
Salon na dabanne labarine mai cike da sarƙaƙiya, biya 300 ko 1k ki karance badaƙalar cikin salama.
By
*GARKUWAR FULANI*
????????????️????????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 2
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????️????????????????????????????
LITTAFINA na kuɗine, akwai na 300 wanda a wata ɗaya za’a gama Part 1, akwai kuma na 1k wanda a mako biyu kacal za’a gama Part 1 da izinin Allah. Yimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1ooo ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar BIYANKI ta number 09097853276 Ayyah ƴan SP Group banda kati, in baki da ac bada a POS. Kuna ƴan 300 in dai da hali turamin ta ac yafi, in babu kuma to turo katin mtn na ɗari uku ta layin 09097853276. Na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san niyarki ki saya ki fiddamin littafina, dan daraja da girman Allah da tsarkin al’ƙur’ani kada ki saya Please kuwa darajar iyayenki kada ki saya, ba don niba sai ɗan Allah da manzonsa da iyayen da suka haifeki/ka
~AKWAI KAYAN GYARA HAƊIN AMARE DA MASU JEGO, DA MASU SABUNTA AMARCI, IN KINASO KI TUNTUƁI WANNAN NUMBER 09097853276~
Ta juye ta dawo mutun bani Adam mace fara ƙal mai tsananin kyau da cikar sura da haiba.
Wani irin zabura sukayi cikin tsananin tsoro da firgici da tashin hankali suka zaburi gaba ɗayansu, Giɗaɗo kuwa da azaban ƙarfi ya afka jikin Arɗo Babayo,
Inna kuwa gaba ɗaya jikinta rawa da karkarwa yakeyi tamkar mazari wata iriyar fitinenneyar zufa mai azabar ƙarfice taketa tsastsafo mata tako wani sashi na jikinta.
Seyoji, Gainako, da Ja’eh, gaba ɗaya jikinsu karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Giɗaɗo kuwa wani irin juyawa yayi a firgice ya yunƙura zai gudu, Arɗo Babayo ne yayi hamzarin kamo hannunshi ya rikeshi gam.
Zabura sukayi.
Gaba ɗayansu sabida wata iriyar fitinenneyar iska mai azabebben sanyi daya fara kaɗawa yana rausaya ganyayyaki da dukkan tsirran dake yakin surururururu haka iskar ke kaɗawa a hankali tana ratsa jikinsu.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun. Hasbunallahiwani’imanwakil”.
Shine abinda suketa maimaitawa gaba ɗayansu cikin tsananin kaɗuwa, ruɗani, firgici, tashin hankali da tarin tsoro, da nitsuwar ganin ikon Allah.
Iskar dake karkaɗawa ce tasa gaba ɗaya suka hautsine.
Parvina kuwa da sauri ta faɗa jikin baiwar Allah’n tare da ruggumeta.
Baki na rawa ta fara addu’a.
“Allahumma inni as’aluka khairaha wa’azubika min sharri ha”.
Da ƙarfi take fidda sautinta tana maimaita addu’ar.
Wanda sanadin haka suma kab suka fara bin bakinta.
Allah cikin ikonsa da ƙudurarsa sai ga iskar nan ta fara lafawa a hankali.
Cikin al’ajibi da tsoron ƙudurar Allah suka ware idanunsu baki ɗaya a kan baiwar Allah’n nan, da
shigar suturar dake jikinta ne yayi masifar sasu ruɗani.
Cikin dakiya da ƙarfin zuciya Arɗo Babayo ya kalli Buba a hankali yace.
“Buba ɗauki su Giɗaɗo ku tafi garke kuje kuyi tatsa”.
Kai ya gyaɗa mishi domin baki da jarumar Buba sun tafi,
Dan a iya tsawon tarihin rayuwarsa ko a films ko a books story bai taba ji da katari da makamancin abinda ya yagini a zahiriyaba, tsuntsuwar Kurciyar ta zama mutun mace a gabanshi ba labari aka bashiba ra’anul ayni.
Cikin yanayin tarin kaɗuwa da rawan jiki yasa hannu ya jawo hannun Giɗaɗo daya kifa kanshi jikin babanshi.
Cikin fillanci yace.
“Zo Giɗaɗo zomu tafi”.
Da sauri ya miƙa hannunshi ya kama na Buba kana suka juya suka fita.
Appa kuwa kanshi ya kauda daga kallon wannan kekyawar halittar dake gabanshi a cikin ransa yace.
“Anya kuwa, wannan mutunce ba iskaba”.
Inna kuwa gefe ta ɗan matsa cikin rawan murya na tsoro da hausar da sai ka dage zaka gane me take cewa tace.
“Ra ga Allah bewar Allah mutun ko al’jan?”.
Ido suka tsurawa matar a zatonsu ko zata basu amsa.
Sai dai ganin yanayin da take cikine ya sasu cire tsammanin samun amsarta.
Domin gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, tamkar mazari.
Kana sai zufa dake tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta,
ta rumtse idanunta da azaban ƙarfi, tasa haƙoranta ta datse lip ɗinta na ƙasa,
duk mace data taɓa haihuwa in ta ganta tasan naƙudace ke azazzabarta.
Tausayin ta ne ya cika zuƙa tansu baki ɗaya.
Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace.
“Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al’jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al’amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace”.
Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa.
Appa ne ya kalleta tare da gyaɗa mata kai, alamun eh ta taimaketa,
Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace.
“Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata”.
Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace.
“Zo nan Parvina za’a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta,
kinga ki dena danne mata hannun da cikinta”.
kai ta gyaɗa kana ta kalli matar cikin sanyi tace.
“Sannu!”. Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu,
haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba.
cikin sanyi tace.
“Taso muje daga ciki”.
ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji,
hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye.
Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas.
Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin ɗakinta ta kaita,
a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta,
da sauri ta koma woje wuta ta hura ta ɗaura ruwan zafi.
Kana ta dawo ciki.
Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta.
Gefenta ta zauna ta zuba mata ido.
Jin an zauna gefen tanne yasa ta buɗe kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace.
“Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?”.
Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji,
murmushi inna tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana”.
Kanta ta jujjuya mata alamun.
“Bazan iyaba”.
Jin muryarsu Arɗo Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito,
Ganin Arɗo Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa.
“Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa”.
Taburma ta shimfaɗa musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa.
“A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?”.
“Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne”.
Inna ta faɗa cikin alhini.
Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
“Ina son ganinta”.
Arɗo Babayo ne yace.
“To bisimilla, shigo daga ciki”.
Ɗakin suka nufa Inna na gaba Arɗo Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya.
Suna shiga suka sameta zaune ta haɗe jikinta wuri ɗaya,
jin motsin shigowar mutanene yasa ta ɗago kanta,
da sauri ta kauda idanunta.
Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al’hini yake cewa.
“Mutun ce ba al’janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki.”
Sai kuma ya kalli Arɗo Babayo cikin sauri yace.
“Maza a bani madarar shanu mai ɗumi wanda aka tatsa yanzu”.
To Arɗo Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono,
da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin.