GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

GARKUWA COMPLETE NOVEL

Juyawa sukayi suka nufi cikin gari.
Shi kuwa Ba’ana da ido ya rakasu a a baiyane yace.
“Zanga ta yaya zaku zama GARKUWA’nnata, dan na fahimci duk bakwa son aurena da ita, toko zanyi mgninku.”

Su kuwa basuma juyo sun kalleshi ba.

Ita kuwa Aysha tana komawa ta samu, Rafi’a ta dawo ta gyara musu komai na ɗakinsu, to samun Rafi’a da tayine yasa ta ɗan samu nitsuwa, ranar kam wuni sukayi suna hira, darema haka sukayi ta hirar yaushe gamo.

A Rugar Bani ( Rugar kikan) kenan nake nufi. kuwa, su Ya Gaini suna komawa suka tafi kiwo, kamar dai yadda suka saba, sukaje kiwo lfy suka dawo lfy.

Washe gari ranar Litinin!

             Saudia.

Sheykh ne konce, bisa wani fitinenne gado yayi lib cikin tattausan blanket,
bacci yakeji yasa gaba ɗaya jikinsa yayi lakwas sabida jiya a harami ya kwana ɗawafi, shiyasa yana dawowa ya konta. Yanayin wayarrshi na bada ɗan sassanyan sautin,
wani irin ɗan gajeren tsaki yaja, ba tare daya buɗe idanunshiba ya miƙa hannun kan bedside drower’n glass dake kusa dashi, lalubo wayar, yayi tare da ɗan liƙa yatsarsa kan gilashin wayar ya amsa kiran, kana ya ɗauwara wayar bisa kunnenshi a hankali cikin muryar bacci yace.
“Assalamu alaikum, Umaymah”.
Murmushi Umaymah tayi cikin son ɗan yar uwartata tace.
“Na’am Jazlaan ya akayi”.
Cikin murya baccin ya kuma gyara konciya tare da cewa.
“Umaymah baki amsa sallamar ba”.
Da sauri tace.
“Afwan Jazlaan, Wa alaikassalam”.
shiru yayi.
ita kuwa murmushi tayi tare da cewa.
“Naji kamar bacci kakeyi ko?”.
Murya can ƙasa yace.
“Uhummmm”.
Da sauri tace.
“To yi baccin sai ka tashi muyi mgna nasan a harami ka kwana”.
Da sauri yace.
“No Umaymah gaya min menene?”.
Dan shi a zatonshi ko akan Ya Jafar ɗinshi ne.
Ita kuwa Umaymah cikin hikima tace.
“Uhum dama batun Jazrah ne”.
Fuska ya kwaɓe kamar yana gabanta cikin nuna ko in kula yace.
“Menene kuma hakan? Umaymah”.
Kai ta jinjina dan tasan a rina, cikin tsare gida tace.
“Ina nufin Jazrah ƴar Ƴayan Sitti Uncle ɗinmu Aliyu”.
Numfashin ya ɗan fidda cikin ƙosawa da zancen yace.
“Ni ban santaba. Umaymah zanyi bacci, kaina ciwo.
Kin yarda in katse kiran Please Umaymah kada kicemin a a dan Allah”.
Murmushi tayi wato duk yadda mutun ke zaton Sheykh ya wuce tunanin mai tunani a hankali tace.
“Kashe, Allah ya muku al’barka”.
Da sauri yace Amin Amin kana ya katse kiran,
hannu yasa ya cusa wayan ƙasan pillow’nshi.
Kana ya gyara konciyarshi afili yace.
“Ni ina zan kai mace? Toma me zanyi da mace a rayuwata.
Zakuna damuna da wata Jazrah mai koɗeɗden fuska”.
Daga nan ya lumshe ido yaci gaba da baccinsa.
Haroo dake bakin kofar shigowane yayi dariya kana yace.
“Uhum zaka san me zakayi da ita ai Ustadz ai ba’a gane maci tuwo sai miya ta ƙare, dama kirarinku ustazu ƙalilan iya shege kasiran, wai me zanyi da mace, hmmm miskilanciba ba”.
Daga nan ya koma da baya dan dama Sitti ce ta aikoshi ya kira mata Sheykh ɗin, akan yazo yaci abinci kafin yayi baccin wai.
Koda ya koma sanarwa Sitti cewa yama rigada yayi baccin sai suka zauna na nan sukaci gaba da hiransu…

A nan gida Nigeria kuwa cikin Rugar Kikan.
Tunda safe duk makiyayan garin suka tafi kiwonsu.

Sosai suka shiga irin tsakiyar tsaunuka, wasu na nan wasu na can suna dai hango juna da, sabida abu na kiwo bazai yiwu su zauna wuri ɗaya ba, dama sai in zasu komane suke haɗuwa baki ɗayansu.

Misalin karfe uku da rabi na yamma, duk kowa ya fara ɗan zagawa cikin kwazozzobon dake gefensu da. Yin ɗaharan yin al’wala.

Ya Gaini ne ya fara gangarawa cikin korin babu sanda bare wuƙa a jikinshi. Ko buta babu a hannunshi Don akwai ruwa a cikin kwarin dashi suke al’wala, a hankali ya tsuguna yayi buƙatarsa kana.
Ya dawo wurinda suke al’wala ya tsugana yayi al’wala.
A hankali ya yunƙura ya tashi.
Ɗago kanshi da zaiyi yayi dai-dai da…..!

