GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

To yau kwanansu takwas a Madinah kuma yaune suke shirin dawowa makka.

Kullum sai sun gaisa dasu Hajia Mama dasu Jalal.
Kullum yakan kira Juwairiyya.

Da maraicin suka isa cikin Makka kai tsaye masarautar suka wuce.

Bayan sun gaggaisa, Sheikh Aliyu yace suje su huta, kafin su gaisa da Sheykh Abdulkareem domin yana tare da manyan baƙi.

Haka kuwa akayi, bayan duk sunyi wonka suka dawo falon Sitti.

Suna zaune cikin shiga ta al’farma a wuri na al’farma, an zagayesu da dukkan kayan jin daɗin rayuwar duniya,

Sitti na zaune bisa tsakiyar falon akan wani tattausan carpet, Jannart da Jazrah suna gefenta, cikin shiga ta al’farma,

Sheykh kuwa zaune yake bisa wata lumtsimemiyar kujera kana sawunshi na kan wasu tim-tim masu masifar kyau da taushi, wasu kyawawan larabawane guda biyu suke zaune a gaban Sitti sawunta dake bisa tim-tim ɗin sukeyiwa tausa.
Yayinda wasu hadiman kuma ke shirya musu ababen ci dasha dangin yayan itatuwa kamarsu, Inabi, tupa, ayaba, dabino, gabaruwa, sai zam-zam kana, saisu shawarma and pizza da kuma wasu irin manyan Foodflaks da aka cikasu da danƙawa-ɗanƙwal dajaja sai sauran abincinsu na larabawa.

Haroon kuwa gefe yake kusa da Jannart suna ɗan taɓa hira.

Wayarshi ce ta fara ringgin a hankali, idonshi ya ɗan juya ya kalli wayar ba tare daya juya kanshiba,
Da idonshi ya nunawa hadimin dake gefenshi wayar,
da sauri ya ɗauko wayar ya miƙa mishi, ganin Hajia Mamace ya sashi amsa kiran.
Kara wayar yayi a kunne cikin girmamawa yace.
“Barka da dare Hajia Mama”.
A can gida kuwa cikin wani irin salo na musamman Hajia Mama ta rufe idanunta tare da cewa.
“Uhum ka manta Jabeer mu nan yammane”.
Idonshi ya ɗan ɗago ya kalli agogon dake jikin ginin, a hankali yace.
“Haka nefa Hajia Mama. Ya gida yasu Jalal”.
Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Suna lfy gasuma nan kusa dani, Jamil ne ya tsokano Jalal shine suka shigo sunata muzurai”.
Kanshi ya jingina da jikin kujerar, a hankali yace.
“Hajia Mama kiyi musu faɗa kice su barifa sun girma”.
Murmushi mai sanyi tayi tare da cewa.
“Na gaya musu sunma daina gasu nan sunata hira kuma”.
Gyara zamanta tayi kana taci gaba da cewa.
“Ina Sitti na?”. A taƙaice yace.
“Gata nan kusa dani”.
Cikin yanayin jin daɗi tace.
“Bata waya”. To yace kana ya miƙa Sitti daketa kallonshi wayar, da sauri ta amsa tare da karawa a kunne, murmushi tayi jin muryar Hajia Mama na cewa.
“(Allah beddu sabbugo Sitti), Allah ya ƙara nisan kwana Sitti”. Amin Amin tace, kana suka gaisa cikin tsananin jin daɗi.
Bayan sun gama wayarne kuma Juwairiyya ta kira Jannart nan suka gaisa ta bawa Sitti wayar hirar tasu kab kan ya Jafar ne. Saida suka gama wayarne ta kalli Sheykh dake kishinƙiɗe ya lumshe ido a hankali tace.
“Juwairiyya tace , yau tun safe Jafar ya shiga sashinka yayi ta nemanka ɗaki ɗaki, da bai gankaba yaƙi fitowa sai kuka yake tayi, har saida yammane da Jalal ya dawo gida shine ya lallasheshi ya maidashi sashinsu.
Hannu tasa ta share hawayenta da ke kwaranyowa, Haroon ma hawayen ne ke zubo mishi,
Haka Jazrah da Jannart,
Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace.
“Lamiɗo ya gaya min ɗazu da mukayi waya”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, a hankali Haroon ya miƙe kwance tare da faɗawa nazari mai zurfi.
Nan kuma kiran Umaymah ya shigo wayar Sitti still hira sukayi sosai wanda ta kontar musu hankali kafin, sukayi sallama da juna.

Yau jumma’a ne gajeren lokacine basa kai yamma a wurin kiwo, kafin azahar suke dawowa, shiyasa yau Shatu tace da ita za’aje kiwo.
Dariya kawai sukayi mata dan sun san ba iya jurewa zatayiba amman tunda ta kafa ta tsare cewa dole zataje, sai aka barta.

Kasan cewar basu kai yamman bane yasa kuma suna tafiya da wuri.
Bayan duk an kunce dabobbin gaba ɗaya, hakama sauran makiyayan baki ɗaya, sahu- sahu shanayen keta wucewa.

