GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jamil da Jalal da Yah Jafar Imran dake shigowa ne suka haɗa baki wurin cewa.
“A to a haɗa harda mu dan muma kansu mana kwarjini yana mana yawa Hamma Jabeer”.
Murmushi yayi kana suka shigo suka zauna suna hira cikin jin daɗi.
So a nanne yaji kaso 30 cikin 100 na azabebben kishin daya cakeshi ɗazu ya ragu.

Ita kuwa Shatu suna shiga kai tsaye bedroom nashi ta wuce.
Ta gyara komai ta killace komai ta ɗan ƙara gudun AC kana tasa turaren ɗaki Tuch me mai sassayan ƙamshi.

Kana ta dawo ɗakinta, kamar kullum bayan tayi wonka ta fitone.

Ummi ta shigo riƙe da kasko da rushi kaɗan a ciki.
Gaban gadon ta ajiye kaskon tare da jawo kujerar ƴar tsuguno mai rami ta turaren gyara ta ɗaura kujerar kana ta jawo wani kolba dake kan mirror ta buɗe tasa hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi.
“Zauna”. Tace tana fita.
Da sauri Shatu ta zauna bisa kujerar tana mai jin yadda ƙamshin yake game jikinta,
Tabbas wannan turaren tana jin daɗin shi ita da kanta da kanta.
Dan ko fitsari tayi sai taji yana ƙamashi sai dai tana ji yana tsuketa.
Bayan kamar 30 minute Ummi ta kuma shigowa riƙe da cup da madarar gongoni a ciki mai sanyi da haɗin Garin maɗi.
Motsashi tayi da cokali tare da cewa.
“Yauwa amshi ki shanye”.
Ba musu ta amsa sabida tana masifar jin daɗin haɗin.
Bayan ta shane ta ajiye cup ɗin kana ta matso gaban dreesing mirror’n humra mai sanyin ƙamshi ta murza a jikinta tare da zura wata tattausar rigar bacci royal blue mai ɗigo-ɗigon fari.
Rigar iya karya guiwa.
Turaren laylaytul sahrah ta fesa.
Kana ta zura jibajinta har ƙasa.

Su Sheykh kuwa bayan sun gama hirane.
Yasa hannunshi ya amshi Afreen da Mamey ke miƙa mishi tare da cewa.
“Kaita tasha mama”.
To yace.
Tare da amsarta ruggume ta yayi a jikinshi tare da cewa.
“Sai da safe”.

“Allah ya bamu al’khairi”.

Amin yace yana mai fita, sai kuma ya tsaya jin Abbanshi na cewa.
“Kaje wurin Lamiɗo akwai takardun aiken masarautu da yakeso ya baka”.
Cikin bin umarni yace.
“Toh”.

Yana fita Part ɗin Lamiɗo ya nufa.

Gefenshi ya zauna ruggume da ƴarsa cikin kula Gimbiya Aminatu tace.
“Kai ɗa da daɗi ko Sheykh”.
Murmushi yayi tare da kallon Afreen dake jujjuya ido tana lumshesu alamun bacci zatayi yace.
“Uhumm sosai ma kuwa ɗa kam da daɗi Gimbiya Aminatu”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa kissing goshinta yayi tare da sa mata al’barka.
Kana ya kalli Lamiɗo a fakaice yace.
“Abba yace akwai takardun da zaka bani”.
Eh yace tare da miƙo mishi wasu takardu liƙe cikin wani, kekkyawan mazauni tare da tambarin hatimin masarautar Joɗa a jiki.
Hannu yasa ya amsa tare da cewa.
“Toh na menene?”.

Cikin tsareshi da ido Lamiɗo yace.
“Aiken Masarautar Joɗa ce zuwa ga sauran masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria, zaka kai musu ɗaya baya ɗaya”.
Da sauri yace.
“Yaushe kuma aiken menene?”.
A daƙile Lamiɗo yace.
“Gobe sai kaje ka dawo zan gaya maka na menene.
Waziri, Wambai, Galadima, Chiroma, Durbi, duk sun sa hannun”.
Taɓe baki yayi tare da cewa.
“Sai dai kuma ai kai ba ubana bane da zaka wani tirsasani ka sani abu dole.
Harda wani wai gobe”.
Ya ƙarashe zancen yana miƙewa tsaye riƙe da takardun.

Shi kam Lamiɗo murmushi kawai yayi ya bishi da ido.

Kai tsaye Part ɗin su ya nufa.
Ba kowa a falon haka yasa ya rufe ko ina ya kashe duk kayan wuta.
Kana ya wuce Side ɗinsa ruggume da Afreen.

A hankali yaja sassayan numfashi tare da shaƙar ƙamshin ɗakin.
Wutan ya kunna,
ido ya lumshe ganin komai fes-fes.

A can tsakiyar gado ya kwantar da Afreen tare da gyara mata kwanciyarta dan tuni tayi baccinta.

Addu’o’in yayi ya tofa a tafin hannunsa ya shafa mata.
Bathroom ya wuce.
Wonka yayi mai rai da lfy kana ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo pink guava color da ratsin Royal blue masu ɗan karen taushi.
OudKareem ɗinsa ya fesa kana ya fito.

A hankali ya ɗan zauna bakin gadon ba tare daya kashe wutanba.

Miƙe sawunshi yayi bisa gadon tare da ɗan zamewa ya kwanta rigingine.
Ido ya rumtse a hankali tuno kalaman Ba’ana a kan Shatu.

