Da sauri ta ƙarasa cikin falon nashi tare da cewa.
“Assalamu alaikum Yah Sheykh gani da kusa”.
Da sauri yace.
“Wa alaikassalam (Y!.M!.D!.G!.) na! Nooryat Noor ƙalbi My love my happiness”.
Cikin jin daɗi tace.
“Yah Sheykh kenan kamar wasu yara”.
Da sauri yasa hannunshin ya kamo nata ya jawota jikinshi tare da ruggumeta ajiyan zuciya ya sauƙe tare da sa kanshi tsakanin wuyanta da kafaɗarta yana sunsunan wuyanta yace.
“Aish waya ce miki soyayya tana tsufa? Ai sai dai masu ita su tsufa.
Mu kuma bamu tsufan ba tukun”.
Ya ƙarashe mgnar tare da wucewa bedroom ɗinsa da ita.
A hankali ya meda ƙofar ya rufe kirib.
Tare da sauƙe nufamshi kana ya sunkuyo ya ɗagata ciɗak yayi kan gado da ita.
Cikin lumshe ido ta ƙanƙameshi gam a cikinshi.
Haka yasa suka kwanta a tare.
Da sauri yasa hannunshin ya ture rawaanin kanshi tare da cewa.
“Hegen nauyi da takura”.
Murmushi tayi tana mai kunce igiyoyin dake sarƙafe gaban al’kyabbar jikinshi.
Tare da cewa.
Ash Yah Sheykh nauyi”.
Mirgina wa yayi gefe ya kwanta kana ya jawota jikinshi ya zama sunan fuskantar juna.
A hankali ya kai lips ɗinshi kan mata wani ɗan sasayyan kiss ya manna mata kana a hankali yace.
“I missing You so much my love”.
Sai kuma taga ya ɗan juya da sauri ya kalli windows ɗinsa.
Fahimtar yana dubawa ko a buɗene yasata cewa.
“Yauwa Hamma Jabeer niko inda da wata tambaya data daɗe min a rai.”
Da sauri yace.
“Wacce tambayace haka faɗeta miji”.
Ya ƙare mgnar yana tura hannunshi cikin rigarta.
Hannunta tasa ta ɗan shafa sajenshi tare da cewa.
“Akwai lokuta da dama ina wani dalili yasa munje HOTEL duk ɗakin da ka kama in mun shiga sai ka bibbincika ka dudduba lungu da saƙo, wani lokacin ma kace in fita mu sauya ɗaki. Koma sauya HOTEL ɗin baki ɗaya, meyasa? Me kake dubawa?.”
Ronƙofawa yayi kanta yana zare zip ɗin rigarta yace.
“Ok ban taɓa yi miki bayani bako?.”
Da sauri ta gyaɗa kai.
Cikin nitsuwa yace.
“Wato shi HOTEL wani wurine mai cike da ƙalubale ga duk wani mutumin kirki, Especially in a cikin ƙasar ka ta haihuwa kake, domin da yawa har yanzu mutane basu fahimci cewa larura zata iya kaika hotel, ba lallai dole sai ɗan iskaba kamar yadda wasu ke zato.
Sai dai abin lura a nan abinda ya kamata ga duk ko wani musulmi, muddin larura ta kaika HOTEL, to ka tabbatar ka binciki duk ɗakin daka kama ciki da woje kama Daga jikin ƙofa, wurin kunna fanka, wurin ajiye Rimot ɗin AC,
Jikin AC, tsakiyar jikin fanka, saman silin, jikin ƙarfen labule, jikin TV Especially in suna fuskantar gado, da kuma jikin kan gado kofar Bathroom dama cikin Bathroom ɗin”.
Da sauri Shatu tace.
“Me yasa? Sabida me mutun zai tsaya wannan dube-duben duka!?”.
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Sabida mafi akasarin HOTEL’S wasu ƴan iskan kajeme kawai dan su dasa na’urar Camera a jikin duk waɗannan wuraren da na faɗa miki.
Ya ɗauka musu duk mu’amalar mata da miji ko ɗan iska da ƴar isa, daga nan sai su sarrafashi ya zama blue Film, da yawa waɗanda suke ciki basa sanin ana ɗaukar su.
Na’urar Camera da suke amfani da ita ƴar ƙanƙanuwace kamar botur ɗin rigar maza, in sun liƙata sai ta ɗauki komai.
Su kansu masu hotel basa sani.
Wasu lokutan kuma su ɗin ne da kansu ke dasata.
In baki mantaba akwai ranar da na samu camara ɗin ma liƙe a cikin abin AC. Har muka canza ɗaki masu hotel ɗin sukayi ta bani haƙuri suda kansu suka binciki ɗakin da muka sake shiga kin tuna.”
Cikin jan dogon numfashi tace.
“Eh tabbas na tuna Hamma, eh to lallai kuwa in hakane dole musulmai muyi taka tsantsan”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Shiyasa shi musulunci yana da daɗi kinga koda mutun baya bincika in yana amfanin da hadisin nan da manzon Allah ya hanemu da yin jima’i tsirara har sai an rufu.
Kinga mutun zai tsira.
To amman dai mafi sauƙi ka bincika kawai.
