Wani ɗan raunataccen ƙara ta saki sabida.
Zafin da taji yayin ziyartarsa wanda dole ta janye ta kwanta tare da cewa.
“Bazan iyaba”.
Jikinshi na rawa yayi mata rumfa.
Da ƙarfi ta ɗan saki ƙara sabida ji tayi kamar yau ta taɓa sanin namiji dan gyaran da Ummi da Mamey da Umaymah sukayi mata ya haɗawa.
Hannunta ta ɗan yarfa cikin raki tace.
“Wash Honey”.
Cikin yanayin shiga duniyar maji daɗi Yah Sheykh ya rinƙa sanya mata al’barka”.
Cikin nitsuwa cikin sararin samaniya murya a narke tace.
“Yah Sheykh zaka mulki masarautar Joɗa ko”.
Da sauri yace.
“Eh eh ehhhhhhhhhhhhhh Aishhhhh”.
Sabida yana gab da jin numfashin sa na shirin ɗaukewa in bai buɗe bakinshi ba…
Bayan komai ya lafane sunyi wonka sun dawo suna konce.
Ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da shafa maransa kana a hankali yace.
“Alhamdulillah naji sakayau”.
Sai kuma ya kai hannunshi bisa cikinta tare da cewa.
“Allah yasa ƙanwa ko ƙanin Afreen ya kasantu”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Ai ni dai tunda ka yarda zaka mulki masarautar Joɗa ko duk shekara zan haihu ba matsala”.
Da sauri yace.
“Toh yaushe kuma mukayi haka dake?”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Yanzu mana”.
Juya mata baya yayi yana gyarawa Afreen kwanciya yace.
“Uhumm to ke waya ce miki al’ƙawarin a irin wannan lokaci yana aiki, ai ko al’ƙalai basa amsar shaida da al’ƙawarin mai fataucin kayan daɗi”.
Da sauri tace.
“Yah Sheykh al’ƙawarin fa kayi”.
Jawota jikinshi yayi tare da cewa.
“Kai sake wannan al’ƙawarin Aish, yoh ai sai ince miki na baki Makka da madina ma a cikin wannan yanayin ke baki san Y.M.D.G. bane”.
Dariyar da take dannewa ne ta kubce mata.
Haka yasa ya lakace hancinta tare da cewa.
“Ja’ira wato dariya ma zakiyi min”.
A haka dai sukayi bacci liƙe da juna.
Washe gari da asuba suna dawowa masallacin.
Abbanshi yake ce mishi.
Wai yayi maza fa ya fito su tafi shi ɗaya ake jira.
Sosai yayi mamakin ashe dama da gaske Lamiɗo yake yau zaiyi tafiyar.
Bisa dole bisa umarnin iyayenshi ya fito suka tafi.
Shatu nata bashi baki.
Ta kaicinsa ɗaya da aka hanashi tafiya da ita.
Alhamdulillah yayi tafiyar kai takardun murabus ɗin da Lamiɗo zaiyi ya bashi mulki ga masarautun gargajiya na Arewacin Nigeria.
Gaba ɗaya sunyi na’am da haka sun sa hannun.
Duk da shi baima san takardun me bane dan bai buɗeba.
Randa ya isa masarautar su Umaymah kuwa daɗi kamar zai kasheta.
Kwanashi goma ya gama zagaye kab masarautun ya dawo dasa hannun da buga hatimin dukkan masarautun.
Koda ya dawo da Lamiɗo ya gani saida yayi ƙwalla sabida zallan farin cikin ganin yadda ya samu haɗin kan kab masarautu har aka ƙara da yabawa sarki maijiran gadon.
Shida Shatun kuwa a ranar suka tabbatarwa juna.
Sunyi bege da kewar juna.
Kasan cewar ranar Al’hamis ya dawo.
Tun a daren Shatu ke ta masa batun.
Zuwa Rugar Bani.
Toh yace dai ba matsala ran asabar zai kaita.
Mamey ma da Ummi dasu Jalal duk sunce zasu je.
Ba’ana kuwa zuwa yanzu gaba ɗaya.
Ya zama wani irin al’ummar Rugar Bani kuwa sun cika da mamakin ganin yadda ya sauya jami’in salla baya wuceshi yayi sanyi ya sauya kamar ba shiba abu kaɗan sai hawaye.
Yauma kamar kullum yaje ya samu Bappa a garkensa bayan ya gama magiyar a bashi Shatunsa Bappa ya babbashi haƙuri.
Sai kawai ya jingina kanshi da jikin itacen nim dake gefenshi.
Murya na rawa yace.
“Zan sake barin Nigeria’n kuma tabbas da Shatu da duk dabbobinmu Rugar Bani zanyi awon gaba dasu muddin baku dawo min da ita cikin lumana ba.”
Ya ƙarashe mgnar cikin alamun wai baraza zai mishi.
Ganin yadda Bappa ya zuba mishi idone yasa yaci gaba da cewa.
“Wlh Bappa mutuwa ce kaɗai zata rabani da Mata in haƙura, bayan mutuwa babu abinda zai rabani da ita na barshi.
Tabbas zan saceta.
Sabida itace cikon farin cikina Mata ce burin duniyata”.
