Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ƙanin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar ɗan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sauƙi.
Shi kuwa Ba’ana daga nan izayarsa ta ƙaru manufarsa shida ƙabilar ɓachamawa shine. Su tarwatsa al’ummar fulanin Rugar Bani baki ɗayansu.
Zuwa yanzu kuma ko ƙudane in dai na mijine to bazai sauƙa kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.
Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.
Yau kwana huɗu da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma’a ne.
Kasan cewar jummace yasa gaba ɗaya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam’in sallan jumma’a.
Iro ɗaya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haɗu da gungun matasan Ɓachamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
“Kai ɗan fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?”.
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
“Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani”.
Cikin mugunta ɗaya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi”.
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
“Kada ka sake dukana”.
Kusan a tare suka haɗa bakin wajen cewa.
“In mun dakeka sai me?”.
A kufule yace.
“Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba”.
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da ɗan lenge-lengen saurayi matashi ɗan Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, ɗaya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ƙugunshi, da ƙarfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wuƙan a cikinsa wani irin ƙara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma’a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda suka daddatseshi da wuƙa.
Daga nan suka kira Ba’ana a waya, nan take ya kaɗa shanayen yace. “Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza’a zargekuba”.
Haka kuwa sukayi, suka kaɗa kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce ɗakinsa bayan ya bawa uwarsa lbri.
Koda aka taso sallan jumma’a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la’asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ƙara tashi.
Cikin kiɗima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba.
Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji,
Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini.
Nan suka ɗauki gawa suka koma cikin gari dashin.
Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba ɗaya ma sai ba’amaida hankali kam ɓatan shanunba,
Hankali ya tashi, ɗauki ɗai-ɗai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin,
Gashi kisane da babu wanda za’a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case ɗin, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers ɗin shiyasa suka korasu da batun.
Salmanu wanda shine ɗan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ƙarƙashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba’ana ya kasheshi.
Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka Arɗo Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan ɗin, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero.
Koda sukaje masarautar Numan ɗinma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu.
Dole suka dawo suka nade hannun suka kai kukansu ga, Allah, sai dai sun ɗauki mataken kare kai da kai, bisa shawarar daddatawa cewa kada makiyayan ko manoma su yarda su rinƙa rabuwa a daji ya zama suje tare su dawo tare da hakane zasu gane mai ke musu ɗauki ɗai-ɗai ɗin.
Yau la’hadi tunda safe, Aysha keta shirin komawa makaranta. Sabida hutunsu ya ƙare.
Tafiyan safe takeso tayi shiyasa ta gama shirinta da wuri.
gaba ɗaya suna tsakiyar gida Yayunta maza sune zasu rakata bakin hanya.
Haka nan taji bata son tafiya ta barsu, tsoro mai yawa ya rufeta Especially in tayi tunani da yadda ake kashe makiyayan.
Durƙushe take gaban Bappa yana yi mata masiha mai ratsa jiki da zuciya ya kare nasihar tashi da cewa.
“Allah ya miki al’barka Shatu, Allah ya kaiki lfy.”
cikin sanyin murya tace.
“Amin Amin Bappa ngd matuƙa”.
Sai kuma ta kalli Ya Giɗinta da ya zuba mata ido tamkar bai taɓa ganintaba, cikin sanyin murya yace.
“Yanzu shike nan zaki tafi ki barmu, ki tafi can ke ɗaya ki zama baki da kowa naki a kusa”.
Haka nan kalamanshi ya karyar mata zuciya, sai kuma taji hawaye nason zubo mata.
A hankali tace.
“Ya Giɗi bazan daɗe ba zanzo”.
Cikin sanyi Seyo yace.
“Allah yasa ki samemu in kinzo ɗin”.
Da karfi ƙrjinta ya bada wani sauti mai karfi, ta buɗi baki zatayi mgna kenan Ya Lado ya ɗanyi murmushi cikin sanyi yace.
