
Washe gari Litinin.
ɗin, sauran dattawan garin suka sallaci Ya Lado, kana suka zauna amsar gaisuwa.
Suna kuma jin labarin inda yaransuke.
Ganin sunata wahalar tafiya ba lbrine yasa.
Bappa yace su dowo. Domin wanna abu addu’ace mgninshi.
Sannan kuma wannan karon bazasu saurari masarautar Numan ba , gangami zasuyi su kai kukansu, ga masarautar Joɗa, wanda a cikinta ne GARKUWAN FULANIN ƙasar Nigeria gaba ɗaya yake.
Da fari Arɗo Yabani bai gamsu da hakanba saida Bappa yayi mishi bayanin.
Dolefa suna da buƙatar hukama mai tsarki ta shiga tsakaninsu da ƙabilun Ɓachamawa nan, kana dole mgnar ta isa ga babbar masarautarsu, wacce za’a miƙa mgnar ga Ƙungiyar TABITAL POOLAKU, DA KUMA ƘUNGIYAR.
MIYETTI ALLAHA
Wannan dalilin ne yasa Ardo Yabani ya umarci gaba ɗaya matasan da suka bazama neman su Gaini su juyo su dawo gida.
Haka kuwa akayi kafin yamma sai gasu duk sun daddawo domin.
Wasu da yawa motoci suka shigo.
Bayan sallan ishane suka zauna zaman mitin domin sun gama shirya komai gobe dai kai tsaye masarautar Joɗa zasu wuce.
Bayan sun gama tattauna yadda abun yake suka tsaida zance kan cewa dattawansune zasuje.
Daga nan Duk suka tashi taron kowa ya koma gidanshi da tarin al’hini a zuƙatansu.
A can cikin birnin Ɓadamaya kuwa cikin makarantar su Aysha.
Zaune take bisa salla hannunta riƙe da carbi tana ja.
Kana hannunta ɗaya kuma rike da wayarta, wacce taketa kiran yayunta kab baya shiga tun jiya da yamma.
Cikin kula Rafi’a ta kalleta a hankali tace.
“Aysha ba komaifa, kinsan garin naku kunada matsalar Network, wasu lokutan kuma kinsan basu da cajine”.
Kanta ta jingina da jikin gini, murya can ƙasa tace.
“Gaba ɗaya fa, woyoyinsu basa, shiga, na maƙotanmu kuma ko sun shiga basa ɗagawa, Rafi’a hankalina ya tashi.”
Da sauri Rafi’a tace.
“No kada ki damu tunda kikaga basa ɗagawa alamun kenan woyoyinsu na wurin cajine ko?”.
Idonta ta lumshe tare da cewa.
“Zuciyata na yawan sinkewa Rafi’a, fargaba nakeji”.
Cikin sanyi Rafi’a tace.
“Yauwa to ki kira Ba’ana mana”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh hakane fa”.
Ta karishe mgnar tana dannawa wayarshi kira.
Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga,
Da sauri tace mishi.
“Ina wuni ya Ba’ana”.
Ba’ana dake zaune tsakiyar ƙabilun Ɓachamawa suna mitin yadda zasu farma garin Rugar Bani da yaƙin sunƙuru gobe, murmushi yayi cikin sonta yace.
“Lfy lau Mata, ya karatu?”.
Alhamdulillah tace tare da cewa.
“Ya Ba’ana ya garinmu ya lbrin gidanmu duk suna lfy?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Duk suna lfy garinmu duk anata kewarki ɗazuma na wuce ya Ladonkin a kwance yanata shan baccinsa babu ruwanshi da damuwar duniya”.
sam bata kawo komai a rantaba kan mgnarshi ta ƙarshe, saima sanyi da ta ɗanji daya bata tabbacin, suna lfy, sabida iya tsawon zamanta da Ba’ana bai taɓa yi mata ƙaryaba, koda zaiyiwa duk mutanen duniya ƙarya to ita baya mata ƙarya, kuma duk zafin gskyar mugun abunda yakeyi zai gaya mata. Abu biyu ya ɓoye mata a rayuwarshi sata da kisan da yakeyi, sai dai yana gaya mata in dai a kantane zai iya kashe kowa ma.
So cikin sanyi tace.
“To yasu Ya Gaini kuma”.
Murmushin mugunta yayi tare da cewa.
