
Amin Amin yace kana ya juya ya tafi.
Ita kuwa Shatu cikin tsoro ta kalli Ya Salmanu a hankali tace.
“Ya Salmanu tashi ka tafi kada yazo ya sameka”.
Cikin harshen fillanci yace.
“To shi mala’ikan ɗaukan raine? Ko dai so kike in guje masane Shatu, kina son ragon mijine?”.
A hankali tace.
“A a Ya Salmanu zai cutar da kaine nake tsoro”.
Da sauri ya katseta da cewa.
“Babu mai rayawa da kashewa sai Allah, ko yaya zaiyi bashi da ikon kasheni sai in kwana-nane ya ƙare. Ko ciwon kai bai isa ya samin ba”.
Shiru tayi tana kallonshi.
Sai kuma tai maza ta miƙe tsaye ganin kamar daga sama aka jefo Ba’ana gabansu.
Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa.
“Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haɗa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaɗi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ƙasar nan gaba ɗaya zan koma ƙasar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki ɗayanta!”.
Cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Shatu tace.
“A a fa Ya Ba’ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min”.
Da sauri Salmanu ya katseta da cewa.
“Sonta nakeyi Ba’ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar Shaɗi da kai a ranar Litinin na amince”.
Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace.
“Lallai gidan Arɗo Yabani na gab da rasa motsin ɗana miji”.
Yana faɗin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya ɓaci.
Cikin ƙarfin hali Salmanu ya nufi gida.
Shi kuwa Ba’ana yana ɓacewa a tsakiyar dottawan Fadan Arɗo Yabani ya baiyana,.
Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi.
So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa.
“A a Ba’ana lfy kuwa?”.
Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace.
“Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al’farma fagen shaɗi, nida Salmanu ɗan Arɗo zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki ɗaya”.
Da sauri Bappa yace.
“A a”.
Da sauri Arɗo Yabani yace.
“A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar Shaɗi mai nasara yaci gasar”.
Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru.
Shi kuwa Ba’ana cikin tarin ƙeta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci.
“Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taɓa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu”.
A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi.
Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda Shaɗin zai kasance.
Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar Shaɗi da za’ayi jibi litinin, da kuma, waɗanda zasuyi gasar da sunan wacce za’ayi dan ita.
Gaba ɗaya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici,
Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ƙarar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za’ayi gasar Shaɗi da mutun da sun san ba’a taɓa nasara a kansa a.,
Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da Arɗo Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu.
Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi.
Shi kuwa Ba’ana tun ranar ya ɗauki tunƙur ƙasar da yake tsuma bulalinshi, ya kaishi Ƙauyen Bonon, gaban dodon tsafinsu,
Anan tukunyar ta kwana bulali tamanin dake cikin tunkuyar nan aketa tsumawa da tsafi.
Kana an jikasu da ruwan gishiri sannan an juye kunamai sama da ɗari a ciki, irin baƙaƙen kunamun nanne masu mugun dafi, an sasu ciki sunata harbin bulalin nan suna sa dafinsu a jiki. ranar lahadi da yamma ya amso tukunyar,
Har zauren gidansu Shatu yaje yasa aka kira mishi ita bayan ta fitone yace ta leƙa cikin tukunyar, a hankali tace.
“Me zan gani a ciki?”.
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
“Nazo in nuna miki bulalin shaɗi nane, ki gansu da kyau, dan ki cewa wancan koɗeɗden ya shirya shan zabga”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Ni ba sai na ganiba”.
Murmushi yayi tare da buɗe tukunyar kana ya karkatar mata shi gabanta.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
“In……
Littafina na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ko karanta a nitse.
By
*GARKUWAR FULANI*????????????????????????????????????????????
????️????????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 10
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????️????????????????????????????
LITTAFIN GARKUWA NA KUƊINE, TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta number 09097853276 domin samun cikekken labarin, ko kiyi min transfer ɗin 1k ɗan samun SP GROUP ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276
FREE PAGE
Cikin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ya Ba’ana me wannan, abu kamar macizai”. Da sauri ya meda ya rufe kana ya miƙe cikin yin ƙasa da murya yace.
“Kinga ni kada ki tayarmin da hankali kinsan bana son ganinki cikin tashin hankali, in sha Allah nine da nasara ko dai bakya so nane”.
Da sauri ta girgiza kanta tare dasa tafin hannunta ta rufe bakinta.
Ganin haka ya kwashi abinshi ya tafi.
Ita kuwa koda ta shiga gida, gefen Inna ta zauna tare da cewa.
“Inna ku cewa Bappa ya cewa Arɗo ya hana gasar nan, kada a cutar da Ya Salmanu”.
Cikin sanyin jikin da duk kwanan haka inna ta zama, a hankali tace.
“Uhumm ba komai Shatu in sha Allah duk abinda zai faru da sanin Allah.
Yanzu ke yaushe nema zaki koma hutunmu?”.
Kanta ta gyaɗa a hankali tace.
“Rana ita yau zan koma kimga saura mako ɗaya kenan”.
Ummey ce dake gefe ta ɗanyi ajiyan zuciya gami da cewa.
“Alhamdulillah ni in kin komama hankalinmu zaifi konci, domin muddin kinanen sai Ba’ana yayi ta kalato fitina”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, jin an fara kiran sallane tasa, duk kowa yayi al’wala haraman salla.
A daren ranar kuwa Ya Salmanu da abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za’ayi kuma tunda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.
Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
Haɗuwa a filin da za’ayi shaɗi.
Mutanen sun cika maƙil dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.
Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan Arɗo Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman Arɗo yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa.
“Haƙiƙa naso a janye wannan shaɗi, domin nasan abun bazaiyi daɗin ganiba ace Ba’ana na zane Salmanu ɗan Arɗo ga wannan rugar, amman kaƙi ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda ɗana yayiwa ɗanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taɓa samun wanda zaifi ƙarfin ɗanaba”.
Shiru Arɗo Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi Arɗo Yabani yace.
“Duniya da faɗi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za’a samu wanda zaifi ƙarfin ɗan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin ɗan ka”.
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
“Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taɓa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu”.
Wani dogon numfashi Arɗo Yabani yaja tare da cewa.
“Uhummmmmm”. Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaɓe rigarsa ya juya ya tafi yana faɗin.
“In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira”.
Da ido Arɗo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam Chuɓaɗo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.