
To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.
Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al’wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci.
Yayinda ko wanne garke an bar mutun ɗaya sabida tsaro…
Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.
Suna zaune, yaro yayi sallama, yace.
“Wai ana kiran Shatu a woje”.
Ummey ce ta ɗan juyo ta kalli yaron tare da cewa.
“Wake kiranta?”.
“Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne”.
Yaron ya faɗi.
Da sauri Ummey tace.
“A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo”.
To yaron yace kana ya juya ya fita.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa.
“Yace wai ince mata, ta fito woje”.
“Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa”.
Sai kuma Inna ta ɗan kalli Shatu tace.
“Tashi kije ai mun gama aikin ma”.
Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma,
kwano ta ɗauko a konɗonsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu.
Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon.
A hankali ta ratsa gefen su Ya Giɗi ta wuce.
Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da Arɗo Yabani ya tabbata.
Suna fita suka sameshi zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasu.
Da sauri Junainah ta isa gareshi tare da cewa.
“Oyoyo yaya Salmanu”.
Ajiye kwanon tayi a gefenshi.
Da sauri yasa hannunshin suka tafa da hannunta data miƙa mishi, cikin sakin fuska da nitsuwa yace.
“I miss you ƙanwali”.
Dariya mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
“Miss you too my dear”.
Dariya mai sauti sukayi a tare cikin jin daɗi wanda aka kira da Salmanu ya lakace hancin Junainah tare da cewa.
“Alhamdulillah alama ta nuna ƙanwaliya tana zuwa makaranta babu wasa”.
Cikin jin daɗi tace.
“Sosai ma ya Salmanu yanzu ajiyana huɗu fa, yanzuma dan hutu mukeyi, kuma gashi ko a gidama Ina karatu”.
Jinjina mata yayi da hannunshi kana, ya jawo kwanan data ajiye tare da cewa.
“Ƙanwaliya me kika kawo mim ne?”.
Cikin murmushi tace.
“Gasheshen naman tattabarune Ya Salmanu barima in koma ciki inci rabona inci na Addana”.
Kafin ya ankarama tuni ta juya da sauri tayi cikin gida.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da kallon Aysha dake jingini da bakin kofar zauren,
Cikin sanyi yace.
“Kamar bakiyi farin ciki da zuwana ba? Ko dai in komane?”.
A hankali tace.
“A a Ya Salmanu nadai ga kamar kafi farin cikin ganin Junainah ne akai na”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Kin rama kena”.
Murmushi sukayi dukansu, cikin sanyi yace.
“Ga wuri kizo ki zauna mana”.
A hankali tace,
“A a Ya Salmanu mu shiga cikin gida mana”.
“Kina tsoron kada saurayinki yazo ya ganmune?”.
Salmanu ya faɗa a hankali.
Da sauri tace.
“Eh”.
Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa.
“Babu abinda zai faru sai al’khairi zoki zauna, ki gayamin me kike tsoron?”.
A hankali ta zauna gefenshi ɗan nesa dashi.
Shi kuwa juyowa yayi ya fuskanceta a hankali yace.
“Gaya min me kike tsoro?”.
Kallonshi tayi cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ina tsoron kada Ya Ba’ana ya cutar da kai, ina gudun kada sakaiyar alaƙarmu ya zama cutarwa, sabida Ni kamin rana a rayuwata, rana kuma ta al’khairi shiyasa bana son abinda zai cutar da kai”.
Murmushi mai yelwa yayi kana a hankali yace.
“Ina sonki zan kuma aureki da izinin Ubangiji zan rabaki da wannan taƙadirin, domin baki cancanci zama matar mushurkiba”.
Da sauri tace.
“Kada kace haka Ya Salmanu Wallahi zai cutar da kai, kada ka bari wani yaji, bare mgnar ta koma kunnenshi”.
Murmushi yayi tare da jawo kwanon ya buɗe. Numfashin yaja jin ƙamshin naman a hankali ya fara ci, saida yaci ɗaya kab sannan ya rufe kwanon yace.
“Ga rabonki dan nasan Junainah ta cinye naki rabon”.
Cikin yanayin nitsuwarta tace.
“A a kaci kawai Ya Salmanu”.
Da sauri yace.
“No kada kimin musu”.
Shiru tayi jin yaci gaba da cewa.
“Muddin dai ina raye in sha Allah.
wallahi Allah bazan bari Ba’ana ya aureki ya lalata miki rayuwaba, zan jure duk azabar da zai shayar dani na shaɗi in Sha Allah zan aureki”.
Ido ta zuba mushi tana kallon shi cikin kamalarsa, ganin sam hankalinta ba’a kwance yakeba, yasashi ce mata ta shiga gida zasuyi mgna a waya, haka kuwa akayi, ta juya ta shiga gida shi kuma ya nufi hanyar gidansu.