Dan in kayi garaje wata ran za’a yaɗaka a bazaka a duniya kana jima’i da iyalinka ace BF ka fara yi. Kaga anci zarafin ka anci zarafin addinin ka”.
Ya ƙare mgnar da fara yin ƙasa da rigarta.
Ita kuwa Shatu kai ta jinjina tare da cewa.
“Masha Allah da kamilin miji mai cikekkiyar kamala da Nagarta.
Sai kuma wata tambayar”.
Da sauri ya kwaɓe fuskarsa tare da cewa.
“Bazaki bari sai na nitsuwa ba dan in baki amsa mai kyau”.
Cikin narke mishi a jiki tace.
“Afwan kada in mance ne ai, kuma tambayar ba tsawo”.
Hannunshi yasa yana jan zariyar wondonsa tare da cewa.
“Toh ina jinki”.
Cikin maida nitsuwarta gareshi tace.
“Menene ma’anar (Y.M.D.G?)“.
Wani irin kekkyawan murmushi yayi mai cike da shauƙi yace.
“Sirri nane kalmar”.
Cikin fara murzashi tace.
“Dan Allah ka gaya min”.
Wani sassayan numfashi yaja jin salon da ta fara yi mishi.
Murya a narke yace.
“Sai in kinyi al’ƙawarin bazaki gayawa kowa ba”.
Da sauri tace.
“Nayi”.
Murmushi yayi tare da zare rigarta ya ture gefa.
Cikin raɗa yace.
“Zan gaya miki harufa ukun na huɗun na ƙarshe ki ƙarasa da kanki”.
Cikin zaƙuwa tace.
“Toh ina jinka menene ma’anar Y.M.D.G. Please bani amsa da sauri na zaƙu?”.
“Matso da bakinshi yayi kusa da kunnenta a hankali murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Y. Yana nufin Yarinya M yana nufin Mai D yana nufin Daɗin G ɗin kuma ki gane kinga ukun dai suna nufin
(Ƴarinya mai Daɗin…”.)
Narkewa jikinshi tayi tare da cewa.
“Please na tuba gaya min”.
Murmushi yayi tare da kai bakinshi bisa kunnenta a hankali cikin raɗa yace.
“Ƴarinya mai daɗin G…”
Da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen kunyan kalmar da ya rufeta.
Haka nan taji kanta na huruwa yana sama tana jinta a saman gajimare ashe waɗannan harufan abinda kenan suke nufi, iya wannan sunan da yake kiranta ya isheta gane matsayin yadda Yah Sheykh ɗinta ke gamsuwa da ita ɗari bisa ɗari.
Shi kuwa ya Sheykh cikin tsananin so, bege, shauƙi, kauna, yace.
“Allah sarki ƳAR FULANI mai kunya Alhamdulillah da Na samu sa’ar samunki dan da na rasaki to tabbas da NAYI NADAMA (MI WASMITI) kinga ko lallai na yarda shi NAMIJI BAYA KAƊAN dan da shawarar Affan na fara gano magautan mu.
Gashi a hankali muka samu Kekkyawan shaƙuwa da TAUSAYAWA JUNA sai daga baya na gano ashema ke BANDIRAWO ce a gareni tunda uwa ɗaya ce ta bamu tarbiya.
Gashi cikin ikon Allah RUBUTACCEN AL’AMARI ya ƙaddara saduwarmu da aurenmu cikin HUKUNCIN ALLAH harda yara.
GASHI MUN ZAMO tamkar hanta da jini.
Tsorona ɗaya a duniya kada RIGAR KOWA ta fara ɗaukanki ta barni.”
Wani sassayan numfashi ta fesar a hankali tana maijin tattausan kalamansa gareta. Shi kuwa Sheykh cikin gsky da gsky yaci gaba da cewa.
“Gwara ta ɗaukeni ta barki.
Domin duk da nasan cewa NAKASA BA KASAWA BACE tofa in ta ɗauke min ke ta barni zan rabu da rayuwar farin ciki domin Shatu kece GARKUWA a gareni sabida sam Rashin ki BA KASON ƊAUKA BANE Agareni.
Ya karashe mgnar tare da yujowa yayi mata rumfa da ƙirjinsa tare da jawo tattausan blanket ya rufesu yana mai cewa.
“Mu ɓuya Shatu na kada wannan ƴar darun Hammanta AYSHA ALIYU GARKUWA, ta hangomu ta samu abin rubutawa makarantanta. iyayen son ganin ƙoƙob sai kuma ya fara tasbihai tamkar yadda ya saba.
Subahanallahi Alhamdulillah wa la’ilahaillahu, Allahu Akbar Astagafirullaha…………………………!
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah na gode maka da ka bani aron rai da lfy da nitsuwa da kwanciyar hankali ka bani iko da dama na kare wannan littafina mai suna GARKUWA lfy kamar yadda na farashi lfy dani da makaranta shi baki ɗayansu.
Yah ka jiƙaina ka gafarta min al’farma Annabi da al’ƙur’ani a duk abinda nai kuskure, ka tsare min al’ƙalamina a karo na gaba.
Abinda nayi dai-dai ya Allah ka taramu bisa ladan nida masoyan Manzon Allah waɗanda in an haɗa su da Allah da manzo kan kada suyi abu bazasuyi shiba.