GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Shiru falon sukayi baki ɗayansu sai sutin kukan Giɗi, Shatu, Junainah, Ummey, Seyo, Gaini. Raunin da kukansu ya sauƙar a zuciyar Bappa ne yasa shima sakin kuka dan yau sai sukaji gaba ɗaya rasuwar Yah Lado da Inna ta dawo musu sabuwa.

Sosai Shatu keyin kuka tana durƙushe ta tanƙwashe sawunta, hakama Ummey.

Gaba ɗaya kab falon saida idon kawa ya ciko da ƙwalla.

Cikin Rauni Sheykh ya matso inda Shatu ke durƙushe gaban yayun nata, cikin sanyi ya kalli Bappa Ummey murya a raunace yace.
“Tabbas bansan irin ƙunar da kakaji a cikin ranka ba Bappa amman nasan kwatankwacin kamannin ƙunan rashin ɗa, a suman da Afreen tayi naji ciwo da ƙuna a zuciyata tamkar ban taɓa farin cikiba, nasan zafin rashin uwa, amman ban san zafin rashin mataba dan kamin gatan bani Mar’atussaliha ta zame min GARKUWA tana sani farin ciki a duk lokacin da nake cikin baƙin ciki.”
Shiru yayi sai kuma ga hawaye shar-shar a idanunsa cikin rauni yace.
“Na samu komai da nake nema a rayuwata daga gareka ka bani mata ta gari, Allah ya azurtamu da samun ƙaruwar arzin haihuwa sanadinka Ummey na ta dawo.
Inama! inama! ace Inna da Lado ɓata sukayi ba rasuwa ba, da tabbas zanyi iyakar iyawata in dawo maka dasu da izinin ubangiji.
To amman wannan hurumin ubangijin sammai da ƙassaine.
Kayi haƙuri Bappa Allah ne ya baka Inna matsayin mata ya ɗauketa ya sauyama da ƴar uwarta kuma Allah shi ya baka Lado ya ɗauke shi kuma ya killace maka Seyo Gaini Giɗi, wanda wata ƙil da suna Rugar ba’a sacesu ba da an kashesu.
Gashi yanzu Allah ya dawo maka dasu.
Bappa kace Alhamdulillah ka godewa Allah da ni’imar da yayi maka sai ya ƙara maka wata a kai.
Kayi haƙuri ka bar kuka kaga kukanka na ƙara ingiza nasu”.
Ya ƙare mgnar yana sa hannunshi cikin tafin hannun Shatu yana murza a hankali.
Cikin gamsuwa da jin sanyi a ransa Bappa yace.
“Alhamdulillah”.
Da sauri Su Giɗi suma sukace.
“Alhamdulillah”. Hakama su Lamiɗo kab falon sai suka fara mai-mai-ta hamdala.
Ai kuwa cikin ikon Allah duk ƙuna da ƙuncin da zuƙatansu keyi a take Allah ya sauƙaƙa musu shi.
Cikin gyaran murya Lamiɗo yace.
“Alhamdulillah komai yayi forko zaiyi ƙarshe duk abinda yayi tsananin tabbas zaiyi sauƙi Allah mun gode maka daka ara mana rai da lfy”.
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Sheykh dake kallon agogon hannunshi sabida jin anyi kiran sallan azahar.

Cikin tarin jin daɗi Abbansu Sheykh ya matso kusa da Bappa da Abboi murya cike da tarin jin daɗi yace.
“Bappa Abboi dama duk al’ummar Rugar Bani da Rugar Arɗo Babayo ngd matuƙa Ubangiji yayi muka sakayya da gidan al’ljanna mafi ƙololuwa girma.
Shatu Allah ya dafa miki ya tsareki dake da ahlinka”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Shi kuwa Bappa Sheykh ya kalla tare da cewa.
“Muhammad Ngd matuƙa Allah ya saka da al’khairi da kulawarka Alhamdulillah ga mahaifiyarku da ƙanwarku Allah ya bamu aron rai da lfy da ikon dawo muku dasu lfy”.
Cikin jin daɗi Ummey tace.
“Bappa dani dasu ya kamata muyi godiya ba kuba kun gama min komai a duniya musamman Alhaji Abboi da matarsa Dedde sun min karar bani yar su duk da tarin son da sukeyi mata, suka amince muka dawo da ita nan, kana suka bawa Jabeer na aurenta.”
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu tare da cewa.
“Kin min komai kin juya min Jabeer daga bauɗeɗɗen mutun zuwa dai-daice gashi yanzu har fara’a yakeyi ga Jalal na shima ya zama mai fara’a Jamil kuma ya nitsu.
Sai dai yanayin Affan nane ke min ciwo a rai, Affan ka dena kuka kajiko Shalelen Mamey”.
Cikin rauni Affan ya matsota ɗaura kanshi bisa cinyarta yayi tare da sakin kuka.
Gaba ɗaya kowa yasan takaicin abinda mahaifiyarsa tayine yake sashi kukan.
A hankali Lamiɗo yace.
“Kayi shiru Affan ita rayuwa kowa abinda ya shuka zai girba”.
Daga nan dai kuma akayi gaishe-gaishe.
Kana mazan duk suka tafi masallaci.
Matan masarautar Joɗa kuwa irinsu Gimbiya Saudatu da Gimbiya Aminatu dasu Mom da Samira duk ko wacce ta koma part ɗin ta cike da al’hinin sharrin ɗan Adam.