                     By
               *GARKUWAR FULANI*

Wasa farin girki, yanzu ake nutsawa ciki.

Da yawa naga basu fahimci banbancin. Garinsu Parvina da kuma Rugar Bani ba. To ku saurara, Rugar Arɗo Babayo, itace Rugarsu Parvina, kuma a can ƙasar Cameroon yanki Yahunde Rugar take.

Sai kuma ɗaya rugar wacce a nan ƙasarmu Nigeria take yankin Adamawa state, wani dalili yasa na sakaya sunayen garuruwa da ƙasar tamu da masarautun. Amman nasan duk mazauna Nigeria Adamawa zasu gane Rugar Kikan nake nufi nasa Rugar Bani Numan nake nufi nasa Shikan, dama duk sauran jihohinmu na sakaya sunayensu sabida wani dalili Amman nasan duk munsan inda tushen ƙabilar ɓachama suke.
Amman ba mmki in medasu yadda zakufi ganewa.
Ba wata ƙasa bace Kautal Nigeria nake nufi????????????

                         By
             *GARKUWAR FULANI*

????????????????????????????????????????????

????????️????????????????????????

             *GARKUWA*

                   PAGE 11

                            NA
              *AYSHA ALIYU GARKUWA*

                 ????????????????️????????????????????????




     Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku  kacal ta layin nan 09097853276 domin KARANTASHI daki-daki, ko kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, kana sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta WhatsApp number ta 09097853276. Special Group ne 1k cikin mako biyu za'a gaba wani sashi na littafin.    

Ido ya zubawa mutanen da yayi arba dasu, dai-dai lokacin daya.
Ɗago kanshi, yayi arba, da wasu mutanen, da shigar hukuma (police), da sauri ya miƙe tsaye yana ware hannun rigarshi da ya naɗe dan yin al’wala, tare da cewa.
“Lfy? Ku su wayene?.”
Basu kulashiba, sukayi kanshi gadan-gadan, cikin dakiya yace.
“Me hakan?”. Still no respond.
Sai matsoshi da suƙa ƙarayi, cikin dakiya da jarumtar jinin fulani ya gyara tsayuwarshi, yana binsu da ido ganin zagayashi da suka farayi, da ido yake binsu a zatonsa faɗane shiyasa bai guduba, domin, duk da yawansu bai Karaye ba, dan zuciyar gskya ce dashi kana jinin fulani ke yawo a jikinshi.
Su kuwa mutanen, na gabanshi ne ya ɗan fesa mishi wani abu mai kamar turare a fuskarshi.
Da sauri yasa hannunshin wai zai kare fuskarshi, cikin dakiya da haɗe fuska ya buɗe baki yace.
“Me kuka fesa meeeen.”
Sai kuma kawai yayi lu ya lumshe idonshi ya faɗi nan kamar gawa.

Da sauri biyu daga cikinsu suka ɗaukeshi tsallaka korin sukayi sukaje suka ajiyesu cikin motorsu dake can bayan lampon dake bayan korin.

So biyun kuma komawa mafakarsu sukayi.

A can wurin kiwon kuwa, Seyo ne ya ɗan kalli Giɗi tare da cewa,
“Bari in shiga muyi al’walan,in mun fito, sai kai da ya Lado ku shiga mu kuma mu tsare dabobbin namu gudun kada su shiga gonakin manoma.”
Kai Giɗi ya gyaɗa mishi daga, nan ya gangara ya shiga cikin korin.

Yadda sukayi Ya Gaini haka sukayi mishi, shima.

Giɗi da Ya Lado sunata jira, shiru-shiru ba motsinsu,
ganin hakane yasa, Giɗi ya fara kiransu.
“Ya Seyo!, ku fito mana, Lokacin sallafa na tafiya”.
Lado ne ya kalleshi cikin sanyi jiki yace.
“Shiga ka kirawosu”.
To yace kana ya juya ya nufi cikin korin,
har yaje inda zai gangara ya shiga sai kuma ya juyo ya kalli Ya Lado cikin sanyi yace.
“Ya Lado ka kula da dabobbin nan fa kada su cutar da manoma kaga kai ɗaya ka rage mai kula dasu, kada ka bari suyi nesa dakai”.
Lumshe ido Ya Lado yayi cikin wata sassanyan murya mai cike da rauni yace.
“Zaku dawo ai, kuɗin sai ku kula dasu da kyau in yaso ni sai in tafi”.
Kai ya gyaɗa tare da yiwa yayan nashi murmushi ya shige cikin korin.

Yana shiga ya fara dube-dube babusu babu dalilinsu, cikin ciyawa da kozozzaban ya fara leƙawa yana cewa.
“Ya Gaini! Ya Seyo!! Ya Gaini!!!”.
Jin shiru babu amsarsu bare motsinsune ya sashi ci gaba da waige-waige tare da cewa.
“Ya Gaini ina kukene? Yaya Seyo, ina kuke ban gankuba, kuyi mgna mana”.
Cikin fargaba yake lelleƙa wuraren, da yake ganin mutun zai iya fakewa a wurin.
Yana sunkuyowa cikin wani sunkurun kawai sai ya koma luuu ya faɗa ta baya sabida abinda suka fesa mishin yasashi bacci.

Daga nan suka ɗaukeshi sukaje suka sashi cikin motar da suka saka sauran yayunshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217 218 219 220 221 222 223 224 225 226 227 228 229 230 231Next page

Leave a Reply

Back to top button