
Kamar bata wurin haka ya jawo System ɗinshi ya fara daddannata.
Kamar babu kowa kusa dashi haka yaci gaba da aikinshi.
A system, ita kuwa Sitti ido ta zuba mishi.
Tana kallon yatsun hannunshi da yaketa sassarfa, tamkar shiya haaliccin na’ura.
Yanajin idanunta na yawo a sasan jikinshi, hakan yasa, ya ɗan juya kwayar idanunshi, ya ɗan kalleta ta wutsiyar idonshi, murya can ƙasa yace.
“Sitti wannan kallonfa, kin san bana son kallo kam ko?”.
Ajiyar zuciya ta ajiye, kana ta ɗan janye Hiramin kanshi, da sauri yasa hannunshin ya kame hiramin cikin kwaɓe fuska yace.
“Sitti ya haka, kinsan Haroon ba kan gadone dashiba, yanzu zai iya shigowa da yaran nan”.
Ido ta ɗan rufe kana tace.
“To su yaran mayune, ko yaushe kana rufe da Al’kyebba da hirami, kasha iska mana, ko nauyi basa makane?”.
Kanshi ya ɗan juya kana a hankali yaci gaba da aikinshi tare da cewa.
“Suturce jiki shine, zaiyiwa ɗan adam nauyi, Sitti, sannan ya za’ayi in bari ko wani Tom and Jerry su kallarmin suman kai, ai shi hula da hirami kamar ɗan kwaline wa mace”.
Sai ya kuma ɗan juyowa ya kalleta tare da cewa.
“Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo”.
Fuskarta ta haɗe kana tace.
“To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faɗa mana”.
Kauda mgnar yayi tare da cewa.
Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma’a ina son in kasance cikin ƙasata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu”.
Haroon da yanzu ya shigone ya ɗan kalli ɗan uwan nashi, cikin mmki yace.
“Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ƙasar ba?”.
Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system ɗinshi yayi kana ya miƙe a hankali,
gaban drower’n gadon ya nufa,
buɗewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya ɗauko,
Kana ya dawo gaban Haroon.
Hannun shi ya kamo ya danƙa mishi su, kana yace.
“Gasu, ina son zamu bar ƙasar nan ranar al’hamis.”
Da sauri Sitti tace.
“Kaida waye zaku tafi”.
Ba tare daya kalletaba yace.
“Da ke”.
Kai ta kuma juyawa tace.
“A a kam ka koma kai ɗaya, ni ban gaji da ganin ahlinaba”.
aKanshi ya kaɗa tare da cewa.
“Zafa ki koma, don bazan barki a kasar nanba, kiyi ta haɗa min tarko, dole tare zamu tafi, inada zama mai mahimmanci, dole inje inji da matsalar al’ummar da aka naɗani GARKUWANSU, tunda ke kika sa na amince da wannan naɗin, ina zamana lfya, wani mulki ko sarauta basa jadawalin rayuwata, keda waɗancan tsofoffin sarakunan kuka likamin wai GARKUWAN FULANI,
To sun samu matsala kuma dole inje in bincika”.
Shiru kawai Sitti tayi ganin karfin hali ziraran miraran.
Zuwa yanzu ta dena mmkin, cewa akan abu biyu Sheykh ke iya doguwar mgna, akan Alqur’ani, wanda shine zaka samu zai iya wuni a zaune yana tabsiri ba gajiya ba yunwa bare ƙishi ko bacci.
Sai kuma akan wannan sarautar GARKUWAN FULANI da aka bashi shekarun biyar baya, wanda harga Allah baison wannan Sarautar ko kaɗan sai dai dole da akayi mishi, da fushin da Abbunsu ya nuna a kan haka.
Shiyasa duk sanda zaiyi ƙorafi yakan iya jera mgna biyar zuwa bakwai, wanda sam shi tsarin rayuwarsu ba mai doguwar mgna bace.
Kai takaɗa jin yana cewa.
“Ku ɗan bani wuri”.
Basuyi mgna ba suka fita, a tare, domin sun san Sheykh Jabeer mutunne mai tarin tsananin al’kuyya da killace jikinsa, shi kanshi yana kunyar kanshi a rayuwarshi ta duniya shi bai taɓa yin tsirara a kan kanshi wai yaga surar jikinshi ba, Allah yasani yana masifar jin kunyan kanshi.
Haka yasa koda wonka zaiyi, baya yin tsirara,
yanada wasu tausasan gajerun towel wanda duk rintsi dasu yakeyin wonka a jikinshi.
Suna fita falo, Haroon ya tsaya yana kallon Jazrah, dake konce bisa kujera ta kife kanta a cinyar Jannart tana kuka mai sanyin sauti.
Kai Sitti ta juya ta nufi ɗakinta,
Allah ya sani Jazrah na son Sheykh, shi kuwa bai nuna ya tsaneta ba, amman dai ya nuna zahirin bazaiyi aureba.
Haroon da Jannart ne suka zauna suna bata baki.
Saida ta nitsune suka fita tare.
Shi kuwa Sheykh suna fita, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe.
Kana ya dawo bakin gado.
A hankali ya zare tattausan al’kyabbar jikinshi, fararen kayan dake jikinsa suka baiyana.
A hankali ya zare rigar ya ajiyeta gefe.
Zariyan wonɗon ya kunce, tare da zama, ya saɓule tare da matsawa gefe.
Ya rage dagashi sai fararen boxes da vest.
Juyawa yayi yana taku mai cike da nitsuwa,
ya shiga bathroom ɗin.
Yana shiga ya maida ƙofar ya rufe,
kana ya rage hasken ciki.
Sannan ya cire ƙananan suturun dake jikinshi tare da ɗaura towel ɗin, a ƙuginshi zuwa kan cinyoyinshi masu yelwar gargasa mai taushi da tsulɓi da sheƙi tana,konce lib-lib a farar fatar jikinshi.
A haka ya fara, wonkan, bayan yayi Brosh a hankali yake bin jikinshi da sabulun mai ɗan karen ƙamshi, yanayi ya cuccuɗa jikinshin.
a hankali ya iso kan ƙugunshin, cikin sabo da iya ɗabi’ar tasa, ya cusa hannunshi ta cikin ɗaurin towel ɗin, ya rinƙa cuccuɗa jikinshin da murza mishi daddaɗan sabulun ya murje ko wani lungu da saƙo na sasan jikinshi ba tare da idanunshi ma, sunga tsiraicinsaba.
A ƙalla yayi sawon daƙiƙu ashirin a bathroom ɗin kafin, ya fito,
yana ɗaure da wani babban towel mai ɗan karen kyau da taushi bayan ya matse wancan ya shanya.
Yana saƙo ƙafarshi cikin bedroom ɗin ya…!
Solo-salo-salon GARKUWA na dabanne!
By
*GARKUWAR FULANI*
????????????????????????????????????????????
????????️????????????????????????
*GARKUWA*
PAGE 13
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
????????????????????????????????
FREE PAGE
Littafin GARKUWA na kuɗine, Special Group 1k Normal 300, in kina buƙatar karanta lbrin GARKUWA turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276. Gareku mutanen Special Group turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.
Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki, in kin san zaki sayi littafinane dan ki fitar dashi, na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki saya bana son kuɗinki, ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina. Dan Allah nace badon niba.
Yaji anata bubbuga mishi ƙofar ɗakin,
bai kulaba, yazo a zauna bisa kujerar dreesing mirror, a hankali yake tsane ruwan jikinshi, bayan ya gama ɗan tsane ruwanne ya busar da tattausan sumar kanshi, ta hanyar na’urar busar da gashi.
Mai ya ɗan shafa, kana ya gyara gashin da kyau, sannan ya miƙe yaje gaban.
Drower’n, a nitse ya buɗe, wasu datsatstsun kaya riga da wondo na yadin Lamud, yadin Sky blue ne mai masifar kyau. Sai kuma ya zaro wata farar al’kyabbar fara ƙal. Da farin hirami.
Rufe wannan gefen yayi, kana ya buɗe ɗaya gefen.
Ƙananan kayan ne a ciki kamarsu Jallabiya da boxes vest dasu zagayen baƙin abin da yake ɗaurawa kam hiraminshi.
Suma duk mafi akasari su fararene.
A bakin gadon ya ajiyesu.
Kana ya fara kimtsawa.
Bayan ya gama shirinsa ya fito ras cikin kalar sky blue and white sai Black half cover da kuma baƙin zagayen saman hiramin.
Ya fito ras tamkar dai yadda zuriyar mahaifiyarshi da suke tsatson limamen Harami suke fita.
Ko yaya ka ganshi dole kace shi balarabene, sabida komai nashi irin nasune. Kyau, fari, gashi, ilimin addini, nitsuwa, imani, da kuma irin shigarsu, da shima ya rainu da hakan tunda a cikinsu ya girma.
Wani turaren Oud Kareem ya feshe jikinshi dashi.
Lumshe ido yayi sabida shida kanshi ya shaida ƙamshin wannan turaren nashi iyakane.
A hankali ya nufi ƙofar fita yana tafe yana tasbihi.
“Astagafirullaha wa’atubu ilaik.
Astagafirullaha zunuba jami’an. Subahanallahi Wal’hamdulillah wa la’ilahaillahu Allahu Akbar.”
Da wuya ka iya jin abinda yake faɗin, sai dai ina ka lura da motsawan jajayen laɓɓansa, masu kama da jajayen kunnen fire masu taushi zaka fahimci tasbihi yakeyi.