GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Jin jikinta yayi zafi jau ne, alamun zazzaɓi ne ya rufeta yasa, Ya Lado yaje ya ɗauko mata mgnin a ɗakin Bappa, nan Ummey ta bata tasha, a take bacci ya ɗauketa.

Ummey kuwa da Inna woje suka fito sunata dariya dan su a zatonsu ko gajiyane yasata hakan tunda ita dai bata saba zuwa kiwoba tunda tanada yayu maza da yawa.

Koda akayi sallam Juma’a aka idar, su Bappa da yaranshi kab basu dawoba saida akayi sallan la’asar kafin suka dawo gida.

Ummey kuwa da Inna aikin abincin dare sukeyi wanda girkin ranar jumma’a na dabanne, zabbi biyar suke yankawa kullum jumma’a wata rana kuma tattabaru wani lokacin kuma jan nama Bappa ke saya to yauma hakanne.

Inna ce zaune tanayi musu wonke-wonke yayinda Junainah kuwa keyin shara, dama wonke-wonke aikintane to duk randa takeji tsiya sai tayi ta ƙorafi, shiyasa yau tana farawa Inna ta fara aikin.
Ummey kuwa tana cikin kitchin ɗinsu, wanda dama da Shatu lfyarta lau muddin tana gida ita keyi musu, girki domin Ummey ta horeta da iya girke-girken na ban mamaki.

A hankali Shatu ta bude idanunta daga baccin da takeyi,
Cin karfin jikinta ya ɗan dawo, a hankali ta tashi zaune, da sauri ta fito woje, sabida ganin ita ɗaya ne a ɗakin.

Da sauri ta fito, Inna ce ta ganta cikin kula tace.
“Shatu kin taso?”.
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Cikin kula tace.
“To ya jikin naki?”.
A hankali tace.
“Da sauƙi, Inna zanyi wonka”.
Mikewa tayi dan dama ta gama wonke-wonken. Botiki ta ɗauka kitchin ta shiga, ruwan zafi ta ɗebo nan take cewa Ummey.
“Shatu ta farka”.
Murmushi Ummey tai tare da cewa.
“Na jita ai wai zatayi wonka, ke kuma harda biye mata kamar ta shekara ba lfy, Shatu ba dai rakiba”.
Dariya suka ɗanyi, ita kuwa a tsakiya gidan ta zauna kan dakalin da ke gindin bishiyar ceɗiya dake wurin.

Bayan inna ta kai mata ruwan ne ta kalli Junainah cikin sanyi tace “Junnu zoki rakani inyi wonka Mana.”
Ido Inna ta zaro tare da cewa.
“Hahhh Shatu yau kuma ta rakaki wonkafa kikace”.
Kanta ta gyaɗa cikin raunin fuska tace.
“Eh Inna tsoro nakeji shiyasa”.
Ummey dake kitchin ne ta fito rike da aikoshn data zuba zabbin data soya a ciki, tace.
“Shatu ki rage tsorofa”.
Kai ta gyaɗa kana taja hannun Junainah tare da ɗaukan kondon kayan wonkanta,
A bakin ƙofar mashiga bayan gidan tace.
“Yauwa Ƙanwaliya jirani a nan”.
To Junainah tace,
haka ta tsaya tana jiranta,
Ita kuwa wonkanta tayi, a nitse kana, tana fitowa.
Tayi al’wala, ɗakin Ummey ta shiga, sallan azahar da la’asar ɗin tayi, sannan ta zira wata tattausar doguwar riga.

Turare ta ɗan fesa kana, ta fito,
Gefen katangar kitchin ɗinsu ta samu Ummey tana haɗa wuta a murhun dake wurin.

Inna kuwa zaune take a gefe, da turmi a gabanta, kana tana jajjaga tattasai da tumatur da kuma tarugu da al’basa.

Taburman data fito dashine ta shimfiɗa gefensu.
Inna ce ta kalli Junainah da itama yanzu ta fito wonka tace.
“Yauwa Junainah zoki kawowa Addanki abinci.”
To tace kana tazo ta shiga ɗakin Inna.
Ta fito da tire a hannunta da wasu ƴan kananun robobi guda huɗu a kai masu marfi, sai kuma kula a tsakiyarsu.
A gaban Shatu ta ajiye kular.

Kana ta wuce ta nufi ɗakin Ummey.
Ita kuwa Aysha kular ta buɗe, dambun zogalenen a cikin wanda yaji, ganyen zogalen da kuma al’basa, sai tururi yakeyi.
Ƙananan robobin kuwa, ɗaya dakekken yajin ƙaragone wanda yaji magi da borkino da kuma tafarnuwa.
Kana ɗaya robar kuma, soyayyan man shanune a ciki.
Ɗaya kuma yankekken al’basane da kuma tumatur, sai dafeffe kwai duk a yayyanka,
Kana ɗayan kuma dambun namane mai laushi, a ciki,
ɗan karamin aikoshin dake gaban Ummey taja, ta zuba dambun, kana ta zuba sauran kayan hadin.
A hankali ta fara ci.
Junainah da ta fito yanzune ta kalla tare da cewa.
“Junainah bani ruwa”.
To tace kana ta juya ta nufi gindin randunarsu inda suke jere a ƙalla sun kai shida ko dan ba manya bane dukansu na taɓone masu ɗan karen sanyi, ga kuma inuwar bishiyoyin ayaba da sukayiwa randunar ƙawanya,
Shiyasa ko yaushe ruwan zakajishi kamar na firiji,
A kofin silver ta ɗebo mata kana tazo ta zauna gefenta, sunaci a tare.