“Shima na wuceshi wurin Binto sunata hirarsu har tanata raira masa waƙoƙin soyayya”.
Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
“To ka gaida min su bari in ɗanyi wonka”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“To Mata kiyi wonkanki anjima zan kiraki muyi hira”.
To tace mishi kana ta katse kira, tare da cewa Rafi’a.
“Alhamdulillah duk lfyarsu lau ashe”.
Itama Rafi’a murmushi tayi kana sukaci gaba da hirarsu sai dai still fa tsoro da fargaba da bugawar da zuciyar Aysha keyi bai bariba, ganin hakane yasa Rafi’a, kallonta kasancewar Rafi’a ƙwararriyar mai koyar da girgirkene, a zahiri cikin makarantar tasu, da kuma social media. Cikin kula da son samawa aminiyar tata nitsuwa tace.
“Yauwa GARKUWA, zomu shiga kitchin, muyi ɗan alalan kwai, naga kin kawo mana koyaye da yawa.”
Murmushi Aysha tayi wace, akefi kiranta da ƙarshen sunanta.
hannun ta miƙa Rafi’a, cikin sanyi tace.
“Help me my friend, jikina yayi sanyi da yawa, ji nake kamar bazan iya tashiba”.
haka nan itama Rafi’a jikinta ya fara sanyi, sai dai sanin in ta baiyana kasalarta tashin hankali Aysha zaifi tsananta ne yasa ta dake, cikin sauri ta kamo hannunta ta jata-ta miƙa kana suka shiga kitchin ɗin.
Nan suka fara aikin sunayi tana ɗan janta da hira.
a haka dai har suka gama, kana, ta shiga wonka.
Shi kuwa Ba’ana maida woyarshi yayi cikin al’jihunsa, kana ya kalli Sarkin mayaƙan ƙabilar ɓachama da yake ce mishi.
“Shege Ba’ana wato, yana bacci cikin kabarinsa babu ruwansa da damuwar duniya”.
Dariyar mugunta sukayi dukansu,
wanda yake gefenshi ne ya kece da wata dariyar tare da cewa.
“Wai ita kuma Binto kukan natane waƙen SOYAYYA ko?”.
Kanshi ya gyaɗa musu cikin muguwar fuskarshi.
Wannan matashin ɗaya fara sokawa Ya Lado wuƙane lokacin da suka kasheshi. yace.
“Ita kuma da yake sokuwace har ta yarda k…”.
Wani irin tashi sukayi gaba ɗayansu sabida wani irin shaƙa da naushi da Ba’ana ya kai mishi, wanda a take ya fara kakarin mutuwa.
cikin zafin rai ya hankaɗa tarin mutanen dake son cotan yaron daya shaƙe ɗin amman ina sun kasa, wata zabgegiyar wuƙa ya lumtsumamishi a ciki wanda yasa sauran duk suka watse tura gawarshi yayi gaban su cikin ɗaga murya yace.
“Ina kashe wanda ya yabi Shatuma yace yana son Shatuma bare wanda ya zageta, duk wanda baya son ransa ya aibata min Shatu a gabana ya gani”.
Cit kake jinsu sabida masifar tsoronshi sukeji.
Dan ya fisu taƙadiranci dan Ba’ana mugun babarbarene mai baƙar zuciya.
Haka dai aka tashi wannan taron da yake dama sun gama tattauna yadda zasuyi farmakin.
Washe gari ranar wata Tuesday 21 November 2017 itace ranar da har abada al’ummar Rugar Bani bazasu mance da itaba a tarihin rayuwarsu, itace ranar da duk motsin da numfarfashi Shatu zatayi sai ta tunashi ranace data girgiza, zukatan al’ummar musulmai, ranace da tasa duk wani bafulatani makiyayi jin ƙuna da tafasar zuciya.
Ranace da tada hankalin al’ummar ƙasarmu nan dama maƙotanmu.
Tunda safiyar ranar, dattawan garin suka gama shirinsu cikin shigarsu ta al’farma, Malam Liman (Bappa) Arɗo bani Jauronsu, Ahaji Horo da Ahaji Umaru, kana Malam Yero, da kuma Alhaji Sa’idu.
su rai takwas dai suka shirya cikin kamala da mutunci. Junaidu ne yake cikin Shikan ya samo musu mota kirar siyana wacce suka ɗauki shatarta, domin zai kaisu har cikin fadar masarautar Joɗa kuma zai jirasu. Su dawo tare.
