kanta tare da kurma ihu.
Cikin wani irin yanayi mai cike da rauni kunya tashin hankali kiɗima gigita.
Affan ya kife kansa da jikin sawun Sheykh ya saki wani irin kunyataccen kuka mai cin rai tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun Hamma Jabeer wanne yanayi ne wannan Hajia Mama take ciki wannan wanne ranane mai cike da kunya Allah ya zai nuna min”.
Da sauri suka juyo suna kallon Baba Kamal da yake fifita da hularshi tare da kecewa da dariya yace.
“Hahaha ta haukace ta haukace na haukace, zasu haukace duk zamu haukace.
Shegiya muguwar babarbariya ba ke kikayi mata sihiri ta zama tsuntsuwar Boleru ba kika haukata Jafar ba kika sawa Jamil bin mata Jalal bin mutanen banza bw”.
Da sauri ta juyo cikin wani irin rawa-rawan haka na sakayyar mugun aikinta tace.
“Tafi daga nan mugun bafulatanin kai kuma ai kai ne kayi mishi ashirin kashe mishi lfyarsa dan kada yayi aure bare ya haihu kana zaton bansan duk abinda kakeyi bane”.
Sai kuma duk suka kece da dariyar hauka tare da faɗi ƙasa sunayi harda tafa hannunsu.
Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani’imanwakil waɗannan sune kalaman da gaba ɗaya mutanen falon sukeyi sabida fahimtar sakayyace ta riskesu tun a duniya.
Baba Basiru ne ya matso kusa da Baba Kamal tare da cewa.
“Mugu bashi da kama Kamal kaida Hajia Mama tabbas kun cika mugaye masu cikekkiyar manufa wanda har kuka iya ɓoye muguntarku.”
Su dai su Sheykh Umaymah Shatu Lamiɗo Abba Bappa gaba ɗaya zuba sarautar Allah ido sukayi.
Affan kuwa kukane mai cin rai yakeyi cike da kunyar abinda mahaifiyarshi ta aikata.
Shi kuwa Baba Basiru a hankali ya matso gaban Gimbiya Saudatu daketa zazzare idanunta cike da mamakin jin tsantsar muguntar mutanen da kullum take faɗa dasu a zatonta masoyan Sheykh ne.
A hankali ya kalleta kana yace.
“Jabeer yau dai ka yarda ka gamsu da abinda nake ce maka ko”.
Cikin yanayi gamsuwa Jabeer ya kalli Baba Basiru wanda mutane ke zato maƙiyinshine har Gimbiya Saudatu ta haɗe dashi bata san cewa ƙididdigarta yakeyi ba.
Shi kuwa Baba Basiru a nitse yace.
“Dama na gaya maka Gimbiya Saudatu sha giri girbauce wautace kawai ke damunta da ƴar hasada, sannan kuma da zugan wannan maƙiyin nata”.
Yayi mgnar yana nuna Baba Nasiru wanda ita a zatonta masoyi ta ne.
Cikin gyara tsayuwarshi ya kalleta kana ya kalli shi Baba Nasiru daketa karkarwa cikin zubda hawaye yace.
“Ke Gimbiya Saudatu kullum Nasiru na ingizaki da zugaki da cewa Gimbiya Aisha da ɗan ta Jafar ne suka kashe miki mijinki babban yayanmu Yah Aumalu mahaifinsu Hashim da Laminu wan dan Jafar ya gaji sarautar Galadima ko?”.
Da sauri ta gyaɗa kanta.
Yayinda suma duk saura suka zuba mishi ido.
Cikin zubda hawaye yace.
“Toh kinga Yah Nasiru ɗan uwanmu uwa ɗaya uba ɗaya shine ya kashe miki mijinki uban ƴaƴanki sannan yanke ingizaki kan su Sheykh da mahaifiyarsu yasa miki tsanarsu kiketa haushi a kansu kamar karya.
Ita wannan muguwar kuwa Hajia Mama da Kamal da Hashim ɗanki da kuke gani kamar yana son Jabeer alhalin ya tsaneshi shi kuwa wai dan Lamiɗo yafi janshi a jikinshi.
Duk sai suka fake a bayanki sunayiwa Sheykh da ahlinsa mugunta yayinda kowani sai yayi zargin kece kinga kin zama bushiya kamar yadda Shatu ta faɗa a zahiri in anganki jiki duk ƙaya amman cikin bushiya namansa ma maganine su kuma suka kasance belbela siffarsa fara cikinta baƙiƙƙirin”.
Cikin rauni Gimbiya Saudatu tace.
“Innalillahi wallahi ni dai Allah ya sani ko garin marke ban taɓa nemowa da niyar cutar dasuba..
Yanzu ashe Hashim kaima muguwar zuciya gareka ban saniba har zaka iya cutar da ɗan uwanka.”
Ina Affan kam tuni yake kuka tamkar zai shiɗe dan baƙin ciki da takaicin abinda uwarsa ta aikata.