A dandalin wurin da yake kamar kasuwar garin nasu ya samu abokanshi, kowa da budurwarshi suna ɗan hirarsu
Can gefe kuma ga yara nata wasansu, ga farin wata ya fito yayi ras, kana iya ganin komai.
Ita kuwa Shatu, bayan sun gama shirin baccinsu, ta kalli Ummey tare da cewa.
“Ummey”.
“Na’am”. Ta amsa mata cikin kula, sai kuma tayi shiru, ita kuwa Ummey ido ta zuba mata,
ganin hakane yasa a hankali tace.
“Ummey Ya Salmanu”. Still kuma tayi shiru,
Cikin kulawa da shaƙuwa wanda ke tsakanin uwa da yarta Ummey tace.
“Gaya min mana, me Ya Salmanun yayi?”.
Konciya tayi gefen Ummi dake bisa sallaya, kana a hankali tace.
“Wai yana sona, Ummey ina tsoro Ya Ba’ana zai illata mishi rayuwa, gashi kwanan nan Ya Hashimu ya rasu, kuma shima ance kasheshi akayi, Ummey ki cewa Bappa na, yacewa Baba Arɗo ya hana Ya Salmanu cewa yana sona, kinji ko Ummey?”.
Kai Ummey ta jinjina mata tare da cewa.
“To zaki aureshi kenan duk da kinsan baya salla kuma yana tsafi”.
Kai ta juya tare da cewa.
“Bazan aureshiba Ummey, amman ya Salmanu yayi shiru, bari in gama karatuna, in sha Allah akwai mafita in na gama karatuna, Ummey kin gane ai ko? Kin tuna ko”.
Murmushi Ummey tayi kana tace.
“Eh na gane, yanzu konta kiyi baccinki”.
da haka suka konta bacci.
Bayan kwanaki, sosai lamarin Ba’ana yake bawa mutane tsoro, mutun kamar ifiritu, dan yanzu yanayin sihirinshi ƙaruwa yakeyi sosai,
Wasu lokutan ba hawa ba sauƙa sai dai kawai ka ganshi a gabanka sabida yanzu layan ɓatarshi tama fi ta baya ƙarfi, ya dage wai zai bawa Shatu taƙi fir daya matsama kuka tasa mishi hakanne yasa ya hakura ya barta.
Ya Salmanu kuwa yanzu ya dage kan batun soyayyarsa da Aysha, ita kuwa tsoron abinda zai faru ya hana yarda da kowa, gaba ɗaya kuma yanzu Ƙabilar ɓachamawan nan masifa tuƙuru suke neman fulanin Bani dashi sabida baƙin ciki da hasadar ganin yadda shuke-shuken wurin fulanin yayi kyau, shinkafa, masara, dawa, gero, maiwa, wake, gyaɗa, gujjiya, riɗi, da dai sauransu.
Ga tarin bishiyoyi dorowa da suke zagaye da garin wanda kan ko wacce bishi akwai jingogin zuma, shiyasa garin suke da tarin zuma.
To waɗannan abubuwan sune suke ƙara tunzura kafuran, sabida gani suke aifa da filin nasune, sun mance kafin a saida wa fulani filin kufayine, fulaninne suke tafe da al’barkasu a jikinsu.
Zuwa yanzu kowa na Rugar Banin da kewaye yasan masoyan Shatu biyune, kuma za’ayi shaɗi, wanda tsawon shekaru biyu kenan ba’ayin ba.
Kowa in yaji da Salmanu za’ayi ana tausaya mishi domin shi mutunne mai laushin jiki shiyasa tun yana ƙaraminshi aka meda hankali kan karatun da yakeso, hakane yasa yayi karatun shi yanzu haka yana zama cikin Shikan ne inda yakeda shagunan kayan tireda sabida bazai iya noma da kiwo ba, kuma Alhamdulillah kasuwar ta amsheshi. Shiyasa shi zuwa yakeyi Rugar Bani ɗin.
A can ƙasa mai tsarki kuwa,
Yau kwanansu Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da Sittinshi goma da zuwa, to kasan cewar zasu gudanar da aikin Umarne yasa tun randa suka cika kwana uku da zuwa suka tafi, Madina,
Kuma sun bar mgnar batun Jazrah cewa sai sun gama gudanar da aikin Umararsu kafin su shaida mishi, kana in sun dai-dai ta da Jazrah sai su shaidawa Mai alfarma Sarki Jalaluddin, shi kuma yaje har Ɓadamaya ya shaidawa mai daraja sarki Nuruddeen Bubayero, da kuma Habeebullah, batun auren in yaso su shirya suzo ayi ɗaurin auren.