Nan suka shiga Mota gaba ɗayansu, suka tafi.
Kai tsaye har bakin masarautar suka tsaya dan an hanasu shiga,
sai da ɗaya daga cikin hadiman dake tsaron ƙofar, yaga duk manyan daddatawa ne yasa yaje ya samesu bayan sun gaisane sukayi mishi bayanin abinda ke tafe dasu.
Jin abin babbane yasa yaje yayiwa sarkin ƙofa bayanin.
Nan shima yaje suka gaisa suka ƙara jaddada mishi, zancen abinda ke tafe dasu, sannan
sukayi musu izini suka shigo cikin asalin farfajiyar mashigar masarautar.
Kan kujerun dake jere a wurin suka nuna musu su zauna.
Bayan sun zaunane sarkin kofa yaje, wurin sarkin fada ya sanar mishi, to nan sarkin fada ke cewa.
“To ai babu abinda zamu iya musu, tunda shi GARKUWAN FULANI, baya ƙasar waye zai saurari kukansu, suje sai ya dawo su sake zuwa”.
Cikin rauni sarkin ƙofa yace.
“Ranka ya daɗe sarkin fada, da dai an nema musu izinin ganin mai martaba, domin bazaiji daɗi ba in yaji sunzo kuma an medasu”.
Cikin isa da izaya sarkin fada yace.
“A kul sarkin ƙofa ka tsaya iya matsayinka, kaje kace suyi maza su bar nan domin GARKUWANSU baya nan”.
Cikin sanyi da mutuwar jiki sarkin ƙofa ya juya ya fita, koda yaje ya sanar musu, abinda sarkin fada ya faɗa hankalinsu yayi masifar tashi.
Cikin tashin hankali Arɗo Yabani yace.
“Shikenan danmu fulanine makiyaya mazauna daji, sai ya zama matsalarmu ba abar dubawa bace, wa al’ummar birane, duk inda muka kai kukanmu sai a koramu”.
Cikin sanyi sarkin ƙofa yace.
“Kuyi haƙuri ba korarku akayiba, in sha Allah za’abi kadunku, wlh shi kanshi mai martaba in zaiji abinda sarkin fada yayi to zai barranta dashi, kuma haka nan shima GARKUWAN FULANI in da zaiji abinda sarkin fada yayi wallahi zai haɗu da fushinsa mai tsauri, domin shi zuciyar Sheykh zuciyace mai cike da imani da tausayi”.
Cikin rauni Alhaji Haron yace.
“Ana binmu ana kashemu, ana sace yaranmu ana kora dabbobinmu.
Munje Police station an koramu, da mukaƙi tafiya suka watsa mata tiyagas, muje masarautar Numan akaci mana zarafi, sannan yanzu mun gudo gareku da yaƙinin zakubi kadunmu sannan kuma zaku koramu, so kuke mu ɗauki makami domin ramuwa ne?”.
Da sauri suka juyo gaba ɗayansu jin muryar Jamil da yanzu ya iso wurin da hadimanshi, cikin sanyi yace.
“A a Baba kada ku ɗauki makami domin ramuwa zuwanku nan shine babban abinda ya dace”.
Cikin jin daɗi suke kallonsa, murmushi sarkin ƙofa da sauran hadiman sukayi dan sun san yanzu dai sarkin fada bai isa ya hanasu ganin Maimartaba. Domin yanzu bai fito fada bama tukun so zasu ganshi a kebantaccen wuri na musamman.
Cikin kulawa da sakin fuska Jamil yace.
“Baba ku biyoni”.
Cikin jin daɗi sukace mishi to, kana suka bishi a baya.
Ta gaban shashin Sarkin fada suka shiga, kai tsaye har cikin fada ya shiga dasu,
shida kanshi yasa hadimai suka kawo musu ruwa.
Sannan a nitse yace.
“Baba ku zauna a nan zanje in sanarwa mai martaba, duk sanda ya fito daku zai fara, tattaunawa
In da masu buƙatan zagawa gacan wancan kusurwar in kumbi cikinta zata sadaku da bayi”.
Cikin jin daɗi sukace.
“Mun gode yaro Allah yayi maka al’barka”.
Amin Amin yace kana ya sallamesu ya fita.
su kuma sukaci gaba da zaman jiran fitowan sarki.