Ummey kuwa tukunyar ƙasa ta ɗaura a wuta tare da tsulala man shanu, a ciki.
Kayan miyan da inna ta kirɓa ta amsa ta zuba a cikin manda yayi zafin ta fara soya miyar, zabbin da zatayi musu.
Kana ɗaya murhun kuma ruwan tuwo ta aza a tukunyan ƙarfe.
Inna kuwa data gama kirɓa kayan miyar, shinkafar tuwon ta ɗebo tazo tana wonkewa.

Suna cikin haka su Bappa da yayunta maza suka dawo.
Nan suka shimfiɗa katuwar taburma a tsakar gidan.
kana Giɗi ya ajiyewa inna ledodin tsarabar jumma’a da Bappa kanyi duk ranar sati.
Tirirruka Ummey ta miko mata ta baza, juye kayayyakin a cikin.
Reke,Lemu, kwakwa, da Giginya, da kuma dafaffiyar gyaɗa, da ƙosai mai zafi da biredi da soyayyen doya da fulawa mai jawa.
kayan cimarmu kenan fulani

Zubawa maza nasu akayi, aka basu a tsakiyarsu suka ajiye sunaci da mahaifin nasu.
Shatu kuwa da Junainah aka basu nasu. Ummi da Inna kuwa sun ajiye nasu dan aiki sukeyi.
Ya Gaini ne ya ɗan danki ƙosai da bredy yasa a bakinshi,
tauwana yayi kana idanunshi na kan Aysha saida ya haɗiye kana yace.
“Shatu, ya jikin naki?”.
Murmushi ta ɗanyi sai kuma ta ɗan harari Junainah dake cewa.
“Uhum ta worke ai dama kawai hegen tsorone da raki”.
Dariya sukayi baki ɗayansu. Seyo ne wanda yakeda tarin jinƙai da nitsuwa,
ya ɗan afa geɗan daya ɓare a bakinshi tare da cewa.
“To Amman Shatu meya samekine lokaci ɗaya kika firgita?”.
Giɗi ne da shi kuma doya yakeci yace.
“Kamar mai cutar al’janufa ta zama”.
Bappa ne ya ɗan kalleta cikin kulawa yace.
“Shatu meya sameki ne?”.
Murmushi ta ɗanyi tare da kallon Ummey dake cewa.
“Uhum tsorone da gajiya fa”.
Kai ta jujjuya a hankali tace.
“Allah ko Ummey ba tsoro bane”.
Sai ta kuma meda hankalinta kan Bappa cikin sanyinta tace.
“Bappa naga abinda ya firgitanine.
Shin Bappa dama bakan Gizon cikin curi yake fitowa ne?.”
Cikin mamaki suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Bappa ne da kanshi yace.
“Ban fahimceki ba Shatu”.
Bredy dake gefenta ta gutsura kana ta dandola da zuman data sa Junainah ta kawo musu, a baki ta ɗansa ta tauna kana a nitse ta basu labarin abinda ta gani da kuma yadda taji, ta ƙara da cewa.
“Bappa dama bakan Gizo a curi suke fitowa ne?”.
Cikin mamaki da al’hini yace.
“Allahu al’alamu. Sai dai koma menene, lallai tabbas akwai abinda ke tunkarar rayuwarmu, fatana mu dage da addu’a koma menene Allah ya kawo mana shi kan al’khairi ya kuma sauƙaƙa manashi, zan kuma bincika in sha Allah.
Sannan kada ku gayawa kowa mgnar nan”.
Ya karishe mgnar da kallon Junainah.
Wannan labari ya sasu cikin dogon nazari. haka dai sukaci gaba hira kamar yadda suka saba.

A can cikin yola kuwa, yau tunda Ya Jafar yaje sallan juma’a ya dawo baiga Ƙaninshi Sheykh ba, gaba ɗaya ya tashi hankalin ƙanenneshi da iyayenshi.
Domin kama hannun Jalal yayi yana kuka, yana jan Jalal zuwa sashin Sheykh koda suka shiga, Jamil kuwa sashin mahaifinsu ya nufa. Ba tare da ya saurari
Hadiman ba ya wuce.
A babban falon ya samu , Abba
Haurawa sama yayi yana shiga kuwa ya sameshi a falo shida jarabebboyar amaryar tasa cingom dinshi.
Sai dai tana konce bisa kujera,
Shi kuma yana zaune bisa sallayane ya fuskanci al’ƙibla, da ƙur’ani a gabanshi yana karatu cikin suratul Khafi.
cikin rauni Jamil ya ƙaraso gabansa.
Bai kulashiba har saida ya kai ƙarshen surar kana ya shafa addu’a.
Cikin haɗe fuska da alamun faɗa yace.
“Jamil lfy kuwa mehakan?”.
ido na zubda hawaye yace.
“Abba Ya Jafa”.
Rai a hade yace.
“To me zan mishi?”.
Cikin zubda hawaye yace.
“Abba tunda aka dawo aka sauƙo sallan jumma’a fa yaketa kuka yana bin Jalal yana kuka alamun a kaishi wurin Hamma Jabeer, yau ko abinci baiciba, Aunty Juwairiyya ma sai kuka takeyi hakama su, Jiddah.”
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
“To ni zaka gayawa? Kaje ka gayawa Mamanku mana”.
Wasu sabbin hawayene suka zubowa Jamil a hankali ya juya ya fita”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button