Matan kuma duk kowa tai al’wala sukayi salla, kana suka sake fitowa falo suka zauna suna cin abinci.

Affan kuwa Part ɗin shi ya koma ganin tashin hankali da yake cikine yasa Mami meda hankalinta gareshi.
Shi kuwa Rumaisa yayarshi ya kira tana ɗagawa yace.
“Uhummm tunda kullum kece kike zuga Hajia Mama kuna cutar waɗanda basu damu da kuba sai ki shirya kizo kiga halin da Mama ke ciki na girbar aiyukanta data shuka”.
Cikin tashin hankali Rumaisa tace.
“Affan m..”
Bai bari ta ida zancenta ba ya katse kiran.

Su Sheykh kuwa dasu Haroon falon Sheykh Suka wuce.

Bayan anyi sallan la’asar ne,
Dedde ta kalli Ummey cikin kula tace.
“Toh Ummeyn Shatu mu zamu koma Rugar Bani, sai jibi zamu koma Cameroon da izinin ubangiji Allah ya kiyaye gaba ya tsaremu”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Yanzu-yanzu zaku tafine?”.
Cikin nitsuwa Dedde tace.
“Eh ai su tuni ma sun shiga mota nida su Khadijah suke jira”.
Da sauri Umaymah tace.
“Ayyah ni kuwa ina son ku gaisa da Sittinmu da Jadda kafin ku tafi”.
Da sauri Mamma tace.
“Ai sun iso suna Part ɗin Lamiɗo.
Amman yanzu zasu iso”.
Da sauri Shatu tace.
“Toh Dedde am ki ɗan jira ku gaisa mana”.

Suna cikin mgnar Sitti da Jadda suka shigo.
Allah sarki iyaye sai gashi Ummey a tsakiyarsu suna kuka gaba ɗayansu an rasa mai rarrashin wani.
A hankali Sheykh da Haroon suka shigo falon cikin tsiya Sheykh yace.
“Toh Alhamdulillah Jadda ni dai burina ya cika ko yau in kana son tafi ka gaida na gaba tunda kaga Mamey na ta dawo ta sameku cikar farin cikinta kusa mata al’barka”.
Dariya sukayi baki ɗayansu kana su Dedde suka matso aka gaggaisa.
Sannan Jadda ya fita ya koma wurin su Lamiɗo.

Cikin sanyi Shatu ta kalli Deddenta Aunty Amina Hafsi Khadijah waɗanda duk suke cikin shirin tafiya.
A hankali tace.
“Allah sarki da mu ƙara kwana mana, yanzu kuma in kun tafi shikenan sai yaushe ni na zama a nan ina gefe duk ƴan uwa suna Cameroon”.
Da sauri Ummi tace.
“Kema kina tare da yan uwanki ga Ummeynki ta dawo kusa dake ga kuma Junainah gani ga Hibba”.
Da sauri suka kalli Jamil da ke cewa.
“Kuma zan auro mana Khadijah ma ta dawo nan zaku bani ita ai ko Dedde”.
Ya ƙare mgnar cikin yanayinsa na wasa da dariya da kowa.
Murmushi Dedde tayi tare da cewa.
“Ai an baka ma Jamilu”.
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Junainah kuwa a hankali ta matso kusa da Ya Giɗi tare da cewa.
“Ummey ni dai zan tafi tare dasu Yah Giɗi ban gaji da ganinsu ba”.
Cikin jin kewar juna Ummey tace.
“Kije Junainah nima in Sitti na da Jadda sun tafi zamuzo tasu Mamma”.
Da sauri tace to.
Kana ta kalli Shatu da tai shiru tana kallonta tare da cewa.
“Kada ki damu Addana nima zanke zuwa masarautar Joɗa”.
Da sauri Jalal yace.
“Zaki dawo dai Junnu gamu ga Abbanmu ga Adda Shatunki ga Ummey”.
Da sauri ta kalli Sheykh tare da cewa.
“Toh Yan Junaidun fa”.
Dariya mai sauti Sheykh ya ɗan yi tare da cewa.
“Shima zai dawo nan”.
Nan dai suka fito gaba dayansu dan yiwa su Dedde rakiya.
Jadda kuwa harda kuka yayi yana yiwa su Abboi da Bappa godiya.

A hankali Salmanu wanda yazo wurin ɗan Hafsi ne ya ɗan matso kusa da Ummey ƙasa yayi da murya tare da cewa.
“Ummey ki roƙa min su Abboi a bar mana Hafsi mana”.
Dariya Ummey tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kuce duk ma zamu kwasosu mu dawo nan dasu”.
Da sauri Salmanu ya shiga mota.
Shi kuwa Yah Al’ameen gefen Shatu ya ɗan kalla tare da yafitota.
Bayan Sheykh suna ɗan ratsa a hankali yace.
“Wannan ƙawar taki Rafi’a fa, da batunta yasa su Abboi zuwa gobe zasuje su zanta da manyanta sai jibi zamu koma”.
Cike da mamaki tace.
“Lahh Yah Al’ameen ashe mgnar taku har ta kankama”.
Da sauri yace.
“Ke da Allah ni kada kimin shele”.
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
“Toh sai na gaya ma kowa yaji”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button