“To Shatu Ni zan tafi inje in kunce dabobbin, bazan samu daman rakakiba, Allah ya kaiki lfy, ya ƙaddara saduwarmu kan al’khairi, ki yafe”.
Kawai sai taji hawaye na zubo mata, cikin dariya ya Gaini yace.
“To kunga kun sata kuka, Shatu ko dai bakya son komawane?”.
Cikin rawan murya tace.
“Inaji bana son rabuwa daku”.
Murmushi inna tayi tare da cewa.
“Ai kuwa dole ki rabu damu, domin lokaci yazo”.
Ummey dai ido ta zuba musu.
Shi kuwa Ya Lado da murmushi a fuskarshi ya fita yana ɗaga mata hannu.
Bappa ne ya ɗanyi murmushi cikin sanyi jiki yace.
“Maza tashi ki tafi, ki gaida Aminiyarki Rafi’a, Seyo Giɗi Gaini ku rakata har bakin titi”.
Da sauri suka miƙa.
Ita kuwa Aysha kamo hannun Junainah tayi wacce tayi kasake tana kallonta cikin sanyi tace.
“Ƙanwaliya, sai na dawo”.
Kai ta gyaɗa mata cikin sanyin da sam ba ɗabi’arta bane a hankali tace.
“Addana, bana son ki tafi”.
Shafa kan Junainah tayi, kana ta faɗa jikin Inna, tana zubda hawaye, sake Inna tayi sannan ta faɗa jikin Ummey, murya can ƙasa Ummey tace.
“Tashi ku tafi, Allah ya sadamu da al’khairi, Shatu”.
Da kuka ta fita, ta barsu jiki a mace.
A hankali suke tafiya tafiya, suna hira, kayan lambu da suka cika mata bakko dashi na hannun Giɗi, jarkan nonon kuma na hannun Seyo, ya Gaini kuma, jakar kayantane a hannunshi, da kwaryan kwan zabbi, kamar dai yadda suka saba, suna tafe suna, hira suna gab da bakin hanya.
Ba’ana ya isosu aka ci gaba da tafiyar,
suna isa motar da zata wuce cikin Yola (Ɓadamaya) na isa,
saida suka samata kayanta, kafin, tazo har zata shiga taji Giɗi na riƙe da hannunta juyowa tayi ta kalleshi cikin murmushi yace.
“Kinsan abinda zamu iya aikatawa a duniya da abinda bazamu iya aikatawaba”.
Kai ta gyaɗa mishi alamar eh, murmushi yayi kana yace.
“To ki ƙara yarda zamu zamu zama GARKUWA’nki muddin muna raye.”
Murmushi tayi cikin ɗan jin daɗi tasan akan mgmar auren Ba’ana yake nufi.
Ido ta zubawa Ya Seyo shi kuma sai murmushin shi nan yake mata,
Ya Gaini kuwa hawayene ya cika masa ido shiyasa ya juya ya bata baya.
Cikin sanyi Seyo ya matsota kana a hankali yace.
“Ki sanarwa duniya halinda muka ciki in kin samu dama Aysha, ki sanarwa duniya Fulani ba ƴan ta’adda bane ba ƴan bindiga daɗi bane ba kuma ƴan Garkuwa da mutane bane, wasu kesa rigar Fulani ke wanzar da ɓarna da wasu ƙalilan na mugayen daji.”
Cikin rauni ta zuba mishi ido tana kallon kekyawar fuskarsa, da gyaɗa mishi kai.
Ba’ana ne ya ɗan kalleta tare da miƙo mata damin kuɗi yace.
“Mata zanyi kewarki, amman ba matsala duk ƙarshen mako zan ke zuwa.”
Drivern ne ya katse su da cewa ta shigo su tafi, haka yasa ta juya da sauri ta shiga, yaja suka tafi tana ɗaga musu hannu, suma basu tafiba saida sukaga motar ta ɓace musu.