Ita kuwa Shatu a hankali taja ƙofar ɗakinta ta rufe Sannan ta nufi Side ɗinsa.

A hankali ta tura ƙofar tare da cewa.
“Assalamu alaikum”.
buɗe idonshi yayi tare da zuba mata su.
Murya can ƙasa yadda bata jiba yace.
“Wa alaikassalam”.
A zahiri kuma sai ya haɗe fuska tare da tsuke bakinshi.

Motsowa ta inda yake tayi tare da cewa.
“Yah Sheykh kayi bacci ne?”.
Bai kulata ba kuma bai ɗauke idonshi a kanta ba.
Ƙara matsoshi tayi tare da zare hijabin ta ninkeshi tana cewa.
“Hamma Jabeer yau ba mgna ne”.
Bakinshi ya taɓe mata.
Wanda hakan ya tabbatar mata yana fushi da itane wanda tasan fushin bai rasa nasaba da yadda yake buƙace da ita take kauce mishi.

Ajiye hijabin tayi a gefe. Sannan ta ɗan matso gaban shi.
Yatsun ƙafarshi ta ɗan ja tare da cewa.
“Nooryat”.
Idonshi ya cire a kanta, yana mai ji kamar ya ruggumeta.
Fahimtar dafa gaskene fushin yasa ta ɗan hauro saman gadon.
A hankali ta sunkuyo kanshi tabi tsawon shi.

Hannunta ta cusa cikin rigar tashi, ta fara mishi tafiyar tsutsa ta gefe da gefen cikinsa.

Kana ta haɗa fuskarshi da nata.
A hankali ta kamo lip ɗinshi na ƙasa ta tsotsa tare da fidda sautin.
“Shyyyyuuyyh Yan Sheykh na tuba”.
Miƙa mai tsawo yayi jin yadda takeyin ƙasa da hannunta.
Kana ta haɗe bakinsu wuri guda.
Wani irin lasa tayiwa harshensa wanda yasa yaji.
Sheykh ɗin shi ya amsa amo ya miƙe cike da zalama.
Da sauri yace.
“Barni”.
Cikin raɗa tace.
“Naƙi”.
Kanshi ya ɗan ɗago tare da tsareta da ido.
“Sai kuma ya tashi zaune yana riƙo hannunta jin tana kwance mishi zariyar wondo.
Da sauri yace.
“Wai menene hakan?”.
Cikin tura baki tace.
“Abuna zan nema”.
Bai san lokacin da dariya ta kubce mishi ba ganin yadda tayi mgnar cikin dariyar yace.
“Abun naki kuma babu inda zaki nemo shi sai cikin wondona?”.
Ya ƙare mgnar tare da jawota jikinshi ya ruggumeta gam-gam yana kissing wuyanta.

Cikin jin daɗin ya huce da kuma son fara shigar mishi da ra’ayin sarauta tace.
“Mai martaba Lamiɗo Jabeer.
Allah ya nuna min randa zaka mulki masarautar Joɗa ka rabamu da duk wasu al’adu marasa kan gado”.
Cikin yi mata kallon shauƙi yace.
“Yoh al’adun gida nama ai kin nuna ban isa in hanasuba bare na masarautar Joɗa”.
Cikin cusa hannunta cikin ƙugunshi tace.
“Al’adar gidanka kuma wacce ta isa tafi ƙarfin ka hanata”.
Hannunshi yasa yana kunce igiyoyin dake sarkafe gaban rigarta murya can ƙasa yace.
“Al’adar wai in mace ta haihu sai ta kwana arba’in kafin ta bari mijinta ya kusanceta.
Kullum a wahale nake kwana ke ko a jikinki kina sane dai al’adace ba addiniba amman kikayi tauye min haƙƙina”.
Da sauri tace.
“Toh ai hakanma Al’adar masarautar Joɗa ne ni yamin ka sani ma”.
Ta ƙare mgnar cikin gimtse dariyarta na ƙaryar da tayi na wai Al’adar masarautar Joɗa sai bayan arba’in za’a koma turaka, tayi ƙaryar ne kuma sabida ta samu ta ƙara cusa mishi tsanar al’adun da son kaudasu.
Ai kuwa cikin kwaffa yace.
“Zancen banza, ai wannan aikin jahilci ne ya za’ayi nida matata kuma ace sai wata Al’adar masarautar Joɗa ta bani izini da damar kusantarta”.
Murmushi mai cike da ƙauna tayi tare da cewa.
“Toh ai shine muke fatan ka mulkemu ka kauda ire-iren waɗannan abubuwan”.
Tayi mgn tana kai bakinta gareshi.
Wani irin dogon numfashi yaja tare dasa hannun duka biyu ya tallabe kanta.
Tare da fidda sautin.
“Shiyyyyyy Ahhhh Aishh”.
Sosai ta gigitashi da salon da tasan yana masifar so.
Saida taga ya gama narkewa ta ɗan janye kanta kana ta ruggume shi a hankali ta kai bakinta kusa da kunnenshi murya can ƙasa tace.
“Yah Sheykh ka mulki masarautar Joɗa dan Allah da manzonsa dan son samar da gyara”.
Cikin yanayin da bai san hali da duniyar da yake cikiba yace.
“Tohhhhh Aish”.
Da sauri tace.
“Kayi al’khairi”.
Jikinshi da muryarsa kab na rawa yace.
“Nayi al’ƙawarin”.
Ai kuwa sai ta mirgina ta jikinshi da kyau.
Bayan ta cire rigarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button