Ya ƙare mgnar hawaye na zuba.
Kai Sheykh ya jinjina tare da cewa.
“Uhumm da kuma ita zanyi maka tarko ka shiga hannun hukuma ba taƙadiri”.
Shi kuwa Bappa da Baroon shiru sukayi suna jin yadda sautin kukansa ke tashi.
Washe gari ranar asabar.
Misalin ƙarfe goma na safe.
Tsaye suke gaba ɗayansu cikin shiga ta al’farma.
Jalal da abokanshi sojoji mutun huɗu su motarsu da ban.
Yah Sheykh kuwa shi yake jan motar da kanshi
Shatu na gefenshi Ummi da Mamey na baya.
Saratu kuwa tana motar Aunty Juwairiyya da Yan Jafar da yaransu.
Jamil da Affan kuwa motarsu ɗaya a haka suka nufi Rugar Bani.
Ƙarfe sha ɗaya dai-dai na safe tayi musu cikin Rugar Bani.
Cikin wani irin masifeffen zabura Ba’ana ya tashi zaune.
By
*GARKUWAR FULANI*
????????
????????????????????????????????
GARKUWA
Page 11
Tare da kallon zoben azurfan dake yatsarsa wacce irinta ya sawa Shatu a yatsarta wanda in suna kusa da juna zasuyi ta yin haske.
Wani irin dariya mai cike da jin daɗi yayi tare da cewa.
“Mata”. Ya faɗi yana mai miƙewa tsaye ya nufi ƙofar gida.
Su Sheykh kuwa a hankali sukayi parking cikin nitsuwa suka fara fitowa.
Ummi na Ruggume da Afreen yar wata biyu tayi kuɓul-kuɓul da ita gwanin burgewa da sha’awa gashin kanta yana kwance lib-lib kamar ɗiyar larabawa.
Wasu irin tattausan kayane masu masifar kyau da taushi da tsada aka kimtsata a ciki rigar mai ɗan karen kyau.
Yellow and Pink color masu taushi sai ɗan banɗanan nashi mai kyau da akasa mata a kanta yayi cib dashi.
Sai Safar kafarta yellow sai takalmanta pink.
Kana towel din da aka ninketa ciki shima pink color.
Sai wani irin fitinenne ƙamshi mai daɗin shaƙa da takeyi.
A hankali suka fito baki ɗayansu.
Ajiyan zuciya Mamey da Shatu suka sauƙe tare da shaƙan daddaɗan iskan Rugar tasu.
Kowa ya bar gida tabbas gida ya barshi.
Da sauri Ummi da Aunty Juwairiyya da Sara suka matsosu.
Mamey ce a gaba duk suna biye da ita a baya.
Sheykh kuwa shine a gaba Yah Jafar da Affan dasu Jamil na biye dasu.
A cikin gidan kuwa, Junainah ce riƙe da hannun Yah Giɗi tana ɗan tsalle-tsalle tare da cewa.
“Yauwa Ya Giɗi muje lambu ka ciro min inabi mana”.
Gyara riƙon da yayiwa hannunta yayi tare da cewa.
“Ba Junaidu ya kawo miki wani ba ɗazu”.
Da sauri tace.
“A a ai na ajiyewa su Adda Shatu da Ummey na shi.
In sun iso zan basu”.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Toh ai kije kawai kici abunki, su tun jiya da yamma bappa yasa na ciro musu komai”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso ƙofar gida.
Da sauri Junainah ta saki yatsarsa tare da cewa.
“Oyoyo Ummey na Adda Shatu na”.
Tayi mgnar tana nufar inda suke a guje.
Da sauri Shatu ta buɗe mata hannu ta faɗa jikinta.
Ruggume juna sukayi suna dariya.
Giɗi kuwa da sauri yace.
“Kai maraba lale sannunku da zuwa”.
Ya ƙare mgnar yana isa gabansu Sheykh.
Da sauri Bappa ya fito jin muryar Junainah na cewa.
“Oyoyo Ummey na”.
Ai kuwa a cikin zauren yayi kiciɓis dasu Ummey cikin jin daɗi yace su isa.
Kana ya wuce wurinsu Sheykh yayi musu jagora har barandar ƙofar ɗakin shi.
Shatu kuwa kai tsaye ɗakin Ummey ta buɗe musu suka shiga.
Inna Amarya kuwa daɗi kamar ta haɗiye haƙorinta Allah ya sani sun shaƙu da Ummey tayi kewarta ainun.
Bayan sun zauna ne ta kalli Shatu tare da cewa.
“Shatu taso kizo ki kaiwa su Sheykh ruwa”.
Da sauri tace.
“Toh Inna Amarya”.
Kana tabi bayanta.
Tiren saƙar kabar dake cike da fruits danginsu Ayaba, inabi, tupa, yazawa, goiba, mangoro, danino, masu masifar sanyi kasan cewar cikin tulu suka kwana.
Sai kuma ƙwaryar damemmen fura da nono da zuma.
Da fefeyin kayan ya’yan itatuwa ta rufe ƙwaryar kana ta ɗauki kananan ƙore da ludayayeyin suma masu kyau, ta riƙe, kana ta miƙe ta nufi ƙofar Bappa.