Sun tafi tun shida da rabi na safe,

Kafin zuwa tara na safe sunyi nisa cikin wurin kiwonsu, inda nan kuma Aysha ta samu su Hindema sunzo kiwo, wanda su kullum dama suna zuwa.

Wani irin hadarine mai ƙarfi ya taso daga ƙasa, ganin hakane yasa, Gaini kwallawa Shatu kira wacce take can cikin ƴan uwanta mata makiyaya, jin shiru bata amsa bane ya nufi wurin da suke zaune,
Cikin kula yace.
“Aysha tashi keda Hinde dasu Mero duk ku tafi gida, kunga hadarine mai ƙarfi ke tasowa daga ƙasa da alamun za’ayi ruwa mai ƙarfi”.
Cikin ƙarfin hali da son wasa cikin ruwan da taketa hari murya a sanyaye tace.
“Ba komai ya Gaini zamu jiraku ai lokacin tashi kuma ya kusa ko?”.
Su Giɗi dasu Aro da sauran makiyayan ne sukace.
“Ya Gaini barsu mana ba kiwo zasuyi ba ai makiyayin shanu da tumaki baya gudun ruwa duk yawa shi”.
Cikin jin daɗi sukace, eh mana,
Shi kuwa Ya Gaini murmushi kawai yayi tare da cewa.
“Shike nan yau zakusha dukan ruwa”.
Murmushi sukayi sukace “Babu matsala”. daga nan mazan duk suka koma wurin kula da dabobbin nasu da suka duƙufa cin koren ciyawa.

Su kuwa Shatu da Hinde a hankali sukaci gaba da tafiya, sosai tsarin wurin da yanayin shigar suturar dake jikinta yayi tsananin dacewa da ita.
Doguwar rigace irin tamu ta fulani, yadin farine, sai daga samanshi akayi mishi kolliya da zaron huɗu, mai color red white, blue, yellow, and green, wanda aka ƙawata saman rigar da kolliyar zanen ɗawisu, inda daga kafaɗunta har zuwa saman ƙirjinta, duk an shimfiɗa zaren, bisa wuyan rigar mai V.
sai kuma hannun rigar shima duk an zagayeshi da kolliyar,
Kana sai tsakiyar rigar dai-dai kan ƙugunta shima an ƙawatashi da wannan kolliyar ulu irin namu na fulanin daji,
Kana sai ƙasar rigar can itama an ƙawata da wannan zaren.

Sai dogon gashin kanta da yake zube a kafaɗunta, yayinda daga saman goshinta kuma tasa, bandana amman irin namu na fulani mai kalolin ƴaƴan tsakiya, ta zagaye kanta dashi, sai kolliyar da tayi a fuskarta irin ta asalin fulani, a goshinta zanen kan shanu tayi, shaidar cikekkiyar bafulatanace, sai kuma ƙasan lip ɗinta na ƙasa zuwa kan ɗan gemunta shi kuma taja zane da kuma yin ɗigo-ɗigo a gefenshi.
Sai wata kekkewar jakar sakan ulun mai kalolin kolliyar jikin rigarta data rataya a hannun damanta, wanda cikin jakar kuma ruwan shantane a ciki sai sassanyan kinɗirmo da goran zuma, sai ɗan sandar mu ta gado, takalman sawunta irin sau cikin nanne daku mutanen cikin birane kuke masa laƙabi da tashi kabi shanu.
Tayi masifar kyau a cikin wannan shigar tamu ta gado, kyau iya kyau farar fatarta ta baiyana tamkar balarabiya gashin girarta ya konta lib lib.

A hankali suke ɗan tattaki a cikin dogayen saunukan, da koriyar ciyawa da tayiwa ƙasanshi ƙawanya. suna ɗan tafe
Suna ɗan tsinkar ya’yan kanya da gwandar daji da suke cike da wurin Chaɓɓulle wato tsada.

Hadari kuwa sai gamgami yakeyi gabas da yamma kudu da arewa, ko ina yayi dib babu motsin komai sai nasu dana dabobbin su,
Iska ta tsaya cak koda ganye ɗaya baya kaɗawa duhu ya kareɗe illahirin yankin.

A hankali Hinde ta kalli sararin samaniya cikin tsoron ganin gaba ɗaya duniyar tayi baƙiƙƙirin ko ina yayi dib, hakanne yasata ɗan zaro ido tare da cewa.
“Kai Shatu, kalli sama, fa hadarin nan yayi duhu da yawa gsky mu tafi gida”.
Da sauri ta ɗago kanta kana tasa hannunta na hagu ta ɗan kare saman goshinta kaɗan, ware idanunta tayi ta kalli sararin samaniya, wani irin azabebben firgita da tsorone ya rufeta wanda yasa ta juya da azaban ƙarfi ta ruggume Hinde dai-dai lokacin, sukaga wani irin tartsatsin azabebben igiyar…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button